Saran Boye 53
No. 53
...............Kamar yanda Yoohan ya faɗa da safe basu haɗu da Aymah ba, dan sammakon barin gidan yayi saboda tafiyar tasa ta gaggawa ce. Zasuyi aikine wa wani shararren ƙusa a gwamnatin UK da aka shaƙama poison a wani taro da yaje ƙasar China. Shima tafiyar tazo masa ne a gaɓar da bai so ba. Dan dama yana shirin ɗaukar hutune saboda fita da zaiyi da Nu'aymah wajen nata aikin itama. Ya kuma ƙiyasta zai ɗauki tsahon wata guda kafin komai ya dai-daita yanda yake buƙata a yanda yay fata. To sai gashi kuma an ɓata masa budget. Dolene kuma yaje wannan nema, sai dai idan ya dawo ya sake sabon tsari.
Da safen koda Aymah ta fito domin yin gyara sai taita laƙe-leƙe a ɗarare. Sai dai taji ko'ina tsit alamar dai baya gidan. Badai ta saki jikiba harta kammala aikin gyara sashen. Ganin bai fitoba ya sata rumtse idanu ta leƙa ɗakinsa. Shiru babu kowa sai kayansa daya cire na barci a saman gado. Da wasu ƴan abubuwan da baza'a rasaba da ya bari saboda saurin karsu makara.
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali duk da ita bawai taji farin ciki a tafiyar tasa bane. Sai dai koba komai ta samu rangwamen kunyar daya aza mata a yammacin jiya da har a yanzu idan ta tuna ita kanta kunyar kanta takeji dan bai taɓa mata irin kalar k... Ɗinnan ba.
Ɗakin ta gyara masa, ta tattare kayan cikinsa daya tara alamar bai samu damar wankewa ba tana tura baki. Kamar ta bar masa kayansa sai kuma ta tuna ya saya mata waya. Baki cike da iska tace, ‘Wlhy badan halinkaba dai. Dan kar ace banda kirki ka saimin waya mai tsada ni kuma naƙi maka wanki, da a haka zan barmaka abunka’.
Fitowa tai da su takai toilet ɗin ɗakinta ta ajiye da nufin sai anjima zata haɗa da kayanta data cire ta wankesu.
★★★-----★★★
Yau satin Nu'aymah biyu kenan a gidan su Yoohan matsayin matarsa. Yayinda Uwaliya keda kwana biyar. Zuwan Uwaliya ya sake bama Aymah damar fahimtar halayyar mutanen gidan sosai. Sannan tana samun abokiyar ɗebe kewa. Dan sosai suka saki jiki da juna ita da Uwaliya. Uwaliya nada wayewar kai sosai saboda yawon da suka ɗanyi da tsohon mijinta kasancewarsa ɗan sanda, tanajin turanci kuma. hakan yasa rashin Yoohan a gidan bai cika damunta ba tunda dama bawani zaman arziƙine ke haɗasu ba da shi a kwanakin da suka kasance tare.
Yanzu tanayin abinci a sashenta, dan haka babu ruwansu da abincin gidan. Sai dai idan akayi wani abu na musamman a gidan Blessing bata gajiyawa wajen kawoma Aymah. Dan ita dai haka kawai ALLAH ya jefa mata son Nu'aymah. Wani lokacinma dan kawai tazo sashen nata take ƙirƙirar yin abu. Wannan shigowa jikinta da Blessing keyi yaɗan saka sabo tsakaninta da Aymah har tana samun wasu bayanai akan gidan da tsarin zamansa.
Kamar yanda akeyo cefane wa mutanen gidan haka itama ake kawo mata nata cefanan dan dama dai Yoohan ne maiyi. Tunda ya fara aiki ya saukema papa wannan nauyin. TA yanzu ma tunda Momy takai masa ƙarar Aymah nayin girki a sashenta sai maimakon ya hana kamar yanda madam Chioma taso, sai gani tai washe gari Blessing da Sj sun dawo kasuwa da uban cefane har kashi biyu. Sj yakai nasu kitchen ɗinsu Blessing ta nufi kaima Aymah.
Tsaidata Momy tayi tana tamabar ina zata dasu?. Cikin girmamawa Blessing taima madam Chioma bayanin cewar Yoohan ya kirata tare da turoma SJ kuɗin cefane kashi biyu. Ayi nasu, akumayima Nu'aymah itama.
