Saran Boye 67


 No. 67


............Juliet taso kiran Yoohan ta sanar masa amma Aymah ta hana. A cewarta ta barsa wai dama ta saba irin wannan zazzaɓin duk shekara. Asibiti ma taƙi yarda suje sai magani data amsa tasha. Daga haka ta fara ɗan ƙarfafa kanta duk dan ta kwantarma Juliet ɗin da hankali ganin ta damu. Gashi itama fama take da kanta dan cikine da ita ɗan wata kusan takwas.

      Dole Juliet ta barta, sai dai duk motsinta na akan idonta. Ita har mamakin yanda Nu'aymah ke bankar coffee takeyi babuji babu gani. Gason yawan kwanciya bisa tiles wai sanyin take so. 

        A hankali tama daina cin abinci, dan kotaci sai tayi amansa take samun sauƙi. Hakan na damunta, sai dai ta kasa faɗama ko Juliet ɗin balle Umm da Hajjo da Addah da kusan kulumm sai sunyi waya. Ko sun kirata ko ita ta kirasu sai taita ƙarfafa kanta yanda babu mai ganewa. Sai dai Uwa dabance. Dan Umm kan tambayeta anya tana lafiya kuwa? Dan a muryarta da yanayin sanyin da tayi na rage surutu da rawar kai Umm takan ji kamar Aymah na cikin wani haline. Amma sai take cemata babu komai, kawai yanayin wajene.

     Juliet nada coffee powder a gida, sai dai kota haɗama Aymah bata sha sai dai suje shagwan shan coffee ta sha tayo guzirinsa kuma. A duk sanda sukai waya da Yoohan ko video call kam sai taita ƙarfafa kanta harda masa ƙarfin halin tsiwa wai karda ya fahimci halin da take ciki.

       Batasan kallonta kawai yakeba, dan tun kafin akai haka ya gama fahimtar shigar ɗan tayin cikinsa a mahaifarta. Sai dai ya barma ransa har ALLAH ya bayyana ikonsa da kansa tunda shima hasashene kawai da shegen ganin ƙwaf irin na likitanci bisa baiwar da UBANGIJIN al'arshi ya azurtasu da shi.


_________________


      Kwanan Yoohan huɗu a ƙasar Oman ya wuce Nigeria. A abuja ya sauka, sai dai maimakon ya tafi gida direct sai ya sauka a hotel ya kama ɗaki. Dan dama babu wanda yasan da zuwansa ƙasar a cikin su papa. Yama toshe duk wata hanyar da zasu iya samunsa a waya tun barinsu Austria. Ya fi son yazo su fuskanci juna akan maganar Solomon ɗin fiye da suyi magana ta waya.

        A daren ranar ya samu aka samo masa Number ɗan sandan nan da ƙyar ta hanyar wani abokinsa da shima ɗan sandan sirrine babba.

     Gajiyar daya kwaso ce ta sakashi yin barci da wuri ranar ko waya da Aymah baiyiba. To itama dai da yake ranar zazzaɓi ya mata rigif ko nemansa batayiba ma. 

      

      Washe gari ƙarfe goma na safe Omar (Rich) ya iso hotel ɗin daga birnin Lagos. Ya iske Yoohan ɗin cikin shirin suit royal blue da sukai masa masifar ƙyau. Musamman yanzu da yay wani ɗan ɓul-ɓul dashi saboda madarar angwanci data hudashi. Rungume juna sukai cike da so da ƙyauna da begen juna. Kai kace basa waya kullum. Bayan sun gama ƴar chapter ɗinsu da suka iya suka fito gwanin sha'awa zuwa motar Omar ɗin. Omar ne ya jasu zuwa headquarter ƴan sanda na jami'an tsaron sirri suna ƴar hirarsu.

      Sai da suka gama shan tambayoyi da uban bincike kafin su sami damar shiga da taimakon abokin Yoohan ɗin da aka sanarma zuwansu daga baya.

