Saran Boye 59
No. 59
..............Sosai yanzu ta nutsu ta ƙarema lungu da saƙo na ɗakin kallo, dan an kashe waɗancan fitulun ansa ainahin fitilu da suka ƙarama ƙawata ɗakin. Lallai duniya budurwar wawa. Idan bakayi wasa ba irin waɗanan abubuwan tuni suke shagaltar da kai ma ga bautar ALLAH.
Shiyyasa wasu mutanenmu dasun samu irin wannan damar sai kaga addininma an fara walagigi da shi. Zama tayi tana jiran shigowarsa dan taji wai yayama za'ayi? taga ɗaki daya ne. Nashi ne nan ko nata?. Dan kuwa dai ba yarda zatai su zauna a ɗaki ɗaya ba ehe.Tayi kusan zaman mintuna goma sha biyar sannan ya shigo ɗauke da ƙyaututtukan dasu Dr Sophia Suka bata. Yi tai kamar batasan ya shigoba. Shima kallo ɗaya yay mata ya ɗauke kansa. Sai da ya ajiye kayan hannun nasa sannan ya nufo inda take. Zama yay a kujerar dake kallon tata ya zaro wayarsa dake ring ya sa a kunne fuska ɗauke da murmushi. Sun kwashe tsahon mintuna a haka yana waya tana satar kallonsa harya kammala.
Kallonta yay ta kauda fuskarta gefe. ‘Yarinyar nan rigimanta yawane dasu' ya ayyana a ransa yana lumshe idanu da buɗewa a kanta. Ganin bazatayi manar daya fahimci takeson yiba sai ya mike ya shiga toilet ɗin ɗakin bayan ya ciri kayan barci a cikin kayansa da Solomon ya kawo ya ajiye rigar a saman gado ya ɗauki wandon kawai.
Duk da Aymah najin sanda ya shiga bayin ta kasa ɗagowa. Haka ta cigaba da zama zuciyarta na tattaro mata abubuwa masu ɗunbin yawa a kansa, ga ɗokin son komawa gida da takeyi, dan wulaƙanci yau ma gaba ɗaya bai kira mata Baba malam ba kamar yanda ya saba.
Duk daɗewar da yay a bayin a yanda ya barta haka yazo ya isketa. Da alama ma dai barci ta fara. Gaban kujerar ya matsa yana mai tsane sumar kansa ta gefe-gefe dan ba jiƙata yayi ba. Leƙa fuskarta yayi, hakan yasa ruwan da bai gama tsanewa ba a jikinsa ya ɗisar mata a gefen fuska.
Motsawa tai tare da buɗe idonta dan da gaske barci ta fara. Suna haɗa ido tai saurin jan gyalen jallabiyarta ta rufe fuska. “Oh God! Dama babyn nan mai bakin tsiwa tanada kunya ashe?. Tom tashi kije kiyi wanka”.
Bata iya ta motsa ɗin ba sai da taji motsin barinsa wajen. Ta gabanta ya zagayo inda Wadrobe ɗin ɗakin take. Tabi bayansa dake raɓar ruwan wanka da kallo, dan dogon wandone kawai a jikinsa babu riga, sai towel ɗin dake a hannunsa ƙarami. harya buɗe Wadrobe ɗin da akwatin kayansa ke a ciki, harma da nata kayan a haɗe da batasan da zamansu ba idonta a kansa. Ajiyar zuciya taɗan sauke da mikewa ta nufi bayin dan tana buƙatar yin wankan da ruwa mai ɗumi ko zataji daɗin jikinta, taga alamar kuma guy ɗin nan ba kunyace da shi ba. Kaɗanma daga aikinsa yace a gabanta zai Shirya. Bara tai wankan sannan tazo taji yanda zasuyi akan zaman ɗaki.
