Saran Boye 58
No. 58
............Wani irin ɗumi ne mai daɗi da saka nutsuwa ya ratsa mata jiki. Ga ƙamshi mai kwantar da zuciya na tashi. Ɗaki ne ƙaton gaske da yaji ababen more rayuwa da birgewa. Ga wasu irin ƙwayayen wuta dake bada kalar blue, green, an purpule ƙanana. Idan wannan ta kawo sai ta dauke wannan ta kawo. Hakanne ya ƙara ƙawata ɗakin da adon da akai masa na musamman daya tilasta Aymah nutsuwa tana kallon komai daki-daki.
Jinsa a bayanta ya sakata juyowa ta ɗan kallesa, ganin ita yake kallo tai saurin janye idonta. Kafarta ta ɗaga ta cigaba da takawa tsakkiyar ɗakin inda aka ɗaura wasu balan-balan da sukaja hankalinta masu zubin love, dan kamar sunanta take hange a jikinsu.
A hankali takai hannu kansu dan kuwa tabbas sunanta ne a jiki. Tana taɓawa suka shiga fashewa da kansu har taɗan zabura dan tsoro. A bazata sai jin abu na zubo mata a jiki tayi mai ɗan karan ƙamshi. Tanason ta kalla amma yanda yake zubowar ya hanata damar hakan. Dole ta tsaya a waje guda kawai ta lumshe idanunta abin na cigaba da sauka a kanta tamkar ana fesoshi.
Tsahon mintuna biyu cif sannan ya daina zuba. Buɗe idanun tayi a hankali tana kallon ƙyawawan kalolin flowers ɗin dake zube a ƙasa alamar sune suka zubar mata a jiki. Samun kanta tai da tsugunnawa tasa hannu ta dumtsosu tare da kaiwa kan hancinta dan ƙamshinsu ya mata masifar daɗi..
Shaƙa tayi ta lumshe idanu wata irin nutsuwa na saukar mata. Ta buɗe a hankali tana ɗagowa ta kalli inda Yoohan ke taye jikin bango ƙafafunsa a harɗe. Hannayensa duka biyu cikin aljihun wandonsa yana mata wani irin kasallen kallo da lumshe idanu. Ga wani irin ƙyaƙyƙyawan murmushi akan fuskarsa.
Samun kanta tai da sakar masa wani lallausan murmushi itama batare data san kona minene ba. Ta miƙe a hankali tana takowa garesa har lokacin idonta dake cikin siririn farin gilashin na kansa. A fuska ta watsa masa fulawoyin cikin hannunta tana sakin siririyar dariya da fadin, “Kallon ya isa malami”.
Murmushin daya bayyana haƙiransa ne ya subuce masa. Ya miƙe tsaye da ƙyau batare da ya zare hannayensa a aljihunba ya nufota. Baya ta fara ja a hankali tana wani marmar da idanu kamar maijin tsoronsa. Haka suka cigaba da takawa tana yin baya yana binta har jikin ɗan ƙarfe da akai kwalliyar ɗakin da shi, inda aka sakar mata flowers ɗin nan. Jin ta dangane da shi ya sakata saurin yinƙurin barin wajen. Ruff taji abu ya rufesu dan shima dai-dai da isowarsa gab da ita. Saurin daga kai tayi ta dubi sama. Abu ne tamkar net ya lulluɓesu, hannu ta kai a hankali jikinsa, tamkar taɓawar tata ake jira dama ya fara juyawa yana dunƙulewa tamkar kwalba.
Idanunsa shima ya ɗaga yana kallon net ɗin tun daga sama harya sauke su a kanta a hankali. Ya tsatstsare ta da mayun idanunsa tare da ɗage hannayensa yana girgiza mata kai alamar shifa babu ruwansa. Dan wani irin kallon tuhuma take binsa da shai fuskarta a tsuke tabbacin ƴan tsiwar sun iso.
