Sanadin Zane 5-6


      🅿️5️⃣🫦6️⃣


Bismillahir Rahmanir Rahim


        Yace"innalilahi wa'ina ilahy raji'un na gan ta kaina Ni kabiru yau sunana gawa na Shiga uku ban lalace ba ya Allah ka fiddani"


Kallon bakinsa take da hanun tayi me alaman what?"


        Ya girgiza Kai,kallon jibrin tayi ta Fara me yarensu na kurame da yike ya iya sosai Dan special education ya karanta anan c o e ya iya sosai 


          Kallon kawu yayi dariya na niman sub'uce me  kawu yace"kayiwa annabi karka fad'a mata kasan kurma Nan mahaukaciya ce yanzu sai ta hanani sukuni a gidan ta kullaceni na  shekaru kafa santa Ni wallahi da a ce Maryam ta fad'a min abinci toh me zai kaini gigin tabawa ai gomma yunwa ta kasheni da inyi kuskure cinye Mata abinci Ni kabiru 


    Lura da Kamar magiya yake ta karasa gun ummi dake Duke tana kokarin hade wutarta da yike icen ya jike abinka da damina sai wahalal da ita yake yanzu ta samu Roba ta saka wutan ya tashi d'agowa tayi tana kallon fannah a kullum in ta kalli fannah tausayinta ne ke lullubeta Dan tasan irin rayuwar da marigayiya mahaifiyarta tayi kafin ta bar duniya wanan lalura cuta ce Mai girma  shiyasa Bata kaunar abinda zai tabata


       Nuna kawu tayi da yatsa ummi tasan halinta Bata tsaya Jan magana ba ta Kai hannun bakinta tana Mata alama da kawu ya cinye Miki abinci....abinci Amma karki damu Zan girki wani yanzu"ummi tana maganane tana Mata demonstrating 


    Fannah da yunwa takeji da k'yar ta karaso gida cikin gurnani da b'acin Rai sai uhhmmmm kake ji alamun matsifa ke cinta sai nuna shi take tana wani irin huci 


   Ba abinda kawu yake sai salati dan fushine da ita na tashin hankali gata da shegiyar kwadayi sai uban rowa in kana son ka gan b'acin ranta ka ci Mata abinta 


      Beyi aune ba ya gan ta jawo icen dake wuta sai hayaki yake

Idanunta a rufe tayi kansa Allah ya kiyaye yayi saurin dukawa jikinshi sai rawa yakeyi sai salati yake ganin tayi kansa ya mike da gudu yayi cikin d'akin ummi da ko kallonsu batayi ba dan inda sabo ta Saba 


Ai da kurma ta Fara bala'i Saida ta hargitse lissafin mutanen anguwa bala'i take ana Bata hakuri Dan Saida ma ta sauke ruwan tuwon ummi ta jikar wutan ummi ko ta koma gefe ta samu wuri ta zauna,sai Yan anguwa ne ke fitowa suna bata hakuri 


Saida hafsat ta dawo ta siya Mata coke da biredi 


Cikin lallashi hafsat ta d'auko Mata kujera ta zauna ta Fara mata alaman ta kwantar da hankalinta zata girka Mata abinci me Dadi 


    Haushi ya dibeta ga magana na cinta a Rai ba hanya fiddashi sai kawai ta fashe da wani irin kuka 


A lokaci d'aya mutanen dake tsaye kanta Dan in ta Fara kamar me iska Suka sauke ajiyar zuciya Dan kowa yasan in har tayi kuka ta sauko kenan dan kamar me iska haka take Abu in ranta ya b'ace 


        Kallon hafsat tayi tana yagan biredi da Coca-Cola idanunta yayi jazur saboda b'acin rai 


Hafsat ta fito da indomie a jaka tace"Sha cock indomie yanzu yanzu Zan dafa Miki 


Murmushi tayi ta jingina da bango sai ta saci kallon ummi ta gan ummi ko kallonsu batayi ba sai kawai ta cigaba da yagar biredinta 


Kawu ko har uwar d'aka ummi ya shiga ya kulle duk wanan hayaniyar Yana jinshi yaki fitowa 


     Ummi ce ta mike ta shige daki ta Fara bugawa tana cewa"ai sai ka bude malam Zan shiga d'aki Ina da uzuri 


Dan budewa yayi ya leko Kai yace"ta huce ne Maryam"


Wani kallo tayi me sai ya fito Yana wani cika Yana batsewa 


Ratsata yayi ya fito ya tarar da hafsat ta girka Mata indomie ana juyewa a plate sai turiri yake 


      Kallon kurma yake harda had'iye miyau ya zauna daga kofar ummi Yana kallo,hafsat na soya  kwai kurma ta mike ta Zo ta d'au plate din indomie din da zafi yayi ta kaiwa Baki har aka saka Mata kwai 


Kawu ya gyara Zama tare da kishingid'a a bango 



Yace 



Maman Nur

No comments

Powered by Blogger.