Lallai indai da ranka kallo baya ƙare maka ba. Dan toilet ɗin kansa ma wata aljannar duniyace. Tsabar ɗaurema ƙarya ƙugu harda television a ciki. Baki ta taɓe tana faɗin, ‘Kunga aljanu ai sun samu nayi. Kayi tsirara ga tv ana nunawa ai al-amari sai wanda kuma ido ya gani’. Da wannan mitar ta shiga wajen wankan na glass shima dake a mulmule. Wankanta tayi, sai da ta gama ne kuma tunanin kaya yazo mata a rai. Kanta ta dafe cike da damuwa tana faɗin ‘Oh Stupid me. Miya shiga kaina ne?’. Fitowa tai gaban ƙaton mirror ɗin da aka shirya towels a wani ɗan drawern glass shima. Fatanta ta samu bathrobe. Cikin sa'a kuwa tana ɗaga ta farko sai taga rigace. Ajiyar zuciya ta sauke ta warwareta ta saka. Tako wuce mata gwiwa, hakan ya sata jin daɗi ta ɗaure igiyar sannan ta naɗa ƙaramin towel a kanta dan duk ta jiƙa gaban goshin da ƙeyar. Kayanta data cire da nasa daya ajiye ta jefa cikin washing machine ɗin ta wanke. Ta sakasu wajen busarwa ma ta busar sannan ta ninke abunta ta fito dasu a hannu duk da harga ALLAH tanajin nauyin fitar saboda Yoohan. Amma da yake bawani jikinta bane a waje sai ta fuske akan zata ɗakko kaya ta dawo toilet ɗinne ta saka.
Zaune ta iskesa a bakin gado yana danna tab. Yana sanye da kayan barci farare ƙal. Baiji fitowarta ba saboda a hankali take tafiya da sanɗa, ita wayonta wai karya ganta. Sai ko akai rashin sa'a tana zuwa saitinsa ya ɗago ido ya kalleta. Cak ta tsaya tana cika baki da iska kamar zata fasa kuka. “Ni dai banason kallo”. Tai maganar da alama dai an ƙure mata gudu ne.
Idanunsa ya lumshe yana sake buɗesu a kanta. Baki ta kuma cunawa gaba ta juya masa baya.
A hankali yace, “Silly girl!”. Yana maida kansa ga tab ɗin.
Cike da munafurci Aymah taɗan karkato ta kallesa. ganin ya maida kansa ga tab taci gaba da tafiyarta kai tsaye yanzun. Bayansa taje ta tsaya ta ɗayan ɓangaren gadon. Kamar zatai kuka tace, “Banda kayan sakawa ni fa”.
Batare daya juyo ya kalleta ba yace, “Tom aro zan baki ne?”.
“Hu'um. Ƙato da kai tayaya kayanka zasumin. Kana kallon kanka kuwa a mirror? Sai kace ɗan dambe”.
‘Yarinyar nan ko’ ya faɗa cikin ransa yana juyowa ya kalleta. Saurin juya masa baya tayi dan itafa batason kallon. Shima ya fahimci kunya takeji, hakan ya sakashi yin murmushi. Wannan ɗabi'ar ta kunya tana abu na farko da yaren hausawa ke burgesa da shi. Ko abu ke damunsu sukazo gabansa matsayin likita sunta ƙunshe-ƙunshe kenan.
Miƙewa yay ya zagayo inda take. Ganinsa kawai tayi a gabanta. Hakkanne ya sakata zabura tai baya kamar wanda tai gamo da abun tsoro. Tai saurin sake juya masa baya a daburce.
Hannayensa duka biyu ya tura cikin aljihun wandon kayan barcinsa yana faɗin, “Uhyim! Tom nama fasa bada aron kayan. Garama ki lallaɓani fa, koki kwana da bathrobe. idan kuma kinaso juyo ki kalleni”.
Ji Nu'aymah tai kamar ta fasa ihu dan takaici, gashi harga ALLAH tana buƙatar aron kayan kuma da gaske. Dan bazata iya kwana da rigar wanka ba. Juyowa tayi a hankali idanunta a ƙasa ta kasa kallonsa. Yanda ta koma kamar wata munafuka ne ya bashi dariya. amma sai ya gimtse kayarsa baiyiba. Takowa yay gabanta ya tsaya gab. Yasa hannu a karɓi kayansu dake a hannunta tare da ɗora na damar a haɓarta ya ɗago fuskarta. Tsaf ta runtse idanunta kuwa. Baiyi magana ba, sai kallonta kawai da ya keyi musamman bakinta da arayuwa yake bala'i-bala'in ɗaukar masa hankali. Kodan shine yafi masa tsiwa oho. “Je gasu can a Wadrobe ki ɗauka badan halinkiba dai”.
