Saran Boye 51
No. 51
............Tun fara jin dariyar Papa Aymah ta rintse idanunta da ƙarfi, ko ɗar bataji a rantaba na tsoro. Sai dai bata fatan ya ganta a ɗakin. Harta yunƙura zata ɗaga katifar da zaton ba shigowa zaiyiba sai taji sautin takowarsa. Da sauri ta saki tana waige-waigen ina ya dace ta shiga ta ɓuya. ‘Toilet ’ zuciyarta ta bata amsa a taƙaice. Da gudu ta nufi toilet ɗin dai-dai da murɗa handle ɗin ƙofar bedroom ɗin da papa yayi. Yana shigowa tana turo ƙofar bathroom ɗin.
Da sauri ya kalli ƙofar toilet ɗin danjin ta ɗanyi ƙara alamar rufewa. Yay tsaiy yana kallonta zuciyarsa fal mamaki. Shi dai yasan baiyi tsammanin ganin kowa a ɗakinsa ba. Musamman daya san duk ahalin gidan ya barsu a church ne. Shima harya fara lecture sai ga baƙonsa mai muhimmanci Andrew yazo. Dole ya baroma Uncle Mike shikuma yazo yaji da baƙon nasa dan yafi lecture ɗin da zaiyi a church ɗin muhimmanci.
Duk da yasan babu kowa ɗin dai, sai ya sami kansa dason tabbatarwa. Dan haka ya nufi toilet ɗin yana zancen zuci.
‘Ya ALLAH!’. Nu'aymah ta faɗa a zuciyarta tana rumtse ido da ƙarfi jin kuma ya nufo toilet ɗin. Da sauri ta koma ta jikin bayan ƙofar, yanda idanma ya buɗe bazai gantaba sai dai idan shigowa yay ya rufe.
Ƙofar kuwa ya tura ya leƙa kansa yana bin ko ina da kallo. Baiga alamar akwai wani motsi ba saboda numfashi Aymah ta ɗauke gaba ɗaya. Yay guntun tsaki ya jawo ƙofar ya rufe ransa na raya masa abarda ya shace a daren jiya bata gama sakinsaba kawai.
Yana maida ƙofar ya rufe Aymah ta saki wani nannauyan numfashi, hannunta toshe da bakinta, idanunta kam har sun kaɗa sunyi jajur dan wahala. Da sauri ta matsa tana leƙensa ta kafar makulli. Ta zaro idanu waje da saurin sake toshe bakinta jin zatai suɓutar baki saboda ganin Papa daya danna wani ɗan abu a jikin Wadrobe ɗinsa. A hankali Wadrobe ɗin ta zuge kanta gefe, bangone sosai kamar yanda kowa ya sani ya bayyana. Amma a mamakinta sai taga yasa hannu yana shafa bangon a hankali, yanayi yana kallon ƙofar shigowa bedroom ɗin. Da alama tsoro yake ƙila kar baƙon nasa ya biyosa. Gani tai ya sake danna wani abu a jikin bangon, sai ga wani ɗan loko kamar drawer ya bayyana. Sai dai shi wannna murfinsa na ƙarfene. Key ya ɗakko a samansa ya buɗe, bata ganin abubuwan dake ciki saboda murfin ya tare ta. Wani madaidaicin jakka ya fiddo a ciki ya ajiye a kan gado, ya cigaba da ɗebo abubuwan da ba fahimta takeba yana lodasu a jakkar. Yana ƙoƙarin rufewane farar envelope ta faɗo. Gani tai ya duƙa ya ɗauka yana jan ƙaramin tsaki, ya ɗanyi magana da yare sai kuma ya ajiye envelope ɗin a saman gadon itama sannan ya maida Wadrobe ɗin yanda take ya ɗauki jakkar ya fita yana gyara wuyan rigarsa.
Da sauri Aymah ta fito tana haɗa gumi, ta ɗauki envelope ɗin jikinta na tsuma ta buɗe. hoto ta gani, duk da bata iya zaman kallon wanene a hoton ba haka kawai zuciyarta ta bata hoton da take nema ne tabbas. zaresa tayi a cikin envelope ɗin, ta buɗe bedside drawer data ga invitation a ciki ta zaro ɗaya ta saka a envelope ɗin. Shi kuma wanda ta ɗauka ta ɗaga rigarta ta saƙa ciki sannan ta gyara ta nufi ƙofa cikin sanɗa. Leƙasu ta farayi ta kafar makulli, hakan yay dai-dai da tasowar papa ya sake nufo ɗakin. Da sauri ta shige cikin labulen window tana rumtse ido, dan harga ALLAH yanzu kam zuciyarta bugawa take da dauri-sauri.
