Sanadin Zane 19-20

 


πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„πŸ‘„ _*SANADIN ZANE*_

πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹πŸ’‹

By maman noorul 

Hudah 



Paid book


      This book is 300  for regular group....500 for vip via 2378022567

Aisha Mohammed

Zeinith bank for more information contact me via watsaap 09090112946


πŸ…Ώ️1️⃣9️⃣🫦2️⃣0️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


         Lalube kawai takeyi cikin duhu Dan wayar Bata fiya lafiya ba  ,ganin ta gan wayar Bata gan battery ba sai abin ya Kara Bata haushi abinka da kurma da mugun zuciya ji tayi numfashinta yayi Sama


D'agowa tayi da niyyar yi me tijara ta saci kallon motar da aka paka tasan masu kudi ne a ranta ta Raya kila sanadin samun sabon wayarta kenan ya yayi Dan tijara zatayi musu har sai sun siya Mata waya 


      Juyawa tayi Dan ta ta tada musu hankali aiko kamewa tayi dan idanunta sauka yayi a kansa aiko fidda idanu tayi zuciyarta na mugun bugu  


   Kawu ya karaso Yana cewa bawan Allah kawo ruwa kardai yayi mutuwar sojoji a tsaye subhannah bazanyi mamaki in Marin ya gigitashi kasan da zuciya take Kai duka fah 


Abbas ko kasa motsawa yayi kamar wani soko saboda lamarin ya mugun gigitashi ko kad'an be ma kalli kurma da nadama ya mamayeta ba 

Kawu ya kalleta yace"ikon Allah kowa da yanayin da ya shiga 


     Keee lafiyarki 


    Duk tunanin da zatayi Taki samun mafita sai yanzu ta gane dalilin kamewarsa ta dinga salati a zuciyarta dan tasan 

Ba karamin mutum ta kaiwa bugu ba 


    Kawu ko Yana ganin irin motar dake pake tunaninsa ya canza burinsa Kar kurma tayi yaren kurmaci su Gane kurmace 


    Kallonta ya sakeyi sai ya gan ta rude abin ya mugun bashi mamaki 


    A hankali tayi ta matsawa kusa da taku d'ad'aya harta Kai kusa da yarima 


            Ai ji yayi ta zube jikinshi a Dole ta Suma 


Kawu rungume hanun yayi Yana kallon ikon Allah Dan yasan ba Suman da tayi tsagwaran iskancine 


Fadiwar da tayi jikinsa shi ya dawo dashi hankalinshi ya wani tunkude ta be Kara ko minti daya ba bare ya kalleta yayi mota Abbas na binsa a baya amma sauri yake sosai 


Driver side ya shiga har Abbas ya Kama handle din motar sai yaji ya jata a sittin 


Tunda Abbas ya gan Haka yasan ran maza ya bace dan  tunda yake tare dashi be tab'a ganin yayi driving ba infact zai iya cewa be tab'a driving da kansa ba in Banda a lokacin da ya koya ba at his early age 


    Jikinsa yayi sanyi Dole zai bi yarima  hakan yasa ya tare napep dan ko ya tsaya ya rasa irin hukuncin da zaiyiwa yariyar 


    Suna barin wurin kawu yace"keee tashi kafin in wanka Miki mari yariya Ina Miki kallon kurma Ashe dai shegiyar d'ari ce,yariya daga ganin mutum sai ki Fara karuwanci ikon Allah "


    Kurma kin Bude Ido tayi saboda pretending wani shuri kawu yayi Mata ta tashi da wuri ya cigaba da magana Yana cewa"yariya dake kin San ki mannewa namiji ikon Allah, ikon gaske 


             Kama hanunta yayi ya jata zuwa gida 


Tun a zaure yake ta kwalawa ummi Kira 


Ummi dake kallo a dan karamin akwatin tv ta ta fito 


Yace"kina ganin yariyar Nan ko na so ki gan karuwancin da ta zuba data gan wani gaye wallahi sai kin Sha mamaki abin ya kazanta Wai fa fad'awa namiji tayi a jiki,toh aurar da ita zanyi in huta wallahi kafin labari ya Sha bambam in Shiga uku 


   Hafsat dake kwance kofar d'akinta tace"ka fasa aurar  son me kudinne"


Yace"ai Sha kuruminki Kamar kinyi bako ya mutu na gan wani had'ad'e yanzu Nan shi Zan bawa Dan na gan alamu da canji hanunsa 