     Da ƴar dariya Dawood yake kallon Yoohan daya ciskule fuska saboda haushi binciken da akaita musu yana faɗin. “Yi haƙuri bokan turai, wlhy banyi tunanin zakuzo a yau bane da nazo na tsaya a gate ɗin na jira isowarku ai. Tunda aka ɗora mana adalin shigaba a hukumarnan tamu tsaro ya ƙara tsauri dan sam bashi da wasa”.

       Dariya shima Omar yayi yana taɓe baki. Yace, “Kai Dawood manta da lamarinsa kewar matarsa ke ɗawainiya da shi badan wannan binciken yake fushi ba”.

    Hararsu Yoohan yayi su duka amma baice komaiba. Da haka suka ƙarasa can sama inda office ɗin oga kwata-kwata na hukumar DSS yake. Duk da Dawood yay masa bayani akan zuwan su Yoohan ɗin sai da suka jira shi ya fara shiga office ɗin sannan ya fito yay musu iso.

      Ƙyaƙyƙyawan dattijo ne da a shekaru a ƙalla zai iya kaiwa 64 Zaune a kan kujerar office ɗin hankalinsa gaba ɗaya akan Computer ɗin dake saman desk ɗinsa. Batare da ya ɗago ba ya amsa musu sallamarsu cike da nutsatstsiyar muryarsa mai tarin kamala da dattako. 

       Sosai kwarjininsa ya cika zukatan su Yoohan duk da bai ɗago sunga fuskar tasa ba da ƙyau. Da hannu yaɗan nuna musu kujerun yana faɗin, “Bismillanku”.

     Kusan a tare Omar da Yoohan suka sauke ajiyar zuciya da duban Dawood dake ƙame a tsaye. Kai shima ya jinjina musu alamar su zauna ɗin. Zaman sukayi tare da haɗa baki wajen faɗin, “Good morning sir”.

        Cikin ɗan fesar da iska Boss *_Jawaad Abdul-aziz Yusif tafida_* ya ɗago gaba ɗayansa fuska babu walwala kamar ko yaushe yace, “Good Morning”. yay maganar da miƙa musu hannunsa alamun suyi musabuha.

      Omar ne ya fara miƙo masa hannun suka gaisa, kafin ya miƙama Yoohan da shima zuciyarsa ke wani bugawa da harbawa da sauri-sauri. sai dai cike da dauriya ya faɗaɗa fuskarsa da murmushin ƙarfin hali. 

      Da ga shi har Boss Jay zukatansu suka buga da ƙarfi. Hannun Yoohan ya dinga rawa dan yama kasa ƙarasawa da shi inda na Jay dake ƙoƙarin zare glass ɗin idonsa yake.

       Hakan yayi dai-dai da shigowar wata kamilalliyar mace da shekarunta zai kai kimanin 53 cikin office da sallama, hannun ta riƙe da takardu. Sanye take cikin doguwar rigar jallabiya baƙa. Shigar tata ta ƙara fidda kamalarta da mutuncinta ga mai kallonta.

       Akan mijin nata ta fara sauke idanunta da mamakin yanayin data gansa. Sai kuma ta maida dubanta ga abinda yakema kallon ruɗani da tsoro. Baya tayi da sauri har takardun hannunta na watsewa a ƙasa. Saurin sunkuyawa Dawood da ke binsu da kallon mamaki yayi yana tattare takardun da faɗin, “Am sorry maa”.

        Bilkisu bata iya cewa komaiba sai takawa da tai da sauri inda Jay yake. Zatai magana yay saurin damƙe hannunta alamar shi ya dawo cikin hankalinsa. Girgiza mata kai yayi alamar kartace komai. Sai ma wayancewa yayi da faɗin, “Wai nikam da gaske likitan da naso gani ruwa a jallo shekara ɗaya data shuɗe ne amma hakan ya gagareni a gabana?”.

       Duk da Yoohan yaji sam a ransa ba wannan batun bane jefa adalin ma'aikacin cikin ruɗanin ganisa sai shima ya sauke ajiyar zuciyar da sam bata samun nutsuwa bace. Cike da ladabi ya jinjina kansa yana murmushin ƙarfin hali. Dan wani masifar kwarjini da Jay ya masa. Yace, “I'm very sorry sir. Nasan ni mai laifine sosai a gareka”.