Jinin ɗan adam ya wuce wasa a waje, dan haka papa sam zuciyarsa ta kasa gaskata masa babu mutum a ɗakin. Ƴan kalle-kalle ya farayi a ɗakin, idonsa ya tsaya ƙyam a inda Aymah take cikin labule. Duk da bawani nuna alamun tana wajen labulen yay ba, saboda yanada kauri da cika, sai ya nufi wajen. Baƙaramin bugawa ƙirjin Nu'aymah ya keyi ba a wannan lokacin, zuciyarta ta buɗe sosai kamar zata faso ƙirjinta ta fito ta toshe bakinta da ƙyau tana rumtse idanu da ƙarfi, dan tama rigada ta sallama sai ya ganta.
Yana ɗora hannunsa saman labulen wayarsa nayin ring. Tsaki ya ja tare da ja baya, ya zaro wayar yana sake jan wani tsakin. Sai dai ganin mai kiran nashine ya sakashi ɗagawa da sauri yasa wayar a kunne.
A hankali Nu'aymah ta sauke numfashi da buɗe idanunta ta sake buɗewa a hankali hannunta dai-dai saitin zuciyarta. Kobi takan wayar da papa keyi bataiba, sai dai jin ƙauri yasata ɗan buɗa tsakkiyar labulen ta leƙa. Hoton nan taga yana ƙonawa yana cigaba da amsa wayar. Sai da hoton ya kammala ƙonewa tsaf a cikin envelope ɗin dabai ciresa ba sannan ya ɗauka abinda ya shigo ɗauka ya fice yana cigaba da wayar.
Saurin fitowa tai daga cikin labulen, dan ta fahimci dolene tabar sashen nan kafin baƙon papa ya tafi.. Komawa ta sakeyi jikin ƙofar yanzunma ta leƙa. Hangosu tai gaba ɗaya hankalinsu nakan centre table da alama wani abu suke lissafawa. Buɗe ƙofar tayi a hankali, ALLAH ya sota ma bata ƙara, ta ziro ƙafarta ta dama tana ambaton sunan ALLAH, ɗayar ta sake zirowa ta fito gaba ɗayanta batare data rufe ba. da sauri ta duƙe ganin baƙon papa zai ɗago, ta fara tafiya da rarrafe har zuwa bayan kujerar da papa yake.
Ganin yanda Andrew ke kallon ƙofar bedroom ɗin kamar baya fahimtarsane ya saka papa tambayarsa ko lafiya?.
Kai tsaye Andrew ya tabbatar masa tabbas mutum ya gani ya fito a ɗakin. Zabura Papa yayi ya miƙe, hakan ya bama Aymah damar rarrafawa da sauri tai gaba hanyar ƙofa, ta buɗe ƙofar da gudu ta fita. Gudunta ya sakasu juyowa da saurin suma, sai dai ta rigada ta fice. Biyota sukayi dan sunajin sautin gudin nata. Suna fitowa tana maida ƙofar sashensu data sami damar shigewa ta rufe. A falo sukaci karo da Yoohan da shigowarsa gidan kenan shima, jin babu motsinta a sashen ya sakashi leƙawa ɗakinta ko barci takeyi. Sai ya sami ɗakin wayam.
Sam baiga daga ina ta fitoba. Jinta kawai yay a jikinsa a bazata, hakan ya sakashi yin baya suka faɗa a kujera a tare, yana ƙasa tana a samansa. Riƙeta yay da ƙyau yana matse ido dan yaji zafi a kafaɗunsa, in kuma ya saketa zata faɗi, itama a firgicen da takene ya sakata mamuƙesa yanda ya kamata, har yana jiyo yanda zuciyarta ke gudu akan ƙirjinsa. Kusan mintuna uku suna a haka, sai da ya tabbatar bugun zuciyarta ya dai-daita yanda ya kamata sannan ya tura hannunsa cikin gashinta, gyalen jallabiyar ya zame. Saurin yunƙurawa tai tana ƙoƙarin ture masa hannun. “Nikam minene haka kuma?”. Ta faɗa tana kumbura fuska.