Batare data buɗe idanunba ta motsa laɓɓanta kaɗan tace, “Thanks you”.
Sakar mata fuska yayi ya matsa. Da sauri tabar wajen dan gaba ɗaya idan ya tsaya kusa da ita koya zauna jinta take a matuƙar takure, duk sai yay mata kwarjini. Tana buɗe akwatinsa dake a Wadrobe ɗin yana isowa wajen. A bayanta ya tsaya gab tare da zura hannunsa duk biyu ya ɗora akan nata dake ɗaga murfin trolly ɗin data buɗe. Jitai numfashinta na fita da ƙyar lokacin da ƙirjinsa ya mannu da bayanta duk da akwai kaya a jikin nasu. Taɗan rintse ido zuciyarta na harbawa. Kansa ya ɗora gefen kafaɗarta ya ajiye kayansu daya amsa a wajenta yana magana a hankali. “Ashe kin iya wanki?”. Kasa bashi amsa tayi, dan harga ALLAH ta matuƙar takuruwa. Shima fahimtar hakan da yayine sanadin numfashinta da yaji yana seizing ya sakashi sakar mata kiss a wuya yaja baya. Kaɗan ya hana fitsari zuboma Aymah. Ta sauke ajiyar zuciya da ƙyar sannan ta buɗe idanunta dake tara ƙwalla. Ɗaga kayan ta farayi ko zataga wanda zai ɗan mata, sai taga kayanta har kala huɗu ashema a ciki. juyowa tai taɗan kallesa da masa ƙaramar harara. Baisan tanayi ba, dan ya juya mata baya ne zai zauna a inda ya taso a bakin gado. Ƙunƙuni taitayi tana ciro kayan. Gaba ɗayansu ma kala huɗu ne. Na barci biyu, dogayen riguna biyu, sauran duk nasane suma dai basufi guda biyar ba, Sai kayan ciki datai fatan ALLAH dai yasa bashine da kansa ya ɗakko mata su ba. Dan wlhy daya gama da rayuwarta kam. Ɗaukar waɗanda zata saka tayi ta maida sauran. Ta haɗo harda wayarta data gani a ciki da Charger. Ta gabansa tazo ta wuce bayi, acan ta canjo kayan ta yafo mayafin jallabiyar data wanke dan dashi ta koma. Kayan bama wani kamata sukayiba, kuma basu fidda mata jikiba. Sai dai wandon iyakarsa gwiwar ta. Sannan hannun rigarma bawani babba bane can sosai. Amma bai mata yanda zataji kunya ba. A kwance ta samesa yanzun, idanunsa a lumshe suke amma batasan duk yana kallonta ba. Wajen Wadrobe ɗin ta koma, ta ɗauki turarensa data gani har biyu saman akwatin ta hau fesawa. Daga haka ta dawo wajen gadon tana kallonsa fuska a tsuke.
“Wai bazaka tafi ɗakinka ba ne?”. Tai maganar a hankali kamar maijin tsoro. Sarai ya jita, amma sai yay shiru abunsa kamar yayi barci. Idanuntane suka cika da ƙwalla. Dan gaskiya ita dai bazata iya kwana da shi a ɗaki ɗaya ba. Ta ɗan ɗaga murya fiye da ɗazun tace, “Kaji! Dan ALLAH kaje ɗakinka. Kokuma ni naje can sai na kwana”.
Idanunsa ya buɗe a kanta. Yace, “Ohooo! Silly girl. Nan gidanki ne ma ashe ko? Dahar sai kin zaɓi ɗakin barci?”.
“To amma ai kasan mu biyu ne sai ka kama ɗaki biyu”. Tai maganar da iya gaskiyarta. Fahimtar da yay yarintar tatace ta motsa ya sakashi gyara kwanciyarsa yana faɗin, “Wasa nake miki ga key ɗin ɗakinki anan zoki ɗauka”. Ya nuna mata bedside ɗin. Da iya yarda ta nufo wajen kuwa ita zata ɗauki key. Tana ɗora hannunta saman handle ɗin drawer ɗin kuwa ya riƙesa caraf.