Ba ƙaramin sosa ran Momy wannan al'amari yayiba. Dan haka da kanta ta nufi sashem Aymah. Lokacin suna falo Uwaliya na mata kitso dan kanta ya isheta sai ƙaiƙayi yake mata saboda rashin kitson duk da basonshi take ba. Ko sallama babu ta banko musu ƙofar. Uwaliya ce kawai ta zabura gefe jikinta na rawa. Dan ita harga ALLAH tsoron madam Chioma takeyi. Nu'aymah kam fuska ta haɗe tamau ta cigaba da game a wayarta da har yanzu taƙi bin Gebrail ya kaita tayo register layin da Yoohan yace. Sai ka rantse da ALLAH bataji shigowar Momy ba.
Wannan shariya ta sake tunzura zuciyar madam Chioma. Da matuƙar masifa tace, “K! Bakiji shigowata bane ba?”.
Sake watsar da ita Aymah tayi tsahon sakanni kafin ta ɗago idanunta tana ajiye wayar tata da Momy kebi da kallo kamar idanunta zasu faɗo ƙasa. “Momy a ƙa'ida babu wani addini daya yarda da shiga waje babu neman izini. Sai dai bansan a al'adunku ba ko baku da wannan tarbiyyar. Dan haka a matsayinki na babba gareni, ni ya kamata nai wannan kuskuren kimin gyara, ni kuma idan su Victoria sunyi na gyara musu”.
Wani irin mugun gurnani madam Chioma tayi, a ranta tana raya ‘Dolene taci uban yarinyarnan la'ada waje’. A fili kam saita zuba mata wani mummunan kallo da a tunaninta zai razana Aymah. sai dai ko gezau a idon mutuniyar taku. Saima tsatstsare ta da idanu data sakeyi tana karanto addu'ar neman tsarin ALLAH daga sharrinta a zuciyarta.
“Yarinya basai kin ƙara tabbatar min ƴaƴan hausawan arewa baku da tarbiyya ba. Ba akan wannan nazo nanba. So nake naji dalilinki na saka my son yo miki cefane ke ɗaya bayan gaba ɗaya ake girki a gidan nan da kowa”.
Baki Aymah ta taɓe tana zama saman kujera. Kanta taɗan dafe kafin ta sake duban Momy. “Oh my GOD! Ƴaƴan hausawa ginin ALLAH. To momy wannan kuma ai tsakanin mata da mijinta ne. Yanzu a gidan nan ko Mama debora ta isa jin tsakaninki da papa ne?. Inaga ki kirasa zakifi jin komai daga bakinsa yanda ya kamata kamar”.
Ta ɗauke kanta tana maidawa ga Uwaliya da kanta ke a ƙasa ita da Blessing dake can bakin ƙofa. Saika rantse ba itace tai maganarba. “Uwaliya Please zomu ƙarasa kitson nan inada abinyi, inba hakaba na banbance tarbiyyar hausawa data aljihun baya dan wlhy ni babu ruwana da matsayin kowa gidan nan”.
Baki Momy ta buɗe a matuƙar hasale zatai magana dan da turanci Aymah ta faɗa, Papa ya shigo falon. Tsawa ya daka mata cikin yare yake magana a fusace batare da Aymah da Uwaliya sunji mi yake faɗa ba. Ita kanta Blessing batajin yaren dan su papa sunajin yaruka kusan uku ne.
Gani sukai kawai yaja hannun Momy sun fice tana kumfar baki kamar zata haɗiye harshenta. Su Blessing dai basu motsaba, Aymah kam da uwar harara ta raka bayansu tana jan tsaki. Daga ƙarshema ta tashi ta shige bedroom kitson da ba'a ƙarasaba kenan.
Washe gari da safe papa ya aiko Abraham kiran Aymah. A yanda yaron ya shigo musu babu sallama babu gaisuwa yana magana a gadara ne ya bata haushi. Tako tashi ta tallare masa ƙeya da kama kunnensa ta murɗe tana faɗin. “Kai dan ƙaniyarka ƙaracin tarbiyya yasaka banbance na gaba da kai ne? Ko Muhammad ɗina ya girmeka amma kake neman saka kanka a filin yaƙin da ko uwarka tamin ƙaɗan wajen gwajin ƙwanji”.