Bai kulata ba, ya cigaba da tura hannunsa har sai da ribbon ɗin data ɗaure gashin ta fita gaba ɗaya gashin ya baje. Ƙara yunƙurawa tai da zafin nama zata raba jikinta da nasa ya maidata suka sake mannewa. Zatai magana yay saurin faɗin, “Shiiii!!”. Bata fuskar ta sakeyi da cewa, “Toni ka sakeni na tashi”.
Batare da ya saketanba yace, “Daga ina kike haka?”.
“Babu ko ina, tsoratani akayi”.
Ta bashi amsa tana ƙoƙarin sake tashin, maidata yayi fuskarta gab da tashi har hancinsu na gab da gogar na juna. Duk yanda taso yin tsiwar tata sai ta gaza. Dan yanda ya sarƙeta da mayun idanunsa, ga numfashinsa da yake busa mata yana zuƙar nata shima sai taji kamar ya wani ɗaɗɗauretane da igiyoyi, ga wani shegen kwarjini da yay mata da cika idanu. A takema ta fara jin kasala na saukar mata.
Ƙofar falon da aka buɗe ne ya sakasu sauke ajiyar zuciya a tare, ido huɗu sukayi da papa daya shigo da gani kasan a rikice yake. Nu'aymah tai azamar yunƙurawa zata tashi daga jikin Yoohan. Shima sakinta yay saboda ganin a yanda papan ya shigo.
Papa ko da kallo ɗaya yay musu ya ɗan kauda kansa sai ya sami kansa da sauke numfashi. dan a yanda ya gansu kawai ya tabbatar masa ba ɗaya daga cikinsu bane ya shigar masa ɗaki kamar yanda yay zargi daga farko.
“Papa lafiya kuwa?”. Yoohan ya faɗa yana sauke Aymah dake ƙoƙarin barin jikinsa a hankali”. Da sauri papa yace, “No Son karka damu, kuyi haƙuri na shigo muku babu knocking ”.
“Babu damuwa papa. Amma inji dai ba wani abune ya faru ba ko?”. dafe kai papa yayi dan duk ya shiga ruɗani. Yace, “John ni nama kasa fahimta gaba ɗaya, mune a ruɗe kokuwa abinda mukai tunanine a gaske?. Kawaifa muna zaune da baƙona sai mukaga kamar mutum ya fito a bedroom ɗina. Mun duba ko ina na gidan nan kuma amma babu alamar kowa. Maigadi ma ya tabbatar mana shi baiga kowa ba sai kai daka shigo tun ɗazun”.
Kafin Yoohan yay magana Aymah tai saurin faɗin, “Yes papa nima naga mutum, ina kitchen zan dafa noodles naji gudu an sakko daga downstairs, shinefa na tsorata na shigo da gudu na zatama ɓarayine ko aljanu”.
“Daughter da gaske?”.
“Eh papa, da gaske naga mutum ya fita da gudu”. Tai maganar tana satar kallon Yoohan ta ƙasan ido.
Daga Yoohan har papa sun yarda da zancen Aymah, hakan yasa duk suka fito har ita da keta faman maƙalewa bayan Yoohan wai a dole tsoro takeji (😂wagga ɗiya ko).
Tsaf Nu'aymah ta saka papa da Maigadi da Yoohan da Andrew zagaye gidan nan duk faɗinsa. Tana kuma biye dasu kamar jela. Sai dai babu ko alamun wani yama shigo gidan balle maganarta ta tabbata.
Dafe goshi Yoohan yayi yana faɗin, “Papa wannan shi nake faɗa maka a koda yaushe. Ka daina saka guards ɗin gidannan gaba ɗaya tafiya church, taya za'ace maigadi ne kawai za'a bari a gida bayan wasu su irin wannan damar suke nema. Dolene a sake tsari dan wannan tsarin baiyiba na shigo mana da kowa cikin gida”. Ya ƙare maganar da kama hannun Nu'aymah suka shige ciki.