      “No no no son. Inama mutane irinka uziri sosai ni a rayuwa. Dan haka manta kawai da wancan batun, tuni an kauda matsalarma”. Jay ya faɗa yana maida glasess ɗinsa akan ido.

      Cike da jin daɗi Yoohan yace, “Thanks you Uncle”. Sai kuma ya ɗan kalli Bilkisu da alamu suka nuna har yanzu tana a cikin ruɗani ita dai yace,  “Good morning maa”.

         Da wani irin sanyi tace, “Good morning dear”. Shima Omar (Rich) da al'ajabi ya cika gaisheta yayi. Ta amsa masa da kulawa shima tana duban Jay da har yanzu idanunsa akan Yoohan suke. Kauda kansa yayi ya ɗan dubeta saboda taɓa masa kafaɗa da tayi. Murmushin ƙarfin hali yay mata da nunama su Yoohan ita faɗin, “My wife. Itace naso na kawo maka a wancan lokacin muka gagara samun dama. Itama ma'aikaciyace a wannan hukumar. Amma Alhmdllh, daga baya mun fahimci babu waccan matsalar da mukai zargi”.

       Cike da girmamawa Yoohan da Omar sukace masha ALLAH. ALLAH ya ƙara kiyaye gaba.

         Amin suka amsa musu. Bilkisu data fahimci zamanta a wajen zai iya kawo matsala sai tai ɗanyi murmushi da ranƙwafawa saitin kunnensa tai magana. “Bara naje, su Zuhrah na jirana zamu wuce. Ga takardun nan duka na haɗo maka na case ɗin matar nan mai safarar ƙwayoyi”.

      Kansa ya jinjina mata kawai yana murmushi. Yana son ɗan sumbatar matarsa babu dama. Dan haka ya kashe mata ido ɗaya cike da salon ƙwarewar manyan masoya😉😂.

      Itama murtani ta maida masa da nata salon taima su Yoohan sallama ta fice. Numfashi Jay ya furzar a ɓoye. sannan ya maida duka hankalinsa gasu Yoohan da kansu ke a ƙasa. Dan gaba ɗaya zuciyar Yoohan ta gaza samun nutsuwar zama a waje ɗaya. Yadai dage yanata ambaton sunayen ALLAH kozai samu sassauci daga abinda yakeji cikin jininsa.

         “Tom Doctors ina saurarenku. Dawood ya sanarmin kuna son ganina cike da magiya a garesa. Ina fatan dai lafiya ko?”.

       Omar yace, “A lafiya lau sir. Wani taimako mukazo nema ne a wajenka da alfarma akan wani case”.

       “Okay. Babu damuwa. Dawood zoka ɗauka dukkan bayanansu dan kar a samu kuskure ko”.

        Da tsantsar girmamawa Dawood yace. “Okay sir”. Yay maganar da ƙame jikinsa waje guda yana buga kafarsa ƙasa. Hannu Jay yaɗan miƙar alamar amsawa. Daga haka ya ciro takarda da pen ya zauna ya fara sauraren bayanin da Omar ya farayi kasancewar Yoohan ya sanar masa komai dangane da gidan su Aymah akan abinda yaji daga gareta da wanda ya sani.

        Sai da ya kai aya Jay ya sauke numfashi yana janye pen ɗin da yake gogawa saman laɓɓansa. Ya ɗan murmusa da faɗin, “Babbar magana. Ɗan jibiya family kam ba ɓoyayyan gida bane. dan ahaline na masu daraja saboda ilimin addini da harkokin kasuwancinsu. So dama akan samu irin waɗanan rikice-rikicen da ZAGON ƘASA a irin mafi yawan waɗan nan gidajen. Shi kuma zagon ƙasa Kamar wani SARAN ƁOYE ne mai cin rai da ruɗa tunanin wanda akemawa. So na tayaku murna tare da shigowarku cikin hasken musulinci. Na kumayi alƙawarin taimaka muku wajen ban kaɗo abinda kuke buƙata bisa son ƙyautatawarku ga Sheikh Soorajidden Hashim. Saboda nima malamina ne ai. Kuna ambata masa sunana zai baku labari. Har ɗaurin aurenku naje ma. tabbas kwanaki dana buƙaci zuwa wajensa muyi magana ya sanarmin zaiyi tafiya za'aima yarinyarsa aikin ƙwaƙwalwa a ƙasar ƙetare”.