Kuka Abraham ya fasa. Aymah ta sake talle ƙeyar tana nuna masa hanya. “Ficemin anan kafin na maka ɓalli-ɓalli a waɗanan shegun kumatun samfarin gurasar kano”.
Da gudu yaron ya fita yana kuka. Itakuma ta juya bedroom ɗinta tana bambamin masifa akan wlhy dai-dai take da ƙugun duk wanda yace shi shegene a gidan. Babu mai sakama rayuwarta kahon zuƙa ya tsira. Dan zuru bata cin zuru sai dai a haɗu ai zuru-zuru.
Itadai Uwaliya binta kawai tai da kallo tana jinjina ƙarfin zuciyarta da tsaurin ido. Sam yarinyar bata da tsoro kamar dangin ifiritu. A fili tace, ‘Koda yake tun kina ciki an gama tsumeki da addu'oi shiyyasa’.
A falon papa ta iske Momy na banbamin jaraba ga Abraham na sharɓar kuka. Dama ta wuto su Joy na nasu masifar a downstairs kuma tasan duk akanta ne. Kallo ɗaya papa yayma fuskarta shi kansa yaji shakkarta. Duk da kasancewarta ƙaramar yarinya kwarjinita na tada masa hankali dan kallon mahaifinta yake mata. Zama tai tana gaishesa batare data kalli ko sashen da Momy take ba. Ya amsa mata da kulawa.
“Daughter miya haɗaki da ɗan ƙanin nakine?”.
Zuciyar Aymah ta gado a ƙirji take. Dan haka tama manta da matsayin wani papa. Cikin ɗacin rai da rufewar idanu tace, “Papa har wannan ɗan mitsitsin yaron yakai girman da zai dinga kawomin raini a gidan nan? Tunda nake bai taɓa gaidani ba. Hakan yasa sam bana shiga sabgarsa. Shine tsabar rainin wayo yanzu yaje yana min magana a tsaitsaye kamar wata sa'arsa, shiyyasa naga ya dace na fara koya masa tarbiya idan wadda aka bashi bata ishesa ba, dan.........”
A wani irin harzuƙe Momy ta katseta. “Yaƙi ya gaishekin? Ke kina girmama nagaba dake ɗinne?”.
“Tabbas ina girmama nagaba dani Momy, sai dai fa inhar shi wannna na sama dani ɗin ya nunamin shekaruna da nasa babu banbanci to wlhy zan bi na taka shima na koyar dashi tarbiyyar daya rasa tun ƙuruciya. Kuma wlhy inhar Abraham baya gaisheni a gidannan, koya sake rainani saina sakasa a makarantar jiki magayi a gidanan a kuma gabanki”.
Ba Momy ba hatta papa lamarin Aymah tsoro ya ƙara bashi. Sai faman jinjina kai yake yana magana da zuciyarsa. ‘Like Father like daughter. Lallai John ya ɗakko mana shugabar ƴan boko haram a gidan. dan kuwa tabbas jinin Sooraj dama bazai kasance na banza ba’. A fili ko sai yaya saurin dakatar da Momy da taso yin magana. “Ya isa Darling. Bakiga yarinya bace ita. bai kamata ki biyetaba. Kuma tama fimu gaskiya. shi Abraham ɗin miyasa baya gaisheta?”.
Nanfa ya shiga yima Abraham faɗa sosai, ya kuma sakashi bama Aymah haƙuri dole. Itama Momy akan abinda ya faru jiya yay mata sulhu da Nu'aymah. Yasa Aymah bata haƙuri, ya kuma jama Momy gargaɗi akan shiga sabgar Nu'aymah inhar ba wadda ta kasance ƙyaƙyƙyawa ba.
Hakan ya sake cima Momy rai akan yarinyar. Amma sai tayi shiru saboda maganar da suka tattauna da papan a daren jiya gameda shirinsu akan mahaifin Aymah dama ita kanta da zasu raba da ɗansu nanda lokaci ƙanƙani.
Daga haka ya sallameta ta tafi. A wannan yinin kaf Nu'aymah tayisa cikin ƙunci ne a gidan. Tare da ɗaukar alwashi kala-kala ga duk jama'ar gidan. Dan ta rantse da gemun baba malam duk sai ta gasa musu aya a hannu. Papa ne kawai zai tsira a cikinsu shima idan yaso.