Bata ankaraba sai jinta tai a jikinsa ya fisgota ta faɗo. Duk da yaji zafi bai damuba, sai ma juyi da yay da ita suka koma tsakkiyar gadon sosai. Mutsu-mutsu take nason ƙwacewa ya matseta da ƙyau. Ga bakin ya kasa magana. Bargo ya jawo da hannu ɗaya ya lulluɓesu, kafin ya kai hannu ga makunnar fitulin ɗakin duk ya kashe na barci suka kawo da kansu.
Cikin kunneta yace, “Silly girl, ai kecema kike kama da ƴan damben. Garama ki nutsu muyi barci dan zaki gajiyar da kankine. A wancan karonma dana ƙyaleki akwai dalili. Yanzu kam ki fiddama ranki zamu cigaba da raba wajen kwanciya yarinya”.
“Ni dai gaskiya bazan iya kwanciya da Namiji a ɗaki ɗaya ba”. Tai maganar tana kuka.
Cikin kwaikwayon maganarta yace, “Nima gaskiya bazan iya kwanciya da mace ɗaki ɗaya ba”.
Ɗagowa Aymah tayi tana kallonsa fuska shaɓe-shaɓe da hawaye. Ya ɗaga mata gira da kansa yana faɗin, “Kin zata kece kaɗai kika iya drama ɗin? Nima actor ne a film ɗin ai Trouble maker”.
“Kaima Trouble maker ɗinne ai, Kuma sai na faɗaka da Abbana”.
“Nima sai in faɗaki da Papa na. Kinga saisu haɗu su mana faɗa muyi-muyi mu kawo musu jikokinsu, dan ni nama ƙagara na ganki da ciki”.
Da sauri Aymah ta maida kanta a ƙirjinsa saboda kunya. Ta dunƙule hannunta dake a bayansa tai masa ƙaramin dundu.
Dariyar da bata taɓa ganin yayiba taji ya sanya mata yana riƙo hannun nata. Da ɗayan ta ƙara dukansa a ƙirji itama tana dariyar kaɗan-kaɗan. Matseta yayi gaba ɗayanta a cikin jikinsa yana ɗora haɓarsa bisa gashin kanta da hular ta zame duk ya mimmiƙe. Sumbatar kan yayi yana lumshe idanu har sannan da murmushi a fuskar tasa.
“Yanzu fa idan nace zan rama sai ki kamamin raki ko? Kuma naji zafin dukanmin baya da kikayi”.
Da sauri tai ƙoƙarin ja da baya yay azamar riƙota cikin jikinsa yana mata magana a hankali. “Matsoraciya kawai, wasa nakeyi. Tashi kisha maganinki sai ki kwanta”.
Itama luf tayi tana shaƙar ƙamshinsa, kusan mintuna biyu suna a haka kafin ya saketa dan yanayinsa neman fara sauyawa yakeyi. Jin ya saketa ta tashi zaune. Shima kunna fitilar ɗakin ya sakeyi ya tashi da kansa ya ɗakko mata maganin da ruwa ya kawo mata. Amsa tai tasha tana ɗan matse ido. Ta miƙa masa sauran ruwan batare data bari sun haɗa ido ba. Shima baice mata komaiba ya amsa ya juya. Da wannan damar ta tattaro filos ɗin gadon ta hau jerawa a tsakkiyarsu tana faɗin, “Kowa ya kwanta sashensa to gaskiya”.
“Ai garama haka, ni karkimata ball da ni da waɗanan ƙafafun naki da basa zama waje ɗaya”. Yanda yay maganar yana kwanciya da juya mata baya kamar bashine yayiba ya sakata gallama bayan nasa harara. Itama bata tankaba ta kwanta ta juya masa bayan. Murmushi yayi dan yasan abin cewarne ya ƙare mata shiyyasa tayi shiru. Ba'afi mintuna biyar ba sai jin saukar numfashinta ya farayi a hankali alamar maganar ya fara aikinta har tayi barci. Juyowa yay a hankali yana kallon bayanta, musamman sumar kanta dake kwance luf a ƙeyarta har zuwa dokin wuya da ƙananu sukaima wajen ado mai ƙayatarwa bisa farar fatarta mai sheƙi da bawai ƙal-ƙal takeba irin ta turawa. Dan shi kansa ma ya ɗan ɗarata haske duk da farin fatar tasu ba iri ɗaya baneba sam.