     Da jindaɗi a fuskokinsu suke dubansa.

    Shima murmushi yayi yana zare glasess ɗinsa. ya cigaba da cewa, ”Ina ƙaunarsa sosai dan yayima rayuwata hidima mai yawa. Insha ALLAH nima bazan gajiya ba wajen bankaɗo azzalumai masu cin dunduniyarsa. Sai dai wannan aikin dolene ya kasance na sirri”. Yakai ƙarshen maganar da duban Dawood.

      “Dawood! Ina buƙatar ganin Bilkisu Jawaad”.

      Da sauri Dawood ya miƙe yana faɗin, “Okay sir”.

    

      Cikin mintuna ƙalilan sai ga Dawood ya dawo tare da matashiyar mace da bazata gaza shekaru talatin da biyu zuwa da uku ba. Daka ganta babu tambaya kasan jinin Boss Jawaad Abdul-aziz ce. Sanye take cikin wando da riga na Uniform ɗin hukumar. Da alama itama jami'ace a hukuma (dan ƙari. Bilkisu ƴar bilkisu jikar bilkisu kenan😉. Ita ƴar sanda, mamanrta ƴar sanda. Babanta ɗan sanda😝. Wani aiki sai Jay😂lol).

       Fuskarta cike da miskilancin data gada wajen iyayenta ta ƙame tare da salute ɗin mahaifinta kuma oganta a wajen aiki. tace, “Sir gani”.

      Daga Yoohan har Omar kallon mamaki suke mata. Dan basa buƙatar ƙarin bayanin komai game da Biljay.

       Takardar da Dawood ya rubuta ya miƙa mata cike da bada umarni a gareta matsayin oga ba mahaifiba. “Duba min wannan takardar”.

      “Okay sir” ta faɗa tana ɗaukar takardar. Cike da hazaƙar ƙwarewar aiki ta duba rubutun takardar tsaf, kafi. ta ɗago ta kallesa tana sunkuyar da kanta da ƙamewa. “Na duba Sir”.

       “Me kika fahimta?”.

“Report ne na case ɗin ɓoyayyun mutane masu laifi”.

       “Masha ALLAH. Little bee kece zakiyi wannan aikin. Waɗanan sune masu kawo Report ɗin. Zakiyi joining ɗinsu kuyi aikin tare. Sai dai kece zakiyi kutse a cikin gidan ko mubi ta wata hanyar insha ALLAH. Kinsan banson wasa, bana son kuskuren ganganci akan aiki, so be careful”.

      “Insha ALLAH sir”.

Kai ya jinjina mata da maida dubansa kan Dawood. “Dawood tare zakuyi wannan aiki da ita, so zata kasance ƙarƙashin control ɗinka, dukanku kuma zaku kasance akan umarni”.

     Shima ya amsa da “Okay sir”.

Daga haka Jay ya maida dubansa gasu Yoohan. “Doctors waɗanan nan sune zasu taimaka muku akan wannan case. Insha ALLAH daga nan zuwa kwana uku zamu san wadda zata shiga cikin gidan matsayin maiyin hutu a wajen Sheikh. Sauran aiki duk zasu yisa baku da damuwa. Sai dai dole kuma sai da hannunku a ciki dan kun fisu sanin sirrin gidan a yanzun. Zaka haɗata ƙawance da matarka ta waya. Dan wasu abubuwan ta hanyartane zasu sami haske sosai. Duk abinda ya dace zaku cigaba da ji ta hanyar Dawood, dan shine oganta”.

