Saran Boye 77
No. 77
............Kai Jay ya jinjina masa zuciyarsa a matuƙar raunane ya dubi Yoohan da kansa ke a duƙe yana hawaye. Nu'aymah kanta kuka take hakama Umar. Cikin ɗacin murya da soyewar zuciya Jay yace, “Goshpower nama rasa abin faɗa a gareka.
Dan kaine mutum na biyu da bazan taɓa yafemawa ba da mantawa da shi, bayan gagarumin zalincin da akaima rayuwata da barmin tabo a shekarun baya. Ka cika azzalumi na gasken gaske. Ni nan da kake ganina nine yayan wannan mata ta ɗan uwanka Anum. Mune mukaje har Italy muka taho da ita, tabbas inaji a raina UBANGIJI ya lulluɓe idanunmu daga garekane saboda wannan shine rubutacciyar ƙaddarar Yoohan, wannan wata hikimace daga hikimomin UBANGIJI, ya kuma fimu sanin dalilin yin hakan, kamar yanda ban isa goge abinda aka zana daga zuciya ba, haka ma ban isa canja abinda ya zama rubutacciyar ƙaddara ba domin ALLAH shine kaɗai masanin gaibu, sai yaso mu sani, sai yaso mu gani, sai yaso muji”.A kallo ɗaya zaka fahimci a tsananin firgice Papa yake, dan jikinsa har ɓari yake ya dubi Jay, bakinsa ma rawa yake amma ya kasa cewa komai. Hakama Yoohan da Nu'aymah wani irin kallo mai firgitarwa sukema Jay ɗin. Ya furzar da huci mai azabar zafi da ɗauke kansa. Dan ji yake kamar yay fata fata da goshpower kawai kozai samu sassauci a ransa. Lallai yanaji a ransa idan ya cigaba da zama a gidan nan babu abinda zai hanashi huhhuda jikin Goshpower da bullets, dan haka ya miƙe da sauri ya fice hawaye na ziraro masa a saman kumatu. Komai dawo masa yake sabo a rai da zuciya. Gawar Anum da mijinta ne ke dawo masa cikin ido tamkar yanzu komai ya faru. Zafi da raɗɗi da ruɗanin da suka shiga da mutincin mahaifin Anum da ya taɓu a idon danginsa da al'umarsa a wancan karon na dawo masa a zuciya. Aƙidar larabawa ce wannan gudun zubewar mutuncin dangi. Idan kuwa aka samu kuskure wani abu ya auku na zubewar mutunci ga ɗayanku sai ya shafi kusan duk zuri'arku. To hakance ta faru ga zuri'ar Anum, dan sanadin wannan al'amarin mahaifinta yabar duniya, ƴan uwanta kuwa sai da suka bar ƙasar saudia. Tsakanin rasuwar Abban Anum da Ummu kuwa baifi watanni bakwai ba. Kuma hakan nada alaƙa itama da kasa goguwar tabon da aka ringa jifan Anum da mijinta da shi na safarar ƙwayoyi. Duk da su sunsan ba haka baneba, amma tayaya zasu fahimtarma duniya ba haka ɗin bane?. wannan ciwon shine ya tarwatsasu zaman cikin saudiya ya gagaresu duk da kasancewarsu manyan mutane.
A hankali Yoohan ya miƙe yabi bayan Jay kansa na juya masa, da ƙyar yake iya ganin wajen taka ƙafarsa. Jay na tsaye jikin mota ya kifa kansa kawai yana hawaye yaji an rungumesa ta baya. Kamar dama wannan damar Yoohan ya ke jira sai kawai ya fashe da kuka. Duk mai imani ya gansu a wannan yanayin sai yaji rauni ya ƙara riskarsa. Juyowa Jawaad yayi ya rungume Yoohan ɗin, hakanne ya sakashi sake fashewa da sabon kuka dan yama manta shi namijine a yau.
Jay dake murmushi yana bubbuga bayansa yasa hannu ya ɗauke nasa sabbin hawayen da suke sake zubowa yana kallon su Aliyu dake fitowa da Goshpower da yaransa daga cikin gidan. Basu Jabeer ba, hatta da papa kansa sai da zuciyarsa tai masa nauyi. Sai da aka gama tasa ƙeyarsu cikin motocin sannan Aliyu yazo inda Jay da Yoohan suke. Cikin lallashi yayma abokin nasu kuma ɗan uwan nasu magana akan ya kamata su wuce lokaci na tafiya.