Hannu ya kai a hankali yana ciccire filos ɗin data jera musu a tsakkiya, sai da ya ciresu duka sannan ya matsa sosai jikinta ya sakata a nasa jikin yaja musu bargo. Ajiyar zuciya ya shiga saukewa a hankali, a ransa yana raya ‘Sarkin rikici’ tare da tura hannunsa cikin rigarta ya shafa cikinta dake lafe a jikinta kamar babu hanji a ciki. Lumshe nasa idanun yayi shima yana karanto musu addu'ar barci da ayanzu Alhmdllh ya haddace duka..
_________★★
Alarm ɗin daya saka musu ne ya tadasu sallar asuba. Shine ya fara farkawa, sai da yayo alwala sannan yazo ya tada Nu'aymah da ƙyar. Ganin yanda take haɗa hanya alamar barcin bai saketa ba ya sakashi taimaka mata har ƙofar toilet ɗin. Bayan ta shiga ya canja kayan barcinsa zuwa jallabiya yasa abin salla ya kabbara raka'a-tainul fajir kafin ta fito.
Itama koda ta fito doguwar riga ta cira a kayanta ta saka. sannan ta hau sallayan daya saka mata a bayansa tai tata nafilan raka'a biyu. suna zaune kowa na lazimi har lokacin sallan ya ƙarasa. itace ta bashi shawaran yay musu jam'i. Da farko ya nuna mata shi ina iliminsa ya kai da har zai musu jan salla. Ta masa taƙaitaccen bayanin da zai iya fahimtarta kafin ya jasu sallar asubahi.
A mamakin Nu'aymah sai gani tai ya ɗakko Al-qur'ani ya dawo gabanta ya zauna. Kallonsa take kamar yanda shima nasa idanun ke a kanta.
“Daga yanzu matata ce zata zama malamata kamar yanda Uncle ya bani shawara (baba malam)”. Sosai Aymah ta waro idanu waje, da faɗin, “Ni kuma Yaya Yoohan?”.
“Insha ALLAH kuwa. Dan duk abinda zanje nema a wajen wani malami na tabbata kinada kaso hamsin a cikinsa insha ALLAH. Karkiyi min wasa da damata Please Zeeynab, dan na yarda tun a farko UBANGIJI ya sakoki rayuwatane dan ki zamarmin fitila mai haska min hanya. So ni koda shekarunki basu kai hakaba zan zauna a gabanki na koyi abinda ban saniba. Cire duk wani kokwanto da shiriritanki nan wannan ba gaɓar wasa bane. Akwai manyan ƙalubale a gabana da dole sai da wannan ilimin zan tunkaresu”.
Kan Aymah a ƙasa tana wasa da yatsun hannunta ta jinjina masa kan. Cikin nutsatstsiyar murya tace, “Insha ALLAH zaka sameni yanda kake buƙata. Sai dai ka sani har yanzu ni ɗalibar ilimice, nima banje ko inaba a neman ilimin. Ko a gidanmu ƙaramin ajin yara nake koyarwa bawai manya ba”.
“Bani da banbanci da waɗannan yaran nima ai Nu'aymah, domin abinda kike koya musu nima shi nake buƙata a yanzu ki koyar dani. Dukkan littatafan da zamu iya buƙata gasu Uncle yazo mani dasu. dan dama muna karatu da shi ta video call a kullum bayan sallar la'ar a duk inda nake. Da wannan ne na ɗan samu abin salla da addu'oin da kikeji a bakina”.
Sosai tausayinsa ya kama Aymah har idanunta suka cika da ƙwalla. Ya kuma birgeta matuƙa, dan ɗaukakarsa da girmarta da yayi, da matsayinsa na miji a gareta bata sakashi girman kai ba........