      Godiya sosai su Yoohan suka shiga yimasa. Dan sam basuyi tunanin samun mafita cikin sauƙiba haka daga garesa oga kwatakwata da ganinsama ke da matuƙar wahala. Yanda bai musu bayani akan matsayin Bilkisu a garesaba suma basu tambayaba duk da sunada buƙatar ji. 

      A tare da shi suka fito office zuwa massalaci saboda kiran sallar zuhur. Bayan an idar da salla kuma sukai masa sallama da ƙarin godiya suka wuce cike da farin cikin wannan karamci da samun sauƙi. Sai dai ƙasan ran Yoohan shi kaɗai yasan mi yakeji game da Jay ɗin.

    Koda suka ɗauki hanya kasa haƙuri Omar yayi sai da yayima Yoohan maganar kallon da yaga Jay ɗin na masa da matarsa. Harma hanata maganar da yayi. Tare da cewa nifa, “Wlhy fisgen kamannima kukaimin”.

        Da mamaki Yoohan yace, “Kamanni kuma?”.

      “Yes X-man. Wlhy a fisge kunyi kamanni like na jini haka”.

      Nannauyan numfashi kawai Yoohan yaja da ƙarfi ya fesar batare da ya iya cewa komaiba har suka ƙarasa wani gidan cin abinci. Anan sukai lunch da cigaba da tattaunawa akan abinda ya shafesu. Daga haka sukawuce General hospital wajen Dr Shikurah. Sai dai sunyi rashin sa'ar samunta wai batama ƙasar.

     Yoohan yayi gaisuwa da abokan arziƙi suka koma hotel ɗin daya sauka. Omar ya jima a wajensa dan har dare suna a tare sannan ya koma gidan papa dan acan ya sauka shi. Amma sai bai faɗama kowa Yoohan na ƙasarba.

      Washe gari Yoohan yaje kaduna yin wani aiki. Sai washe garin daya cika kwana uku a 9ja ya dawo. Dai-dai da ranar da Little bee zata shiga gidan baba malam kenan. Dan haka kai tsaye gidansu ya nufa. Sai dai kawai su Madam Chioma suka gansa tsilum tamkar daren Christmas inji su.


___________★★


          Tun wucewar su Yoohan Jay ya kasa zaune ya kasa tsaye a office ɗinsa. Gaba ɗaya man kan sa ya gama tsiyayewa tas akan wannan kamanni. Goshinsa ya murza da cewa, ‘Kai anya kuwa. Dolene nasan wanene wannan yaron’. Ya ƙare maganar da ɗaukar telephone yay kiran Dawood. 

        Dandanan Dawood ya amsa kiran boss. Nuna masa kujera yayi alamar ya zauna. Bayan kusan mintuna uku ya ture files ɗin gabansa yana kallon Dawood ɗin.

      “Dawood nikam a ina kasan yaron nan ne?”.

      Cike da girmamawa ya bashi amsa da faɗin, “Sir, tare mukai secondary school da su”.

      “Masha ALLAH, lallai kayi masa sani na sosai. Anan cikin abuja suke?”.

        “Yes sir. Ai yaron sanannen Pastor ɗin nanne Goshpower mai ƙaton catholic church ɗin nan dake a wuse2”.

     Ɗan jimm Jay yay yana kallon

Dawood. Sai kuma ya sauke numfashi kaɗan yana wani guntun murmushi mai kama da an masa dole. “Okay thanks you, zaka iya tafiya”.

     Miƙewa Dawood yayi tare da salute ɗinsa ya fice yana mamakin tambayoyin ogan nasu.


      Dawood na fita Jay ya shiga Google. Bayanai ya nema akan dukkan handles ɗin papa dake a social network. Cikin mintuna ƙalilan kuwa suka watso masa komai. Facebook, Twitter, Istagram, Telegram, dama wasu daban-daban. Harda youtobe chennal da suke ɗaura dakan abubuwansu na church ɗinsu. Numfashi yaja ya furzar tare da shiga kowanne shafi ya duba followers nashi da duk wani posts da yayi a kai. Yawanci duk akan church ne dai.