Taku biyu dake a tsakaninsu ya iso gabanta gab. Sosai ta matse bayanta da net ɗin ko nace kwalba a yanzu, dan daga wajema idan kana kallosu sai kace sun cikin kwalba kuma ruwa a ciki. laɓɓanta na motsawa kaɗan-kaɗan sai dai ta kasa cewa komai. Ya zare hannayensa daga cikin aljihu ya duƙa ya dimtso flowers ɗin shima. Ɗagowa yay ya watsa mata a fuska takar yanda tai masa. Baki ta tura gaba da share fuskarta, gefe da gefenta ya ɗora duka hannayensa biyu saman abun, saita koma tsakkiyar jikinsa.
Idanu sosai Nu'aymah ta zaro jikinta na wata irin tsuma da haɗe yawu da ƙyar. Saurin ɗago idanunta tai tana kallon nasa zatai magana........
Da wani irin sallo yay luuu da nasa idanun yana faɗin “Shiii!!!” a saitin kunnenta dan ya ɗan ranƙwafota. Sai dai jikinsa har yanzu bai taɓa nata ba.
Kasa maganar kuwa tayi, dan gaba ɗaya ya ƙure jarumtarta. Ba ƙaramin tasiri katangar da yay mata da jikinsa tayi a gareta ba. Ya shiga busa mata numfashinsa akan dokin wuya. Kafin ya fara magana a ahankali. “Inama ALLAH godiya, tare da taya kaina farin cikin samun lafiyar matata. Zeeynab ke ƴar baiwace......”
Nu'aymah bazata iya jurewa da salon Yoohan ba. Dan jikinta yama fara rawa. A hankali ta sulale tai ƙasa tana matse hannayenta da jikinta waje guda batare data ƙarasa jin abinda ya faro faɗa ba saboda tsigar jikinta data mimmiƙe a dalilin salonsa. A hankali yay ƙasa da idanunsa shima ya bita da kallo. Samun kansa yay da zamewa ya durƙushe a gabanta kamar yanda tayi. Da wannan damar ta samu duƙe fuskarta saman cinyoyinsa dan bata son su haɗa idanun. Sassanyan murmushi ya sauke da ɗaura duka hannayensa akan bayanta. Cikin sake raunana muryarsa yace, “I love you Nu'aymah. I love you sooooo!! much”.
Tabbas a bazata wannan kalma ta zoma Nu'aymah daga harshen Yoohan. Hakanne ya sakata ɗagowa a matuƙar razane, tare da idasa zama daɓat tana waro masa manyan idanunta tamkar wadda taji wata kalmar ban tsoro. Bakinta ta shiga motsawa a hankali, amma maganar ta gagara fita saboda tsabar firgici. Da wannan damar Yoohan yay amfani wajan matsar da fuskarsa gab da tata har suna shaƙa da busama juna numfashi. A bazata Aymah taji saukar tausasan laɓɓansa saman nata dake motsin son cewa wani abu amma hakan ya gagara.
Ba ƙaramin rikicewa ta sakeyi ba. Sai dai ya hanata kowacce irin damar ƙwatar kai. sai ma hannaunsa daya ɗaura ya dafe net ɗin yanda bata da damar motsawa. Idanma tace zata motsa ɗin a takure suke cikin net ɗin dan haka babu wata dama. Wani irin sirrin sumbata yake mata da ke neman jirkice ƙwaƙwalwar daya gama cetowa a kwanakin da suka gabata. A take jikinta ya hau rawa ta kasa daurewa sai da ta ƙanƙamesa. Iya rikitarwa Yoohan ya ruɗama Aymah jiki da tunani. Sai da ya tabbatar da laushinta a hannunsa sannan ya danna wani abu acan ƙasan net ɗin yay sama daga inda ya sakko ya barsu a fili.
Sunayen ALLAH kawai Nu'aymah ke maimaitawa da iya gudun fanfalaƙe da zuciyarta keyi, duk yanda Yoohan yaso ta ɗago ta kallesa ya tabbatar da sirrin tata zuciyar ya gagara. Dole ya ɗauketa cak ya kai bisa gadon da aka ƙawata da kayan ado ya kwantar. Yana ajiyeta ta kife da sauri batare data yarda tama kalli sashen da yake ba.