Kai kawai Jay ya jinjina masa. Sannan ya ɗago Yoohan daga jikinsa, hannu yasa yana share masa hawayen daketa zuba babu ƙaƙƙautawa. Ya ɗanyi murmushi da faɗin, “Yarona bazai kasance rago mai kuka a gaban matarsa da jikana ba ai na sani”. Murmushi ya suɓucema Yoohan da sabbin hawaye a lokaci ɗaya, sai yay saurin sake faɗawa jikin Jay ɗin kuma.
Suma su Naser dake sharar hawaye duk ƴar dariya sukayi saboda yanda Yoohan ɗin yayi. Jay ya yafito Nu'aymah dake goye da Deen tana ta faman kuka itama. “Zo nan my daughter ki lallashi mijin nan naki naga da gaske ɗan shagwaɓa ne”. Ƙarasowa Nu'aymah tayi tana murmushi da hawaye. Jay ya sake ɗago Yoohan yana faɗin, “Kai dama ashe likitoci ragwagene ban saniba ni Muhammadu?”.
Cikin dariyar ƙarfin hali Jabeer yace, “Boss da alama kam, dan gashi Son ya tabbatar mana”. Duk sukai ƴar dariyar ƙarfin hali data rage musu nauyin zukata. Daga haka suka shiga motoci, dan an bincike gidan babu komai a cikinsa. Sabone ma da alama suma su papan jiya suka shigesa. Su Yoohan mota ɗaya suka shiga da Jay. Umar yaja motar, Jay na gefensa, Nu'aymah da Yoohan a baya. Su Abdallah kuma suka koma a motar da sukazo suma. Waya Jay ya ɗauka ya turama Baba malam text message dan hankalinsu ya kwanta, kafin ya juyo ya kalli su Yoohan dake taimakama Nu'aymah ta sakko da Deen daya sake farkawa daga barci.
“Abuja zan wuce da ku, zanyi magana da malam insha ALLAH”.
Sun amsa masa da girmamawa, dan shi kansa Yoohan baya buƙatar yin nesa da Uncle ɗin nasa sam.
Su Abdallah sun wuce gida kamar yanda Jay ya basu umarni, su kuma suka wuce airport domin komawa abuja, fatansu suyi sallar asubahi acan insha ALLAHU.
_____★
Idan nace muku wani babba mai hankali a gidan su Nu'aymah ya rintsa a wannan dare nayi ƙarya. Kamar yanda su Ahmad suka kwana zaune tare dasu Papa haka suma su baba malam suka kwana zaune cike da tashin hankali. Duk da ma Abdallah yayi ƙoƙarin kiran wani a gidan ya sanar masa anga su Yoohan ɗin amma network yayta basa wahala. Dole ya haƙura kawai musamman da labarin da papa ke basu ya ɗauke masa hankali da tunani.
Motar su na shiga cikin gidan duk su baba malam suka firfito da yakema asuba tayi. Ganin babu su Aymah tare da su ya saka jikinsu ƙarayin sanyi kuma. Sai dai kuma Murmushin kwantar da hankali da Naseer yayi ya saka zuciyarsu samun sassaucin bugawar da takeyi. Su Abdallah suka ƙarasa garesu jikkunansu duk a sanyaye, dan gaskiya ba ƙaramin tausayin Yoohan zukatansu suke a ciki ba.
Kafinma wani a cikin su baba malam yay magana malam ƙarami yace, “Abba ku kwantar da hankulanku duk an gansu, sai dai sun wuce abuja yanzu haka tare da Uncle Jay, harma da masu laifin”.
Kusan a tare suka shiga sauke ajiyar zukata, dan baba malam baiga text message ɗin Jawaad ɗinba dama. Jin haka yasa baba malam cewa, “Alhamdulillahi ala'kullihalin, inaga sai muje kowa yay haramar salla dan lokaci yayi”.
Ina idar da salla kuwa kowa dole ya nema gado ramuwar barcin daya gagaresu. Musamman ma Umm da jininta ya hau ita da Hajjo.
★★★
Ƴan Abuja ma dai suna sauka wucewa akai da su Papa station, madam Chioma natama mutane kukan iskanci wai Yoohan ya taimaketa kar sonshi ya kasheta. Wannan kalma ta daki zuciyar papa. Ya bita da kallon tsoro da firgici sai dai babu bakin magana dan shi koma tafiya baya iyayi saboda duka ƙafafun sunsha harbi.