       Komawa yay bincike akan pictures nashi. A take kuwa suka bashi su da yawa. ‘Oh my GOD!!’. Jay ya faɗa da matuƙar razana. Gaba ɗaya kansa ya sake kullewa. yama rasa kalar tunanin da zaiyi dan da gaske shi dai ya shiga ruɗani. Ta yaya hakan zata kasance bayan shi shaidane akan abinda ya tabbatar a zahirin gani da ido. To amma inhar ta tabbata a tunanin da zuciayarsa ke bijiro masa lallai sai dai idan akwai yaudara a lamarin kenan, ko kuma...... Yay saurin girgiza kansa alamar ba haka baneba sam. dan da sun sani ai.

      A wannan yanayin Bilkisu ta sake shigowa ta samesa. Rungumesa tayi ta baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima ajiyar zuciyar ya sauke sannan ya zagayo da ita gabansa. Kaɗan ya ranƙwafo ya sumbaci laɓɓanta da goshinta.

       “My Boss ina baƙin naka suke?”.

“Sun wuce Miemaa. sai dai ina cikin ruɗani wlhy”. Yay maganar yana jan hannunta wajen kujerarsa.

     Zama tai a kujerar tana bashi amsa itama. “Bakai kaɗai bane a ruɗani. Ni kaina rikicewar ta hanani zama na gudo nabar su Ummie acan”.

      Ta bayanta ya ranƙwafo yana nuna mata abinda ya samo game da papa. Ƙwarai da gaske ta cika da mamaki itama saboda ganin hoton papan. Dan haka sukayi zaman tattaunawa yay mata bayanin dukkan hukuncin daya yanke. Tare da alƙawarin zuwa wajen baba malam kozai ƙara samun wasu bayanai ta wajensa game da papan tunda sun zama surukai.

     Ta gamsu ɗari bisa ɗari da hakan. Harma da zuwan wani cikin gidan, dan Little bee bazai yuwu taje gidan baba malam ɗin ta zaunaba saboda mijinta da wahala ya amince duk da yasan dokar aikin. Amma zai tura ƙaramar ƴarsu autar su Little ɗin mai suna Afrah akan case ɗin da su Yoohan ɗin suka kawo report.


_____________★★★


         Lokacin da Yoohan ya shigo gidan ya iske duk suna church. Sai guards ɗinsa kawai da maigadi aka bari alamar papa yaji shawararsa ta kwanaki kenan. A cikin gidanma daya shiga ya samu Blessing. Cike dajin daɗin ganinsa da tunanin tare yake da Aymah ta shiga masa welcome. Ya amsa mata kadaran kadahan. Ya kama ƙafar benen zai haura Blessing da haƙurinta ya ƙare tace, “Sir Aunty fa?”.

      Juyowa yay ya ɗan kalleta yana lumshe idanu da buɗewa. Sai kuma ya ɗan mata murmushi a bazata dan bata taɓa ganiba. Shi kuma jin daɗin nuna kulawarta ga matarsane ya sakashi yin murmushin. Sai da ya juya ya cigaba da hawa steps ɗin sannan ya bata amsa da, “Tana can na barota. Kina missing nata ne?”.

        Cike da haɗiye ɗokinta tace, “Sosai ma Sir. I miss her so much”.

     “Thanks you”. Ya faɗa a taƙaice yana idasa hayewa.

      Da sanyin jiki Blessing ta koma kitchen dan ta haɗa masa wani ɗan abun duk da baice yana buƙata ba.


      Shikam Yoohan ƙofar sashensa ya buɗe ya shiga. Mayen ƙamshin turaren da Nu'aymah ta fara amfani da su yana nan nane da sashen. Cike dajin sabuwar kewarta ya shiga yana kalle-kallen falon. Tsahon mintuna biyu sannan ya sauke ajiyar zuciya ya nufi bedroom ɗinsa. Harya tura ƙofar ya shiga sai kuma ya fasa ya dawo da baya. Bedroom ɗin Aymah ya nufa, yana ƙoƙarin saka key ya buɗe ya ga ƙofar a buɗe. cike da mamaki ya tura da sauri ya shiga. Turus yaja ya tsaya yana kallon yanda aka hargitsa ɗakin. Kayanta na sawa duk a watse a ƙasa. Littatafanta hardasu Al-qurani duk an yasar. Saurin ƙarasawa yay inda Al-qur'anin izu sittin ke a kife a ƙasa alamar jefarma da shi akayi. Ya ɗaukesa ƙwalla na cika masa idanu. Wani masifaffen fushi na yunƙuro masa da tarar masa a ƙirji.