Murmushi yayi yana wani lumshe idanu da buɗewa. Cikin muryarsa dake a dasushe yace, “Zan baki damar ɗorani a mizanin da kikaga ya dace da burin tunaninki da tsarinki. Bazan taɓa miki tilasba, sai dai ki sani bazan taɓa iya haƙura ba. Ina sake jaddada miki ina SON KI!, so kuma da zamanmu ne kawai zai tabbatar miki da shi ba fatar baki na ba. Nima ki So ni domin ALLAH”. Yay maganar a cikin kunnenta. yana gama faɗa ya ɗago daga ranƙwafowar da yay a kanta.
Yayinda ita kuma ta kuma takure kanta waje guda zuciyarta na wani irin harbawa da sauri-sauri.
Gefen gadon ya koma ya zauna kawai yana kallonta, dan yanda ta cure jikinta waje ɗaya abin dariya. Ya dai daure baiyi dariyarba. Ƙarar door bell ce ta sakashi miƙewa yana gyara rigarsa da faɗin, “Oh God! ana jiranmu, taso muje”.
Duk yanda take bala'in jin kunyar haɗa ko hanya da shi balle akai ga ido sai da ta ɗago. “Ina kuma zamuje?”. Tai maganar da ɗan tura baki da waro idonu.
“Silly girl, taso kigani mana” ya bata amsa shima yana riƙo hannunta. Dole babu yanda ta iya haka ta miƙe tana gyara gyalen jallabiyar jikinta da ɗayan hannun. Ta gefen da take ɗauka labulene kawai ya kaita. Ya zaro handkerchief a aljihu ya zagaya bayanta. Ji kawai tayi ya ɗora mata akan ido alamar zai ɗaure.
“Wai kodai saidani zakayi ne?”.
Tai maganar tana son ture masa hannu.
Hannunta shima ya ture yana faɗin, “Kina ƴar tamilo ɗinan ko an saidaki namanki bazai ishi masu ci ba ai”.
Da sauri tace, “To nama fasa”.
Shima saurin riƙe mata hannu yayi yana danne dariyarsa ganin bakin ya fara buɗewa. “Sorry kowa zaici ya ƙoshi, kuma zakiyi daɗi”.
Shiru ta masa, sai dai bakin ya tashi sama alamar ta shaƙa. Shiko sai danne dariyarsa yakeyi dan bayason yayi ta birkice masa. Gani nayi ya danna wani abu sai ga labulen wajen dake bango guda ya zuge kansa ya koma gefe da gefe. Glass ya bayyana. Wanda ta cikinsa kake hango ainahin garin Vienna da ya gama haɗuwa da ƙayatattun gine-gine masu ban mamaki da al'ajabi. Kallonta yayi dai-dai ya sake danna wannan abun glass ɗin shima ya zuge ƙofar fita ta samu. Hannunta yaja suka fito ɗan barandan wajen dan ita dai ta zama makauniya.
Ni kaina sai da na ambaci masha ALLAH a zuciyata ganin yanda aka ƙawata barandar wajen domin hutawa kawai da ado na musamman, wanda a kallo ɗaya zaka fahimci tsarawa akayi dan wani dalili. Hannu ya saka ya kwance handkerchief ɗin daya ɗaura mata. glasses ɗinta daya cire ya ɗora mata duk da kuwa tana gani abunta ko babu shi, sai dai ba yanda ya kamata ba. Baki ta saki kawai tana bin wajen da kallo, kafin ta sami damar tambayarsa irin flowers ɗin ɗazun suka shiga zubo musu a jiki ita da shi, sai dai ƙamshin waɗanan daban suma. Atare suka lumshe idanunsa fulawoyin na cigaba da sauka musu. A bazata Nu'aymah taji tafi. Saurin waigawa tayi dan tafin yayi dai-dai da daina zubowar flowers ɗin a kansu.
Gaba ɗaya Doctors ɗin da sukai mata aiki ne. sai ƙarin mutum huɗu da bata saniba. Biyu mata biyu maza. Sai Solomon da Richard da batasan sanda ya dawo ba. Sai mutum biyu data taɓa gani a wajen dinner ɗinsu wanda take ƙyautata zaton abokansane ko ƴan uwansa ma.