Daga papa har Andrew dake lasar baki tun ganin Aymah da kallo suka bisa. Kasa haƙuri kuwa Andrew ɗin yayi, ya shiga tambayar papa ina suka samo wannan ƙyaƙyƙyawar young lady ɗin haka?. Duk da takaici daya kama papa sai da ya bama Andrew amsa da cewar daughter in-low ɗinsa ce. Da yake baisan Yoohan ɗin yayi aureba, dan papa bai tura masa invitation ba. Kai duk ma abokan harƙalarsa ta bayan fage bai gayyacesu wajen taron ba.
Ciki suka koma ya sallami Andrew dan maganganun Yoohan ne ke neman masa tasiri a cikin zuciya. Idan har ya fahimta dai-dai Yoohan yana zargin wani shirine da Andrew kenan? Maybe shine ya shigo da wani batare da shi ya sani ba saboda wani dalilinsa. Wannan tunanin da yay masa tasiri ne ya sakashi bincike tun daga bedroom ɗinsa har falon gaba ɗaya. sai dai baiga wata alama ta wani abunda zarginsa ke a kai ba. Amma duk da haka bazai sakankance ba kai tsaye. Dan haka ya canja password ɗin kwaba ɗinsa ta sirri yama ƙara mata wasu securitys ɗin.
Aymah kam suna shiga ta zare hannunta cikin na Yoohan ta kwasa da gudu zuwa bedroom ɗinta tana faɗin, “Fitsari nakeji”.
Da kallo kawai ya bita harta banko ƙofar, ya ɗan girgiza kansa da ƙarasawa cikin falon ya zube akan kujera yana furzar da iskar ɓacin ran kwashe-kwshen papa. Baisan daga ina kuma ya kwaso musu wannan mai suffar marasa imanin ba.
Koda Aymah ta shiga ɗaki bata iya tsayawa a bedroom ɗin ba, dan tunaninta Yoohan zai iya biyota nan. Toilet ta shiga ta maida ƙofar ta rufe da murza key har sau biyu. Sai da ta tabbatar tayi gam sannan ta ɗaga rigarta ta zaro hoton da duk ya lanƙwashe. Bata damuba, sai tsuramasa idanu da tayi ko ƙyaftawa babu. Ba kowa bane a hoton face papa yana ɗanyen matashi jagab, sai ƙyaƙyƙyawar balarabiya mai tsananin kama da Yoohan a gefensa da shekarunta bazasu wuce sha tara zuwa ashirin ba. Da cikinta tsoho wanda yay mata ɗas a jiki. Hannunta dana papa duk akan cikin suna murmushi.
A take wani gumi ya fara karyoma Nu'aymah, ta nuna balarabiyar da ɗan yatsa bakinta nason furta magana amma ta kasa. Sai a zuciyarta zantuttukan keta kaiwa da kawowa na mamaki, al'ajabi, ruɗani, harma da firgici. ‘To mi hakan ke nufi?’. Ta ambata a fili da ƙyar.
Harga ALLAH man kanta fa yana neman kwararewa a ƙasa, dan haka ta jingina da ƙofar tana furzar da huci mai zafi tare da sharce gumin daya taru mata a goshi. ‘Tabbas akwai magana kenan. Wacece wannan tare da babansa? Sannan kenan wannan matar dake a gidan itace ta haifesa da gaske? Kokuwa yaya abin yake?’.
Waɗan nan tambayoyi suke sake rikitar da ita da hautsina mata man kai da ruwan kwanya awaje guda.....
Maganganu take ɗanji sama-sama kamar a cikin ɗakinta, hakanne ya sakata leƙawa ta kafar mukulli bayan ta zaresa a hankali. Momy ce ke magana a faɗa-faɗa. “My Son wai yaya ma zaku yarda da zancen yarinyarnan cewar wai taga wani. Sai dai idan itace da kanta ta shiga take neman raina muku hankali. tayaya idan ba ita baceba za'a kulle Miracle ta baya bayan kuma Joy ta tabbatar mana bata kulleta ba, ita kuma gashi tace babu key a cikin ɗakin”.
Idanu Aymah ta zaro waje, tai saurin kallon yatsanta da key ke maƙale wanda bana ko ina bane sai na ƙofar ɗakin su Mira data kulle. Gaba ɗaya tama manta da shi a hannunta. Kanta ta dafe dan ganin key na neman jiƙa mata aiki bayan ta tsalake rijiya da baya........