    Hafsat  tace"Wai kabiru meyasa kake b'atawa yariyar Nan lokaci ne tana da masu santa ga wanan yaron isah gwargwado Yana da rufin asiri Amma kaki bashi Daman aurenta wani me kudi ne zai aureta a Haka ko mance kake kurmace "


Yace"kurmanci ya Hana ta Zama macene wanan da kike gani sai tafi me magana kawo wuta 


      Hafsat tace"Allah ya kyauta muna Nan ai "


Yace"Kuma zaku ji alkhairi ai da yarda rabbi izzati "


     Hafsat Bata Kara cewa komai ba ummi ta koma d'aki abinta dan lamarin kabiru da kurma na caza mata kai 


Yace"ya wuci mu b'oye Masa larurarta mu ninke shi baibai"


                Hamma da kurma takeyi yasa shi cewa je kiyi wanka kiyi sallah ki kwanta 


      Bata jishi ba tayi d'akin ummi shima ya Shiga yayi wanka 


      ________


Abinda ya faru ya shiga jikin yarima sosai Dan Yana shiga d'akinsa a masaukinsa jikinsa ya Fara rawa wanan ai insult ne wa royalty dinshi baya Jin ma an taba dukansa 


   Gaban madubi yaje ya  tsaya Yana kallon kumatunta who is she...ita din wacece a garin Nan Yar wacece Kuma miye ya Bata gut din Kai Masa Mari 


        Sosai jikinsa ke rawa idanunsa ya canza kala sai yanzu yake mamakin tahowa 


  Watsi yayi da kayan saman mirrow din ya kaiwa madubin naushi ji kake tasss ta tarwatse aiko ta yanke hanunsa 


   Yayi zaman dirshen a kusa da gado ya hade Kai da kunya har yanzu karkawa yakeyi danshi mutum ne me pride da eagle 


           Abbas ne ya turo kofa a hankali cike da tsoro ya karasa inda take zaune dan ko motsawa beyi ba ga jini na bin  hanunsa ya saki salati tare da zuwa ya karasa ya duka cike da girmamawa ya Kama hanun 


Fisgewa yayi ya kalli idon nan Kamar garwashi yace"wacece ita "


     A firgice Abbas yayi baya yace"what gave her the gut the audacity to lay her filthy hand a kumatuna 


       Cike da rashin Hankali jinin dake zuba a hanunsa Abbas yace"ranka dade ka Bari muyi dressing din ciwon Dole nema a hukuntata 


    Shako Abbas yayi yace"ta Yaya za a hukuntata bΓ yan a kasar su muke bazaiyi yiwu ba Dan zasu iya kaimu Kara 


         Abbas yace"Dan Allah yallabai ka Bari in Kira ayi dressing ciwon 


Kallon jini yayi kamar mahaukaci ya kaiwa center table din naushi da hanun dake jini Saida ta tarwatse shi kanshi ya ji wani zafi ya ratsa kwakwalwarsa ya saki Dan kara


Abbas ya Kuma kai hanun zai kamo hanun ya d'aga me hanun 


    Kamar wani me bori Haka ya dawo ya saki murmushi kamar ba me natsuwar yarima ba 


      Shako Abbas yayi yace"Ina son a wulakantata,wulakanci mafi Muni I hate Nigerians I hate them,they are all the same ko kasan kurma data kashe mahaifiyana Nigerian ce a hate them,Abbas ka wulakanta min ita Kai Ina son in huce haushin abinda kurma tayi min a Kan wanan shashasha ka koyar da ita tarbiyya 


     Kada Kai kawai yake kamar sabon kamu shima Dan be tab'a ganinsa a Haka ba 


         Zaiyi magana yarima ya katseshi da cewa get ou........"


        Abbas ya katse me hanzari zaiyi magana ya daka me tsawa yace"I said out of my room"


Babu musu ko jayayya Abbas ya mike har ya Kai kofa 


   Yace"wait "


Tsayawa Abbas yayi ya kallesa tare da dukar da Kai alamun girmamawa


     Yace meya faru yau?"


Abbas yace"ba komai ni kaina ban gan komai ba ka kwantar da hankalinka domin rantsuwa nayi da rayuwata Zan b'oye sirrinka Kuma in baka kariya babu Wanda zaiji maganar nan an binneta a inda ta faru "


    Jinjina Kai yayi Abbas yayi waje kallon ciwonsa yayi Yana murmushi a yau be runtsa ba sai kusan asuba hakan yasa ya makara sallah asuba 



Washe gari




Maman Nur

No comments

Powered by Blogger.