A taƙaice dai ƴar ƙwarƙwaryar liyafa ce su Rich suka shiryama Aymah da Yoohan na murnar samun lafiyarta da nasarar aiki. Sai dai basu samu damar zuwa Austria ɗin su duka ba. Sai Richard daya dawo, sai kuma Osin da Joseph. Ɗakin ma sune suka kama musu a hotel ɗin wai suyi Honeymoon na sati biyu Nu'aymah ta huta kafin su koma tunda hutu Yoohan ya ɗauka harna watanni biyu.
Gaba ɗayansu su goma sha biyu ne har Aymah da Yoohan. Hakan yasa komai ya gudana cike da birgewa da nutsuwa. Sunsha shagalinsu na awa ɗaya da rabi sannan aka tashi. Su Richard dai tun anan sukaima Nu'aymah sallama. Dan da safe zasu wuce ba lallai ta gansu ba.
Godiya itama ta musu, ta shigo tabar Yoohan na ƙarasa magana da su. Bayan su Dr Liam sun wuce, Osin ya shige masaukinsu wai zaiyi toilet🤧. Solomon ma dai tafiya yayi can nasa masaukin inda suka fara zama da Yoohan. Hakan ya bama Yoohan da Richard damar kasancewa su kaɗai. Maganace a bakin Rich sosai gameda firar papa da Dr Mateo da yaji, sai dai baisan ta yadda zai tunkari Yoohan ɗinba kai tsaye tunda Papa mahaifinsa ne.
Ajiyar zuciya Yoohan dake ɗan nazarinsa yayi, “Rich kamar akwai magana a bakin nan naka tun kafin ka wuce kwanaki. Sai dai bansan miyasa ka gaza yiba. Duk da nasan dai bazai wuce akan komawata musulmi ba. Na yarda da kai Rich, dan baka taɓa cimin amana ba a tsahon shekaru goma sha shida da mukasan juna. Dan haka zan faɗa maka sirrin komawata mai salla a yanzu koda kuwa bazaka fahimceni ba”.
Batare da ya jira amsar Richard ba ya shiga bashi labarin tun farkon haɗuwarsu da su Nu'aymah a ƙofar Orphanage. Fasa masa glass ɗin mota da tayi da tilasta musu shiga cikin Orphanage akan yaron da suka bige. Fara mu'amularsa da su baba malam har zuwa musulintarsa da aurensa da ita. Babu abinda Yoohan ya ɓoyema Rich. Sosai tsantsar mamaki da firgici ya bayyana ga Richard. Wani irin rauni da ƙwaɗayin shiga musulinci ya ringa kutse cikin ɓargon jikinsa da zuciya. Sai dai baice komaiba akan hakan sai magana akan ƙullin da akaima Aymah na maganar ciki.
Ya janye hannunsa da ga dafe kan da yayi yana duban Yoohan da ke kallon wani waje da ban. “Ka yafemin Yoohan”.
Juyowa Yoohan yayi yana dubansa. Cikin ɗan lumshe idanu yace, “Akan mi? Ni bakamin laifin komaiba ai”.
“Niko na maka laifi X-man. Dan na zargeka akan abinda ba haka yake ba. Sannan na zargi in-lows ɗinka suma. Da ga yau na maka alƙawarin tayaka wannan yaƙin, zan taimakeka wajen cikama iyayenta alƙawarin daka ɗauka na bayyanar gaskiyar maganar cikin da suke zargin ta zubar”.
Kallonsa Yoohan yake cike da so da ƙauna. Ya riƙo hannun Rich cikin nasa yana faɗin, “Nagode sosai Rich, kai ɗin na dabanne a gareni koda bakina bai furtaba”.
“Ba nine na daban a garekaba Yoohan, kai ne na daban a gareni. Dan kamin abubuwa da yawa da ni kaina bansan hanyar da zan iya saka maka ba. Indai ni ɗin ɗan halak ne dolene na kasance a cikin yaƙin nan daka ɗauki alƙawarin yi. Sai dai zan baka shawara ɗaya zuwa biyu”.
Numfashi Yoohan ya furzar da lumshe idanu ya buɗe akan Rich. “Ina jinka”.