       Babu wanda yazo masa a rai da yin wannan aikin sai Gebrail. Kodan dama yana nan a maƙale a ransane oho. Ajiye Al-qur'anin yay saman mirror ya fito a matuƙar harzuƙe yana ƙwalama Blessing kira....

     Hakan yayi dai-dai da shigowar su madam Chioma cikin falon suna dariyar shirmen Abraham. A kusan tare suka tsaya cak suna kallon yanda yake sakkowa daga upstairs ɗin da gudu-gudu. Ga wani razanannen kira da yake ƙwalama Blessing. Yana gama sakko idonsa ya sauka akan Gebrail da yake shigowa kusan a ƙarshe.

      Ture Blessing dake isowa gabansa jiki na rawa tana amsa kiransa yayi gefe. Cikin rufewar idanu na rashin ganin su mama debora ya nufi kan Gebrail da duk ya daburce saboda tsorata na rashin gaskiya. A bazata Yoohan ya saukema Gebrail wasu gigitattun maruka a jajjere bisa kumatu. Kafin wani ya samu damar jin ba'asin wannan tashin hankali ya zare belt ɗin jikinsa ya shiga dukansa da shi kai kace ALLAH ne ya aikosa. Gaba ɗaya idon Yoohan ya rufe, Al-qur'anin nan kawai yake ganowa yashe a ƙasa da Nu'aymah a sume a randa Gebrail ya shigar mata.

       Tunda su madam Chioma suke a rayuwarsu basu taɓa ganin irin wannan tashin hankalin da matsanancin fushin Yoohan ba. A take falon ya rikice da kuka da kururuwar ihu. Ina Yoohan sam bama yajinsu. Laftar Gebrail dake ihu yashe a ƙasa iya ƙarfinsa kawai yake ta ko ina. 

      Duk yanda madam Chioma da su mama debora ke kuka da masa magiya basa gabansa. hakama guards ɗin gidan kowa ya gagara matsawa inda Yoohan yake. Solomon da suka dawo tare da su Madam Chioma da yay ƙoƙarin matsawa wai ko Yoohan ɗin zai sauraresa sai da ya samu rabonsa. Dan zuba masa belt ɗaya Yoohan yayi jiki. Da wani irin mahaukacin tsalle da ihu yay gefe saboda azaba.

          Dukan Gebrail Yoohan yayi sosai har sai da yaga ya daina motsi, dan har papa daya shigo gidan tare da su Uncle Godwin bai sauraresuba. Sai da yay tiɓis shi kansa sannan ya jefar da belt ɗin gefe. Daga Momy harsu Joy kan Gebrail sukai suna kuka. Yayinda Momy Destiny ta riƙo Yoohan da shima ƙwalla ke silalo masa tsabar zafin zuciyar da yake a ciki. Zaunar da shi tayi a cikin kujera.

        A can gefe kuma Omar (Rich) daya shigo yanzun ne gidan, saboda ya fita tun safe. Tun a compound sauran guards ɗin gidan ke sanar masa abinda ke faruwa. Da sassarfa ya ƙaraso falon. A yanayin da yaga Gebrail da ihun Madam Chioma daya hargitsa falon da kururuwar cewar Gebrail ɗin ya mutu ya saka bama su Solomon daya gama shan tasa azabar umarnin cicciɓar Gebrail shi da sauran guards ɗin sufice da shi zuwa asibiti.