Ganin yanda Deen ke numfashi da ƙyarne yasa Yoohan bayan sunje gida sun sauke Nu'aymah su kuma suka koma massallaci. Suna idar da salla yace zaije ya samowa Deen magani dan an ɗibar masa sanyi. Jikin yaronma zazzaɓine.
Nu'aymah na shiga Miemaa ta fito ta shiga da ita ciki dan Jay ya kirata dama. Ganin yanda Deen keta kuka yasa ta amshesa ranta duk a jagule da ɗaukar alhakin yaron da akayi. Bata wani zauna jan zance ba tai ciki da shi, tare da cewa itama Nu'aymah ta biyota tazo tai wanka dan duk a galabaice take. Ruwa mai zafi ta haɗa mata, shima Deen tai masa wankan da ruwa mai ɗumi sosai. ta kuma gasa masa jikin da towel dan tasan mugayen can ba ɗaukar tausayi zasuma yaron ba. Aiko anayi yana uban kuka. ana kammalawa tunkan ta tsamesa a ruwan har yayi barci. Tausayin yaron ya kuma kamata. Goyashi tayi domin yin salla. bayan an idar ta nufi ɗakinta da Nu'aymah ke can. Har tayi wanka tama shirya cikin doguwar rigar data bata. kasancewar ba salla zatai ba tana zaune tana matsa ƙafarta da tun ciwon dataita mata da cikin Deen har yanzu data haihu bata gama saki da ƙyau ba. “Yauwa ɗiyata kin idar?”.
Kan Aymah a ƙasa tace, “Eh Miemaa ina kwana?”.
“Lafiya lau, ya gajiyar gwagwarmaya?”.
Murmushi Nu'aymah tayi dan kuwa da gaske jiya sunsha gwagwarmaya mai wahalar mancewa a tarihin rayuwa. Miemaa ta bata Deen daketa ajiyar zuciya yana barci. “Kinga bashi abinci, kema bara na haɗo miki ko tea ne kisha ku kwanta ku huta”.
Babu musu Aymah ta amshesa. Miemaa kuma ta fita haɗo mata tea. Yanda Deen ke amsar abincinsa har tausayi ya bata. Dan ita dai acan bawani samun nutsuwar ƙwarai tayi wajan basa ɗinba. Ta shafa kansa tare da kissing goshinsa, daga shi har mahaifin nasa ɗunbin tausayinsu da ƙaunarsu ya mamaye mata zuciya. Babu jimawa itama Miemaa ta kawo mata tea da bread da soyayyan ƙwai. Amsarsa tayi da cewa. “Zauna kema ki karya, bara naje da shi babansa zai dubasa, idan kin kammala ki kwanta kema ki huta”.
Godiya Aymah tai mata. Miemaa kuma ta fita.
A falo Yoohan ya amshi Deen ya dubashi da bashi maganin daya siyo sannan Miemaa ta sake amsarsa ta goya. Sashen Awwab da baya ƙasar yana Spain aka kaisu. Jay yace suyi wanka su sha tea ga shi nan da Miemaa ta haɗa musu suyi barcin gajiya. Sun masa godiya. Su dukansu barcine a idonsu, hakan yasa basu wani zauna zaman maida yanda akayi ba. Dan Yoohan ma sai da yasha magani saboda ciwon kai. da taimakon maganinne ya samu barci mai nauyi yay gaba da shi.
__________★
Su Aymah sunsha barci sosai. Bayan tashinsu duk suka sakeyin wanka. Zuwa lokacin gida ya cika da su Little bee. Sunsha kuka labarin da Jay ya basu game da ainahin gaskiyar rasuwar Gwaggosu Anum da mijinta. Da kuma tabbatar Yoohan ɗan uwansu. Lamarin ya taɓa musu zukata sosai duk da bama sanin Anum ɗin sukai ba su. Sanda ta rasu Little kaɗai aka haifa, bakuma wanda ya taɓa faɗa musu gaskiyar magana akan rasuwar tata sai yau. Deen yana hannunsu kowa ji yake da shi, hakama da su Yoohan suka tashi sai murnar kowa ta ƙaru. Anuwar ya rungumesa yana kuka. Shima Yoohan ɗin sai da ya koka. Ransa kuwa cike yake da ɗumbin farin cikin tsintar kansa a cikin dangin mahaifiyarsa. Ya ɗauki komai matsayin ƙaddara kamar yanda Uncle Jay ya faɗa.