Dalilin wannan rikici Nu'aymah ta sake tsumewa kowa a gidan. Bata da abokin hira sai Uwaliya sai ko Blessing dasu Destiny dake fakar ido idan su mama debora basa falo su shigo mata. Ko kuma idan ta fita harabar gidan shan iska. Dan yanzu da gadara ma take fitowa har falon ƙasan ko harabar gidan ko garden ta zauna tana latse-latse a wayar da babu sim card a ciki koda kuwa suna zaune a wajen. Kota duba buks ɗinta na boko kona islamiyya. Kosu zauna da Uwaliya suyi hira idan sun gama aiki tunda yazam aikin nasu bawani mai wahalarwa bane ba. Komai tare sukeyi da Uwaliya, ɗakin Yoohan ne dai bata taɓa bama Uwaliya damar ko taɓa murfinba. ɗakinta ma itace ke gyara abinta, sai dai wani dalili yakai Uwaliya ciki amma badan aiki ba. Abinci ma kusan Aymah keyin abinta, sai dai Uwaliyan na tayata.
Kullum sai tayi waya da Umm da Baba malam da Hajjo a wayar Uwaliya. Yoohan kam basu taɓa waya ba tunda ya tafi, ita harma mantawa take da lamarinsa. sai dai duk sanda zata sha chocolate sai abinda ya faru tsakaninsu akanta ya faɗo mata a rai. Haka kawai abin kan sakata murmushi, kokuma taita ƙunƙuni tana kiransa ƙazami mayen baki.
Bata taɓama kowa zancen hoton data ɗakko a ɗakin papa ba, tundama ta ɓoyesa bata sake waiwayarsa ba. duk da kuwa batunsa na nan damar cikin zuciyarta. A dalilin hakannema ya sata mugun sakama duk wani motsi na madam Chioma da papa a gidan idanu. Tanason ta gano ainahin gaskiyar abinda ranta ke raya mata game da madam Chioma ba itace mahaifiyarsa ba. Abinda Aymah ta fara fahimta shine akwai wani haramtaccen business da papa keyi a ɓoye da Yoohan baisan da shiba. Dan inhar Yoohan yana a gari komansa yakan zama taka tsan-tsan. Amma yanzu da baya nan sai take ganin wasu baƙin halaye muraran ga papan duk da bawai yana fitowa fili yanayi bane, sai idan ka kasance mai lura sosai kamar ita data saka masa idon mikiya ne zaka fahimta.
Wannan ne ya saka ƙaramin tunaninta sake faɗaɗa, harta kasa haƙuri suna waya da baba malam take faɗa masa ita lamarin papan Yoohan na bata tsoro. Da yake dama baba malam ɗinne yay mata tambayar akan papan cikin hikima. Koda ta faɗi hakan dariya kawai yayi, bai tambayeta mita gani ba ko dalilinta nacewar hakan sukai sallama.
Daga ranar kuma baba malam bai sake takalar Aymah da zancen papa ba. Itama kuma bata sake masa ba ta cigaba da hidimarta.
__________★
Yau ta kasance asabar. Kusan ƙarfe sha biyu sai ga su Amal Yah Omar ya kawo mata su. Wayyo zokaga murna kamar zata tashi sama danjin daɗi. Hatta Adawiya da Abbah ya tilastama biyosu dan dole Aymah sai da ta rungumeta. Ranar dai ƴan gidan sunsha kallo dan duk suna gida. Gebrail le kawai yanacan gantalinsa da abokai tunda babu makaranta.
Jama'ar gidan sun sake yarda Nu'aymah bata fito a ƙaramin gida ba, dan motar da Omar ya kawo su Yusrah a ciki kawai ta isa shaida. Ga uban tsaraba da suka shigo dashi kamar sunzo daga wani garine. Nasu daban na Aymah daban kuma.
Adawiya dai nata kallon makeken gidan da aka kawo Aymah a ciki, musamman sashen Aymah daya tsaru da irin burinta da buƙatarta. Tasan iyayensu nada kuɗi sosai, dukda ta taɓa jin ƙishin-ƙishin a gidansu akan kaso biyu na dukiyar gidansu mallakin baba malam ce. Amma sai taji kamar Aymah ta sake samun matsayine sama dana gidansu duk da tana a tsakkiyar waɗan nan mutanen da babu ALLAH a ransu.