          Sannan ya ƙarasa inda Yoohan ke zaune yanata huci har yanzu da sassarfa. Cike da tashin hankali ya kamashi ya miƙar batare daya saurari ihun da Maman madam Chioma kema Yoohan ɗin a kai ba. Dan ya tabbata shirun da yay mata zuciyarsa sake kumbura take. Idan kuma har ya miƙe wlhy zai iya bugeta itama dan Yoohan ALLAH yay masa zafin zuciya na bala'i.

         Duk abin nan dake faruwa papa da su Uncle mike na tsaye suna kalonsu tamkar wasu gumakan farkon karni. Hakama baƙi da suka ɗan fara shigowa ziyara sunyi cirko-cirko da tsoro.

       Harabar gidan Omar ya fita da Yoohan da binsa kawai yake cike da rufewar ido. Turasa yayi a mota ya maida ya rufe tare da zagayawa mazaunin driver yaja ya fice da shi daga gidan. Kai tsaye hotel ya nufa da shi. A motar ya barsa yaje ya kama ɗaki sannan ya dawo ya sake kamashi ya shiga da shi ciki.

       Koda suka shiga cikin ɗakin zubewa Yoohan yayi a kujera kawai yana sauke wasu azababbun huci masu ban tsoro. Ruwa mai sanyi Omar ya ciro a fridge yazo ya miƙa masa. Fisgar robar ruwan kuwa yayi ya kafa kai. A mamakina sai gashi ya shanyeta tas yayi wurgi da robar yana juya idanunsa dake jajur abin tsoro.


____________★★★


         A ɓangaren Jay kuwa tun randa su Yoohan sukaje wa jensa a ranar kasa haƙuri yayi, da yamma liƙis ya shirya shi da Afrah suka nufi kano ta dabo gidan baba malam. Abinda bai taɓa yiba. Dan bai taɓa kai iyalansa gidanba tunda suke mu'amulat nasu.

     Sosai baba malam yaji daɗin ganinsa. Dan yamasa ziyarane ta bazata. Ya kumaji daɗin zuwa da Afrah da akai. Wadda bai taɓa saniba a ido, sai dai a baki. Shima bawai ya taɓa tantance ƴaƴan Jay ɗin maza ne ko mata ba. Duk da kuwa Jay ɗalibinsa ne sosai. Dan ya sanshi ne a dalilin mijin Ummu. Dan shiɗin ɗalibin mijin Ummu ɗinne acan saudia. To acan suka taɓa haɗuwa da Jay shi baba malam yaje miƙa gaisuwa ga malaminsa, shi ko Jay yaje  gaida Ummu ɗinsa ne da kuma yin Umrah shi da iyalansa.

       Tun a can suka ƙulla alaƙa. Bayan sun dawo Nigeria kuma Jay ya ringa zuwa ɗaukar karatu wajen baba malam ɗin a duk ranakun weekend lokacin suna a gari ɗaya.

      Har cikin gida baba malam ya kai Afrah. Inda ta samu ƙyaƙyƙyawar tarba a wajen Umm da Muhammad mai saurin sakin jiki da mutane. Cike da ƙwarewar aiki irin na Afrah data sha tun a cikin uwa da uba ta dinga jan Umm da hira akan hotunan Aymah data gani a falon. Umm kam tanada son yara. Gashi Afrah ta shigar mata rai lokaci ɗaya dan ta tuna mata da tata ɗiyar dake nesa da ita. Duk da kuwa Afrah zata girma Nu'aymah da kusan shekaru huɗu ma da wasu watanni, Afrah zatai shekaru ashin da biyu.

      A take Muhammad ya shiga bama Afrah labarin sister ɗinsa. Umm na tayasu da dariya dan sosai drama ɗin Aymah yake bama Afrah ɗin. Har ranta kuma taji kaɗayi dason ganinta.

       Lokacin da Baba malam ya shigo dan kiran Afrah da Jay ke jiran su wuce dan jirginsu ya kusa tashi sai Muhammad duk yay kalar tausayi. Umm ta haɗa mata kayan kwalliya da su kayan fulawa tanata saka mata albarka da godiya. Tare da roƙon ta dinga zuwa musu ziyara dan ita dai sosai yarinyar ta shigar mata zuciya................✍

       

No comments

Powered by Blogger.