Sunci sunsha tare, kafin su zauna kuma aka gabatar da juna. Sannan aka tsaida ranar da zasuje Oman wajen sauran dangin Anum da ke can a yanzu suna rayuwa. Anan kuma Nigeria za'a zagaya dasu cikin danginsu suma insha ALLAH.
Kiran Jay da aketayine ya sakashi fita dole. Dan yau daga shi har Miemaa da little basu fita aiki ba. Duk da kuwa gari ya ɗauki ɗumi akan kama Papa da yaransa da akayi. Musamman daya kasance an saki video ɗin labarin da papa ya bayar akan saka twin Brother ɗinsa a tarko domin shi ya kuɓutar da kansa. Wannan al'amari ya girgiza zukatan jama'a sosai. Masana nata sharhi akan hukunci daya dace ace ya fuskanta. Wasuma gani suke a kashesan kawai shine babbar mafita ga ƙasar gaba ɗaya. Dan barinsa koda a prison ne wataran wani zai iya fiddosa a ɓoye tunda ƙasar tamu sai a hankali. Hakama jama'ar gari ba'a barsu a bayaba wajen maida yanda akayi dayin sharhi akan wannan al'amari.
Lokacin da labarin ya isa gidan su Aymah har cikin kunnen Mama debora sai ta yanke jiki da faɗi. Dan su su Abdallah ne sukai zaman faɗa musu yanda komai ya faru ma. Kwasarta akai zuwa asibiti a rikice, su Victoria nata faman kuka dan suna ƙaunar kakar tasu. Musamman daya kasance yau sun wayi gari da wannan tashin hankali na halayen iyayensu da ya ƙara fitowa duniya taji. Basu da kamarta a yanzu, dan sun tabbatar ko ƙauyensu kam yanzu sai ya gagaresu zuwa, dan maimakon tarba da zasu samu daga jama'ar garin kamar da, yanzu idan sunje duka zasuci.
Ganin ta farfaɗo baba malam ya hana a faɗama Yoohan. Yace a barsa shima ya hutama ransa, idan ta warware zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu sai suma a maidasu Abuja ɗin.
Su Nu'aymah basu san hidimar da akeba. suna nan cikin zuri'ar data kasance ta Yoohan hankalinsu kwance, kowa zallar ƙauna da kulawa yake ƙoƙarin nuna musu. Tare da bama Yoohan labarin dangi kala-kala dana mahaifiyarsa, tare da hotunanta. Ranar dai haka suka kasance cikin ɗumbin farin ciki, dan ma fitar Uncle Jay ta rage armashin hirar.
A ɓangaren Jay kuwa ashe kirane na sirri ya samu daga manyan ƙasa. Inda sukai zaman tattaunawa dangane da shari'ar papa. Sun yanke shawarar a miƙasa hannun ƙuliya manta sabo da wuri. Wasuko sunce ai masa allurar poison tun kafin shiga kotun, dan suna tsoron abinda zai iya zuwa ya dawo musamman da Goshpower ya kasace yaron manyan shegun duniya ne. Babu hanyar da bazasu iya biba domin ganin sun kuɓutar dashi. Barin irin su papa a duniya kam ai tashin hankaline. Dan babu makawa a yini guda suna iya tada jama'ar ƙasa da ƙasar baki ɗayanta.
Shi dai Jay bai yarda ya tofa wata maganaba, dan suma ɗin ai baisan yaya nasu zukatan sukeba, balle ayyukansu na ƙarƙashin ƙasa. Sannan baima saniba ko suma ɗin wani abu sukesan binnewa ta wannan hanyar tunda kowa yasan yanda papa ke mu'amula da manyan mutanen ƙasar ai. Sai da duk suka gama surutansu yace shidai a nashi shawaran kawai su bari a miƙasa kotun, yanke hukunci aikin alƙaline ba nashi shi jami'in tsaroba. Idan kaga mai laifi ya rasa ransa a hannun jami'in tsaro sai dai akan kuskure ko kare kansa ga mai laifi idan yanada makami. Amma haka ɓakatatan basu da damar yima goshpower allurar poison. Duk da wasu sun nuna jin haushinsa shidai bai damuba. Yay musu sallama ya wuce office. Gudun zuwan abinda zaije ya dawo ya sakashi tattara duk wasu bayanai dake a hannunsa a yammacin ranar ya tura ƙara kotu sannan ya koma gida.
Miemaa kaɗai ya sanarma halin da ake ciki, amma su Yoohan baice musu komaiba, saima sakawa yay aka kawo masa Deen da bai gajiya da barci saboda kasancewarsa jariri har yanzu. Kwata-kwata yau kwanansa tara kenan ma a duniyar. Amma ya fara cin karo da gwagwarmayar cikinta.