Kayan ƙwalam da maƙulashe ta ɗebo musu sukaci iya cinsu suna kwasar hira cike da farin ciki. Adawiya ce dai data saka kanta a uku bata cewa komai. Suko sun watsar da ita sunata sabgoginsu.
Bayan sallar la'asar Aymah tace su shirya su rakata mtn office tayo register layinta ta ɗora a wayarta da suketa faman santi saboda haɗuwarta. Dan ganin wayarnan sai da ya saka idanun Adawiya cika da ƙwallar baƙin ciki. Duk abinda taima kanta buri da fata sai taga Aymah ta fara samunsa kafin ita. Yah Ab ne kawai tayi nasar ƙwace mata. Shima gashi ya suɓuce mata a daidai lokacin da Nu'aymahr ta samu wanda ya fisa komai. Dan ƙyaƙyƙyawar nasaba ce kawai Abdallah zai bugi ƙirji yace yafi Yoohan da ita.
Kan Nu'aymah tsaye taje ta sanarma drivern gidan zai kaisu anguwa. Duk da tsoron madam Chioma dake a ransa haka ya amsa mata saboda uban kwarjinin datai masa a idanu. Itako bama ta damu da halin da yake a cikiba. Ta miƙa masa ɗaya daga cikin keys ɗin motar Yoohan data ɗakko a ɗakinsa. Idanu ya zaro sosai cikin rawar jiki yake, “Madam ai ko oga sau biyu kawai ya taɓa shiga motarnan, kuma da kansa yay driving, duk guri kuma na musamman yaje a ciki”.
Wani shegen harara ta zuba masa tana kallonsa a iskance. “Kai dokar ogan ta dama. Dalla amshi key muje banason ƙananun magana. Motar wofi makamin mutuwa da har za'a wani zauna yin tsarin shigarta. Koshi ogan naka ya zama mota hawa zanyi na zaga duniya nai kallo mtsoww!”.
Amsa yayi dole dan yasan jarabar Aymah tafi gaban naƙi. Masu gidanma ba raga musu takeba balle shi da yake cin arziƙi. Sai dai kuma abinda Nu'aymah bata saniba shine suna fita guards ɗin Yoohan suma suka bisu a baya. Dan dokar Yoohan ɗince haka a garesu. Bata farga da su ba sai da sukaje har sukayo register ɗin suka fito. Aymah tasa aka kaisu wani wajen shan ice-creem dasu shawarma. Sai gab da magriba suka taso zasu tafi idonta ya sauka akan guards ɗin Yoohan ɗin. Wannan abu ya baƙanta mata rai. Amma sai bata tanka ba. A cewarta da ubangidan nasu zatayi shine dai-dai da ita. Sukam basu kai martabar ji daga gareta ba.
Sanda suka iso gidan har an idar da sallar magriba. Sun iske Omar ya dawo ɗaukar su Yusrah. Aiko ya balbalesu da faɗa musamman Nu'aymah da Yoohan ya tabbatar ma Omar a waya cewar baisan da fitarsu ba. Shima guards ɗinsa ne kawai suka kira suka sanar masa gata sun fita yasa su bi su.
Sai da ya ga tayi laushi da faɗan da yay mata sannan ya koma mata nasiha. Ya miƙa mata ATM yana faɗin, “Gashi inji Abbah. Zaki iya fitar da kuɗi yanzu a bank accaunt ɗinki. Saura kuma kiyi musu sukuwar salla kinji ko?”.
Baki ta tunzura gaba. “To ni indai ba saka kati ba a waya mi zanyi da su Yah Omar. Sai kuma idan inason shan ice-creem ne”.
Bugu ya kaima bakinta yana faɗin, “Oh maganar shegen ice-creem ɗin nan bazai bar shegen bakinkin nan mai kama dana tsutsa ba kenan”.
Saurin kaucewa tai tana sake kumbura fuska, ta kwasa da gudu batare da taga tafiyar tasu data so ganiba. Aiko Yusrah da Amal sai kwasar dariya suke daga cikin mota. Duk wannan abu a gaban idanu Joy da Miracle da Gebrail dake can gefe ya faru.