Cikin ɗacin murya da Yoohan ya fara magana ya katsema Aymah tunaninta... “Momy Please, banajin daɗin irin waɗanan maganganun naki akan matata. Taya zakice itace? Idan kince ita ɗince ma mita sani akan gidan nan da har zataje sashen papa kuma harma cikin bedroom ɗinsa? Mima zatayi acan?”.
Dariya sosai ya bata ganin yanda ya haƙiƙance akan abinda bai saniba wai shi nan mai mata. Taima ƙofar gwalo tare da jefa key ɗin cikin toilet tai flushing ɗinsa, sannan ta cire rigarta ta naɗe hoton a ciki ta hau yin wankanta hankali kwance. A ranta tana addu'ar ALLAH ma yasa kar a samu key ɗin buɗe Mira. Tun tana cigaba da jiyosu sama-sama har taji tsit. Ɗauraye jikinta tayi taja rigar wanka ta saka. Dama ta ƙirƙiri wankan ne dan batason fita ta haɗu da madam Chioma.
Koda ta fito bata samesu a ɗakin ba, hakanne ya bata damar ɓoye hotan sannan ta sake sabon shiri ta fita dan yunwa takeji batayi breakfast ɗin ƙwarai ba ta tafi ɗaukar magana.
Duk da hangosa da tayi a saman dining ɗin bata fasa nufar can ba. Sarai shima ɗin yaji motsinta amma ya basar yana cigaba da danna waya. ayaba da gyaɗa a gabansa. Bowl ɗin data haɗa madarar ɗazun ta ɗauka takai kicin, zubashi tayi a ƙaramar tukunya ta ɗora kan gas, tana tsaye sai da ya tafasa sannan ta juyosa ta fito. Inda ta barsa nan ta sake taddashi. Yanzun kam duk yanda taso haɗiye maganar dake bakinta ta kasa sai da ta tanka. ƙasa-ƙasa tace, ‘Yau ina ganin ƙazanta, wai ayaba akeci da gyaɗa’.
Shi dai baima jitanba balle yasan da shi take tunda da hausa tai maganar. Itama daga haka bata sake tankawaba ta zauna ta fara shan madarar data dafo. Kansa ya ɗago ya kalleta a karo na farko, kamar zaiyi magana sai kuma ya fasa ya maida kansa ga wayar.
Gyaran murya ta ɗanyi, hakanne ya sakashi ɗagowa ya sake kallonta. Ta wani ɓata fuska irin bata son wargin nan. Shi dai baice uffanba. Lura da tai ba magana zaiyiba yasata faɗin, “Uhhm ni dai gaskiya zan dinga girka abincina anan ni kaɗai, dan ban iya cin waɗan nan abincin naku ba”.
Idanunsa ya ɗan lumshe ya buɗe a kanta, batare da yace komaiba ya maida kansa a kan wayarsa. A ƙufule tace, “Dan ALLAH Yah Yoohan”.
Duk yanda yaso basarwa hakan ya gagara. Karon farko a rayuwarsa da yaji sunansa a bakinta. Sannan yasan a hausance kalmar Yaya dai girmamawace ga wanda aka kira da ita. A hankali ya lumshe idanunsa ya buɗesu a kanta, yana binta da wani narkakken kallo data gagara fahimtar ma'anarsa. Kamar mai ciwon baki yace,
“Naji”
Ya bata amsa a taƙaice, dan har yanzu ransa a ɓace yake da zantuttukan Momy. Ita kuma mutuniyar taku da yake babu man kai ta kasa fahimtar ransa a ɓacen yake.
Shine ya fara bar mata wajen bayan ya cinye ayaba da gyaɗansa.
_________★★★★
Bayan sallar la'asar tana a ɗaki kwance tanata faman ƙullawa da kwancewa akan yanda zata ɓulloma Yoohan da tambaya game da sanin matsayin Momy a garesa ya shigo. Harya ƙaraso gaban gadon bata sani ba. Sai da ya zauna ne jikinsa ya taɓa mata hannu sannan tai firgigit. Da sauri ta miƙe zaune tana cika baki da iska. Bakinsa ya taɓe da kauda kansa yana lumshe idanu.
