Sanadin Zane 21-22
ππππππ _*SANADIN ZANE*_
ππππππ
By maman noorul
Hudah
Paid book
This book is 300 for regular group....500 for vip via 2378022567
Aisha Mohammed
Zeinith bank for more information contact me via watsaap 09090112946
π Ώ️2️⃣1️⃣π«¦1️⃣1️⃣
Bismillahir Rahmanir Rahim
Washe gari
Radadin zafin ciwon da yaji a hanunsa yasa shi Bude Ido aiko abinda ya faru ne ya dawo Masa ya sake rikecewa duk jinin ya bushe ga katon ciwo da sai anyi me dinki Dan ta bude sosai
Zama yayi ya kalli agogo sai ya gan ya makara ya Kuma d'aura laifin hakan akanta Dan baya Jin Yana Wasa da sallah
Mikewa yayi zuwa toilet ba tare da yabi Kan wayarsa Dake ringing ba gasa jikinsa yayi ya fito ya zura rigarsa ya tada sallah
Kiran Abbas yayi ba ayi awa ba sai gashi ya Zo da Dr
Dressing akayiwa ciwon tare da Yi masa allurar ~tetenus~ aka nade hanun da bandage
Baccin wahala ne ya sake daukarsa bΓ yan su Abbas sun fita be tashi ba sai 11am shima yunwa ce ta tadasa
Noodles yayi ordering da tea ya ci sosai dukda incident din jiya nata flash back a memorysa a Haka ya d'aure Yana gamawa ya Kira Abbas....kallon kofa yayi a lokacin da Abbas ya tura kofar sai Kuma ya dauke kansa
Dukawa Abbas yayi domin girmamawa
Yace"me kake da bukata ranka dade
Yace"na baka nan da 48hrs i want every details about her I dont care how you do it Ina son Jin komai please
Mikewa yayi yaje ya d'auko kudin Nigeria Yar dubu bounch kusan biyar ya ajiye me yace in be Isa ba ka fad'a min
Mikewa Abbas yayi ya kwashe kudaden yace"an Gama ranka dade "
Binsa yayi da kallo har ya fita ji take kamar fah ya jawo yariya ya rasa meyasa ya tafi jiya ba tare da ya ci kaniyarta ba
____________
Da yike kurma akwai son Jin Dadi itama fa ta Kai goma Bata farka ba,Saida ummi tayi da gaske gasken ta farka tayi brush tayi wanka dan ita Bata wani aiki Kuma bawai Bata iya bane ta iya har girki Amma kawu ya d'aure Mata gindi a cewarsa ita ba kalar girki bane ko tayi aure Yi mata za ayi ummi tayi fad'a ta gaji ta koma gefe ta zuba ido
Zuwa tayi ta zura doguwar Rigar shadda da kawu yasa Fahad ya dinka mata a karamar sallah shadda a matse dan samunsa ba me yawa bane yayi Mata wanan shaddan Dan d'inki ma kadai me tsada ne ga shaddar duk yadi dubu hud'u yadi uku Amma kawu yasa shi gaba ya siyi Wai sai tayi gayu zata samu manimimak kudi
Shaddar ta Mata kyau gashi sai maiko take stones da aka jera a aikin na sheki
Dauri ta murza Dan kurma akwai iya dauri ta yafa gyalle ta fito
Kawu na ganinta yace"wanan dai bazan yarda dashi ba koma ciki ki saka hijab
Da yike ta karanci labensa ta gano kalmar hijabi sai ta tura Baki tana Yi kamar zatayi kuka
Yace"wallahi ko Fatima ce zata dawo duniya bazan Bari ki fita Haka ba Haka kawai a cuce mu,gaki Yar dukul dukul son kowa kin Wanda ya rasa wani gardi ya Zo ya jaki lungu ke ba bakin magana ba bare kiyi ihu a jiki fuskar ki kadai zai iya fisgar maza bare kinsa gyalle sun gan diri atoh...."Kama hanunta yayj yace"amshi Nan "ya Mika Mata dan kwarya da maganj ciki yace"Sha kwana biyu Baki Sha maganin tsari ba Dan akwai wasu shegu na Nan gefe masu hanawa kansu bacci Dan su gan fadiwar wani toh nidai ban duba Amma Ina bada taimakon sari ina binki da addu'a allah ya tsare min ke yanzu dai kinci dubu sai ceto duk hasadda me hassada saidai ya gaji ya barki wallahi ina tsaye kanki daram
Shanyewa tayj sanan ta me murmushi ta shiga ta saka hijabi sanan ta ruga da gudu ta bar gidan rataye da jakarta
Maman nur
Leave a Comment