Cike da mamaki Gebrail yace, “Wai wannan ɗan yarinyar aka bama damar ciran kuɗi a bank yanda ta gadama. Amma mu ga Brother Yoohan ya hana a zuba mana kuɗin daya haura dubu hamsin tsabar ya rainamu”.
Joy tace, “Shegiyan yarinyar nan family ɗinta kudine da su shiyyasa takema mutane iskancin data so. Ni dama muyi joining ɗinta mu cinye kuɗin”.
Tsaki Gebrail yaja yana faɗin, “Mumu! Ance miki bata da basira ne kamar ke. Bayan kun nuna bakwa sonta sai ta yarda daku yanzu. Yaran arewa ɗin nan fa shegen wayone dasu more especially yaran Hausawa ɗin nan. Balle wannan mai aiki da aljanu ɗin nan, dan idanunta kamar na Google suke a gidan nan”.
Masifa Joy ta fara masa saboda yace mata Mumu. Nan take suka harƙume faɗa Miracle data tsunduma duniyar tunanin akan zancen kuɗin Nu'aymah ta shiga rabasu daga zaune dan har yanzu ƙafarta batai garau ba sosai. Ga tabon fashewar da tayi a baki akai mata ɗinki nan raɗam ya zame mata tambari😜😂.
_____________
Oho, Aymah bama tasan sunayi ba. Dan tana can ta ɗora layinta a waya tana jiran awannin da suka bata ta fara kira da shi su cika ta kira Umm da baba malam da hajjo dan tsabar zumuɗi. Kota Yoohan da ya sai wayarma ba'ayi bawon ALLAH😪.
Ganin dai lokacin yayi dare dole ta haƙura sai da safe. Tana kuwa idar da salla sai ga massege ya shigo mata. Ɗaukar wayar tayi ta duba. Ɗaya daga kamfani ɗaya kuma credit card ne aka lodo mata harna dubu biyar. Basai ta nema ba'asi ba, dan ta ga sunansa ne. Amma maimakon tai tunanin nemar lambarsa ta fara kiransa sai ta kira Umm ɗinta. Dan tasan baba malam kam yanzu yana massallaci bai fito ba.
★★★
Yau kwanaki biyu kenan da zuwan su Amal gidan, ranar litinin bayan sallar la'asar momy da su mama debora suka tafi church. Blessing taja Uwaliya suka tafi kasuwa cefane. Su joy kuwa suna school. Hakan yasa gidan yin shiru dan da alama ma Nu'aymah ita kaɗaice. Bata damuba dan ko tsoro bataji. sai ma ta buɗe data ta shiga cheating da su Yusrah dan yanzu duk ta koma harkokinta na yanar gizo numbers ɗin ƴan gidansu da ƙawayensu kuwa duk su Amal sun tura mata har ƴan orphanage. Hakan yasata sake samun abubuwan ɗebe kewa tanata hidimarta hankali kwance kamar bata da damuwar kowa a ranta.
Shiru babu wanda ya dawo har magriba ta rufa. Aymah dake ɗanjin ƙafarta na mata ciwo sama-sama tun a daren jiya ta miƙe da ƙyar tana yamutsa fuska dan tasan dai period ɗintane ke nuna alamun ya kusa zuwa. Alwala taje tayi tazo tai sallar magriba. Tana idarwa ta miƙe ta fito waje saboda motsi da taketa faman ji tun tana salla. ita a zatontama ko Uwaliya ce suka dawo. Sai dai a mamakinta sai bataga kowaba a falon, batare data damu ba ta juya ta koma cikin bedroom ɗinta bayan taje ta rufo ƙofar falon data gani a buɗe.
Tana shigowa ɗakin aka kashe fitila duhu ya mamaye ɗakin Tare da rungumota aka matse. Tashin hankali da ba'a saka masa rana. Duhu shine abu na biyu da Aymah ta tsana a rayuwarta bayan allura. Gashi yana mugun yin tasiri akan lalurarta. Aiko a take ta daddage ta ƙwalla wani irin gigitaccen ihu da sai da muryarta ta amsa kowanne kusurwa da bango da ke a cikin gidan...........✍
😱Tofa, wane hege ne zai ɓallo mana ruwa kuma Aymah?🙆🏻. Ga Dafta yayi nisan kiwo🤦🏻😫.
Leave a Comment