Kasancewar Aymah jego take yasa Miemaa tsayuwar daka a kanta ta ƙarasa jegon anan, dan summa gama magana dasu baba malam idan su mama debora zasu wuto Abuja gobe idan ALLAH ya kaimu zasu taho mata da kayanta dana Deen kawai. Koba komai hankalin Nu'aymah yaɗan nutsu waje ɗaya yanzu, hakan yasata ƙagara ma a kawo mata kayanta ta koma sauraren lectures kota online ɗinne kafin suga abinda ALLAH zaiyi akan maganar komawarsu. Danshi kansa Yoohan harma ya ɗauki hutun ƙarshen shekara mai nisan zango sosai.
Washe gari su Jay suka tattare al'amarin papa suka miƙa kotu, yayinda dangi keta tururuwar zuwa gidan Jay ganin Yoohan. Dan su Afrah duk sun baza labari ta waya. Khairiyya kanta da ba'a garin take aure ba sai gata a wannan ranar ganin yayansu. Duk da dai bama wani girmanta yayi sosaiba, amma dai little ta girmesa. shiyyasa abu kaɗan ke sakasu fara faɗa. Shi son girma ita son girma. Daya motsa tace shiɗinfa ƙanintane. Shi kuma yace ALLAH ya kiyaye ya zama ƙaninta. Abun nasu na bama kowa dariya. Musamman ma Nu'aymah.
*_WASHE GARI_*
Washe gari su Mama debora da taji sauƙi duk da bata koma garau ba suka iso abuja saboda suna son halartar zaman kotu da za'ayi. Ba kowa ya matsa hakanba kuwa sai mama debora. Dan tasha kuka, acewarta tanason taga idon papa ko zaiji kunyar yaudarar da yay mata na saka ɗanta mutumin kirki a tarkon da aka kashesa.
Da yake tafiyar mota sukayo, kuma sun taho da wuri sai gasu kusan sha biyu sun shigo garin Abuja. Yoohan na tsakkiyar dangi da keta cigaba da zuwa kiran Gebrail ya shugo wayarsa. Ɗagawa yay ya koma gefe. Cikin girmamawa Gebrail ya gaidashi da faɗa masa gasu sun shigo Abuja. Zasu wuce can gidanne kokuwa suzo nan gidan Uncle Jay ɗin su samesa?.
Yoohan yay ɗan jimmm kafin ya furzar da numfashi, yace, “Okay, inaga ku wuce can, nima gani nan zuwa gidan”.
Da girmamawa Gebrail ya amsa masa da to. Yana yanke wayar ya sami Uncle Anuwar da maganar, dan Uncle Jay baya nan ya fita saboda sunata kai kawo akan lamarin papa da yaransa su Solomon.
Uncle Anuwar yace, “Yahya ai daka barsu sun wuto nanɗin kawai, dan an riga da an zama ɗaya yanzu. A gidan nan kuwa munada isassun masauki insha ALLAH. Sanann kusancin zama da zamu samu dasu yanzu zaisa suma idan sunada rabo sai kaga sun karɓa musulinci”.
Cikin ɗan sosa wuya da jin daɗin wannan fata Yoohan yay murmushi idonsa nakan Nu'aymah da suke hira dasu Afrah acan gefensu. Yasan komi rayuwarsa ta zama a yanzu itace sila, dan haɗuwa da ita shine ya zama hasken da ya haska masa hanyar da yake taka ƙafa, iska yaɗan furzan da faɗin, “Okay Uncle bara naje zuwa anjima ai sai nazo dasu ɗin, kagama sannan Uncle Jay ya dawo”.
Kamar yanda Yoohan ya faɗa bayan sallar azhur ya nufi gidansu. Duk an janye ƴan sandan da suke zagaye da gidan, ko maigadi yanzuma babu balle waɗannan guards da ke cike da gidansu a da. Rayuwa kenan, ka shuka alkairi sai ka girbe abinka. Horn yayi kusan sau uku sannan Gebrail yazo da ɗan gudunsa ya buɗe masa gate ɗin. Sai da ya gama ƙarema harabar gidan kallo da duk motocin dake cikinsa kafin ya furzar da nannauyan numfashi ya fito, dan Gebrail ya buɗe masa tuni.