“Please ki ceto rayuwata Zeeynab ”. Furicinsa ya katse mata tunani. Saurin ɗora hannunta tayi akan bakinsa saboda jin yanda yay maganar da rauni. Ta shiga girgiza masa kanta ƙwalla na sake taruwa mata a ido. “Ka daina roƙona, umarni kawai zaka bani a matsayinka na babba gareni kuma mij......”
Sai kuma tai shiru ta kasa karasawa. Murmushi yayi da ɗaga mata gira. janye hannunta tai daga kan bakinsa ta hararesa. Yay karamar dariya da faɗin, “Hy karasa mana. Wai dama kinada kunya ashe?”.
Harara ta kuma zuba masa tana kumbura baki, tace, “Silly boy”.
A tare suka fashe da dariya babu zato, dan ita kanta kalmar Silly boy ɗin datai saurin kiransa da shi kafin shi ya kirata ta bata dariya.. Sai da sukayi mai isarsu sannan suka nutsu. Ya gyara zamansa yana faɗin, “Silly girl kin rainani wlhy”. Batace komaiba sai murmushi.
Shima dai murmushi ne ɗauke a fuskarsa. Ya kara gyara zamansa. “Gashi Al-qur'anin ɗaya ne yaya zamuyi kenan?”.
Murmushi ta kumayi mai kayatarwa tana lumshe idanu. Batare data kallesa ba tace, “Karka damu, ko babu Al-Qur'ani a hannuna zan iya ai”.
“Woow masha ALLAH” ya faɗa yanajin wata ƙaunarta da girmanta a cikin zuciyarsa da bargo. Daga haka suka nutsu ya fara karanto mata iya inda ya tsaya da harshensa da baya fita sosai. Hakan yasa karatun nasa yay mata daɗi. Sai da ya tsaya ta dubesa da kulawa. “Zamu cigaba da yin Al-qur'ani. Amma ina ganin ya kamata ka fara koyan larabci hakan na taimakama mai karatun Al-qur'ani sosai wajen furta abinda ake buƙata”.
Idanu ya lumshe a hankali ya buɗe a kanta. cikin muryarnan tasa mai amo yace, “Okay maa. Duk yanda kikace haka za'ayi”. Duk da ya bata dariya batayi ba, sai dai ta murmusa kawai. Cikin baiwar da ALLAH ya azurtata da ita na wadatuwa da ilimin addini ta fara ɗorama Yoohan karatun. Ba ƙaramin nutsuwa da shagala yayi a kallonta ba. Dan yaune karan farko da yaji yanda take raira karatun Al-qur'ani mai girma a fili. Wata irin nutsuwace ta ringa saukar masa. har ƙananun ƙwalla suka taru masa a cikin ido bai saniba. Sai da suka sakko a fatar idonsa kaɗan idanunsa sukai masa gizo sannan ya lura. Ɗan yatsa yasa ya ɗaukesu yana cigaba da saurarenta.
Tabbas Yoohan ya saka a ransa zai nema ilimin addini babu wasa a ciki. Hakanne yasa UBANGIJI riko da hannunsa. Gashi kuma ya bashi Aymah a kusa da shi da har cikin ransa ya yarda itace zata zame masa malama kuma sirrin rayuwarsa. Dan haka basu tashiba a wajen sai da ta tabbatat ya fahimci abinda ta koyar da shi.
Bayan sun kammala abinci mara nauyi yaymata, order dan taci tasha magani kar lokaci ya wuce. Tunda shan maganin nata akwai ƙa'ida. Hatta da barcinta yanzu yanada lokacin yi da tashi har sai komai ya ƙarasa dai-daita yanda ya kamata. Tea kawai ta iya sha da cake kaɗan, dan ita dai wannan abinci na Austrian baya mata daɗi. Wanima ƙyanƙyami yake bata. Musamman da harshenta har yanzu ba komai yake masa ɗanɗano ba. A hakama cake ɗin sai da Yoohan ya tayata ci sannan. Tana kammalawa ya bata magani tasha ta shiga wanka. Shi kuma fita yay dan motsa jiki a gym ɗin hotel ɗin. Da kuma son ƙarasa magana da Rich.
Aymah na fitowa kaya kawai ta canja sai kwanciya. Ko mintuna biyar bata rufaba kuwa barci yay gaba da ita.............✍
Leave a Comment