“Ki shirya muje”
Ya tari numfashinta ganin zatai magana. Shi kuma baya buƙatar surutun sam. Haka yake idan abu ya ɓata masa rai, sai ya wuni yana ɗacin rai. Hakan yasa mafi yawan lokaci ƴan gidan suke gaza gane kansa. Ita kanta Aymah ganin har yanzu fuskar tasa a tsuke kamar ɗazun duk sai taji shakkar masa tsiwar tata. Duk da ma dai har ranta taji daɗin jin fita zasuyi.
Fita yay alamar bata damar shiryawa. Aiko cike da ɗoki ta shiga neman kayan canjawa. Tana cikin zarowa Yoohan na sake shigowa ɗakin. Kallonsa tayi da sauri, zatai magana sai dai ta kasa saboda cin karo da fuskarsa dake a matuƙar tsuke. Cikin kaushin murya yace, “Idan kin shirya ki sameni a waje”.
Kanta ta ɗaga masa dan bataga fuskar yin wargi ba. Yana fita ta sauke ajiyar zuciya. A ranta duk sai taji babu daɗi, dan tasan abinda ya saka masa ɓacin ran dai da gaske ta aikata, amma yanata ƙoƙarin kareta a wajensu har yana saka kansa a ɓacin rai irin haka.
Da ɗan hanzarinta tai shiri cikin wata doguwar rigar jallabiyar, amma yanzu baƙa. Taji adon blue stones sai ƙyalli da ɗaukar idanu takeyi. Bata wani tsaya ɓata lokaci ba ta saka hula da naɗa madaidaicin blue gyalen daya shiga da adon stones da akaima rigar. Taɗan gyara fuskarta tasa takalma ta fito tana ƙamshinta mai sanyi.
A sashen ta fito gaba ɗaya tana karanta:
اَللَّهُمَّ إِنَّا نَجْعَلُكَ فِي نُحُورِهِمْ، وَنَعُوذُ بِكَ مِنْ شُرورِهِمْ .
Allahumma inna naj'aluka fee nuhoorihim wana'oothu bika min shuroorihim.
Baƙi sosai ta samu a falon ƴan ziyarar Sunday. A taƙaice tace musu “Good Afternoon” dan taga akwai manya. Batare data jira sanin waɗanda suka amsaba tai ficewarta. A harabar gidanma dai duk baƙin fuska taita cin karo da su. Wasu ta gaishesu wasu tai wucewarta.
Da sauri Gebrail dake jikin motar da Yoohan ke a ciki ya buɗe mata ƙofa yana wani rissinar da kai kamar gaske. A ranta tace, ‘Munafuki dan ka gansa a wajen kake wani acting like mutumin ƙwarai. Zanyi maganinka ne ai, bara na gama da na sama da kai’.
Tana shiga ya maida ƙofar ya rufe tare da leƙowa. a marairaice yace, “Please Brother na shigo muje tare?”.
Wata banzar harara Yoohan ya watsa masa. Saurin barin jikin motar yay yana ɓata fuska. A ransa kuwa wani irin wutar son Aymah ce ke ruruwa masa a zuciya tare dajin zafin Yayan nasa mai share kukansa a koda yaushe wajen magance masa bukatunsa. Da ƙyar ya iya nufar garden inda abokansa suke zaune da giyar da zasu sha ransa duk a ƙuntace. Dan tabbas yanaji a ransa bazai iya haƙuri ya barma Yayan nasa zuƙeƙiyar yarinyarnan datai dai-dai da burinsa ba. Shi musilincinta ko yarenta duk ba damuwarsa ba. Itaɗin yake so, so irin wanda ke shiga ɗin nan farat ɗaya a zuciya batare da yayi shawara da mai zuciyar ba. Dan a kallo ɗaya da yayma Aymah a wajen dinner tai masa shigar corona virus a zuciya. Bakuma tayi sanya ba wajen mamaye dukan zuciyarsa da ilahirin jikinsa. Dan haka koda bala'i sai ya mallaketa, sai ya ɗanɗani zumarta, sai ya ɗanɗana mata tashi kuma. Yanaji a ransa zata soshi fiye da Brother Yoohan inhar ya bayyana masa abinda ke cikin zuciyarsa game da ita..............✍
😸Wa yaga kwamatsala ɗan Nageriya da mulkin Amuruka😜.
Leave a Comment