“Ka ajiye maganar ƙanƙantar matarka ka fara nuna mata ɗunbin soyayyar da kake mata. Waddama bata kaita shekaruba tana ɗaukar namiji balle ita dana fahimci tanada wayo sosai. Kaifa likitane, kasan sirrin mace duk da kuwa karatun likitancinka ba'a kansu kayisa ba. Amma na sanka da bincike, ta wannan hanyarne kawai kaima kanka zaka fahimci gaskiya ko akasin abinda Doctors ɗin suka faɗa a wancan karon, tare da naka gwajin, sai ka bita a sannu yanda kake buƙata.........”
“Amma Rich.......”
“Karkace komai Mr X. Wai shin kai baka tunanin shekarunka ƙaruwa suke ba raguwa ba? Ya kamata kasan sirrin dake cikin wannan tafiyar. Ko dai baka da lafiya ne Yoohan?”.
Harararsa Yoohan ɗin yayi kawai ya kauda kansa. Rich ya kwashe da dariya yana faɗin, “Kai ɗinne kana abu kamar dutsi oga. Ga dama ka samu a hannu amma kana son kasa damawa. Idan da kace kana ƙyanƙyami da gudun matan waje wannan dai matarkace ai ko.......”
“To naji mai shegen surutun tsiya. Muje shawara ta gaba”. Yoohan ya faɗa yana talle ƙeyar Rich.
Shafa ƙeyar Rich yayi da faɗin, “Mugu, ashe dai kanaso. Shawara ta ta biyu itace karku koma Nigeria da ita yanzu har sai na binciko maka duk yanda komai ya kasance”.
“Taya zaka binciko abinda baka saniba. Sannan wannan abun nasu yayi kama dana family, kai da ma ko sakin jiki ka kasayi da Uncle ɗin kanata faman jin haushinsa”.
Murmushi Rich dake kallonsa ya keyi, a ransa kuwa yanason hana Yoohan komawa Nigeria da Aymah ne saboda abinda ya jiyo a wajen papa a wannan komawar da yayi gida. Saboda hirar papa da Dr Mateo ta kasa barin ransa tun wancan karon. A wannan zuwan koda suka koma dasu baba malam a abuja ya sauka shi. Anan ya ɗanbi diddigin papa shine ya sakejin kwangilar kashe Aymah da ya bada ayi masa saboda wai ya ganta a cctv ta shigar masa ɗaki. Duk da basusan mitayiba a ciki saboda cctv ɗin iyakarta parlornsa ne, (Tab, kenan randa Aymah taje ɗakin papa. Ya salam🤦🏻♀️) Abinda yasa suka gaza gane mitayi su basuga komai a hannuntaba. To amma shi papa ya tabbatar ta ga sirrinsa shiyyasa yake buƙatar a kauda masa ita kafin bakinta ya faɗama wani. duk da yana zargin ta faɗama baba malam, yaso kuma ƙyaleta yabi a hankali harya gano abinda tayo a ranar amma su Uncle Mike sukaita tunzurashi aka ya kasheta kawai, shine ya bama Dr Mateo kwangilar kasheta a wajen aiki batare da an zargesaba, dan Yoohan ya sanar masa a inda za'ai aikin da masu tayasa. shine aikin ya gagara kuma.
Wannan abu da Richard yajine ya sakashi zaunar dasu G-boy akan su haɗa kuɗi su saka Yoohan zaman Honeymoon a Austria. Sai dai su basu san dalilinsa nayin hakanba dan bai fito fili ya faɗa musu ba........
Taɓashin da Yoohan yayine ya sakashi dawowa hayyacinsa. Ya sauke numfashi, cikin son kauda tambayar mi yake tunani da Yoohan yay masa yace, “Yoohan ka bani dama. Zanyi bincike nane iyakar likitocin da suka gwadata. Sai kuma ƴar aikin da kace an kawo muku tunda kace ka saka mata abin ɗaukar magana a ɗakin da kuka ajiyeta”.
“Okay Rich, sai dai banason ka saka kanka a haɗari Please”.
“Karka damu kamin addu'a kawai. Kuma ai tare zamuyi aikin ma da kai”.
Murmushi Yoohan ɗin yay masa suka rungume juna cike da so da ƙauna. Daga haka Rich ya korashi wai yaje madam na jiransa shima zaije yay video call da tashi dan gobe ma wajenta ya nufa, tare zasu wuce 9ja daga can..........✍🏻
Leave a Comment