Cikin gidan suka nufa yanama Gebrail tambayoyi, shi kuma yana amsa masa cike da damuwa, dan har cikin ransa kunya da ƙaunar Yoohan ce cike da ruhinsa. Bama shi kaɗaiba, duk sauran ƴan uwansama hakane. Suna shiga kuwa da gudu su Victoria sukazo suka rungumesa. hakama mama debora rungumesa tai tana kuka da rera addu'ar neman sakayya a garesa da yarensu. Ba itaba ko mai saurarenta yaji yanda take addu'an zaisan akwai tausayi a ciki.
Da ƙyar Yoohan ya lallashesu sannan suka zauna suka ɗan sake tattaunawa. Mama debora tace tunda har papa ya kashe ɗan uwansa da matarsa itama ta yarda a kashesa. Yoohan dai kunyar su Gebrail ya hanashi cewa komai akan iyayen nasu, daga ƙarshema yace su shirya zai wuce da su.
Zan iya cemuku a ɗar-ɗar su mama debora suke da zuwa gidan Jay, kamar yanda sukaita ɗari-ɗarin zuwa kano gidansu Nu'aymah. Sai dai abinda ya basu mamaki anan ma sai akai musu tarba ta mutunci da kulawa. Hakan yasa suka sakeji a ransu lallai hausawa nada ƙyaƙyƙyawar zuciya a duk inda suke. Sannan musulmai ba mutanen banza bane kamar yanda a kullum papa ke musu huɗuba a gida da church. Sai gashi tundai suna ɗari-ɗari har suka saki jikinsu. Bayan Jay ya dawo suka zauna aka ƙara tattaunawa. Mama debora da su Momy Destiny sunsha kuka. Su kansu su Joy sunji ciwo da kunyar halayen iyayen nasu matuƙa. Sunata kuka da bama Yoohan haƙuri. Shi dai murmushi kawai yake musu. Nu'aymah ma haƙuri sukaita bata akan abinda sukai mata. Tace babu komai ita ta yafe musu. Gebrail kam ko yarda su haɗa ido Aymah baya yarda suyi sam saboda kunya. Ita har dariyama abin ke bata.
____________
Ranar data kasance za'a shiga kotu da su papa ƴan jarida a abuja har bama magana. Kowa burinsa ayi komai akan idonsa. Kuma burin kowa ya nuna komai live. wannan kuwa duk a cikin shirin su Jay ne. Sun gayyato ƴan jaridune ta kowanne ɓangare dansu katange dukma wata kitumurmura da za'a iya ƙullawa game da shari'ar.
Kotu ta cika maƙil itama da al'umma, musamman waɗanda aka samu ƴaƴansu a gidan papa. Duk da ma wasu iyayen nasu sun gagara ganesu, sukuma basusan daga inda aka ɗakkosu ba dan tun suna ƙanana ne. Shari'a ce da bata buƙatar lauya sam, saboda komai na papa a bayyane yake. Zamane kawai da za'ai maganar ƙarajin abinda ya shuka a yanke hukunci kuma.
Yoohan dai da farko baiso su Gebrail su bisu ba. Amma sai Uncle Jay yace ya barsu suje ɗin dan wannan itace kaɗai damar da zasu samu ganawa da iyayen nasu. Badan yasoba kuwa suka shirya suka tafi kotun, cikin amincin ALLAH kuwa sun sami gaba-gaba saboda sun tafi da wuri.
Sai da kotu ta gama cika tab da al'umma, alƙali ya shigo sannan aka shigo da papa da su Mike. Papa saboda harbin da yasha a kafafu sai a wheelchair, sauran kuwa babu ko ƙwarzanen duka a jikinsu amma a ido zaka gansu a wani irin bala'in galabaice. Su Jay kaɗai sukasan irin horon da sukema rayuwarsu cikin hikima. Bayan buga gudumar alƙali kotu tayi tsitt na wasu mintuna, dan da anata ƴan kananun magana saboda shigo da su papa da akayi.
Alƙali ya sakeyin gyaran murya sannan ya fara magana, “Wannan shari'a ce da kowa zai iya fahimtar bata buƙatar wani kaiwa da komawa balle zaman lauyoyi a tsakani. Dan komai a bayyane yake wa duniya akan masu laifin. Amma duk da haka dolene mu karanto musu laifinsu su amsa kafin mu yanke hukunci”. Bai jira amsar kowaba dan ba ita yake jiraba daman. ya bama jami'an tsaro damarsu. Dawood ne ya miƙe ɗauke da file ɗin dukkan bayanan laifukan Papa ya kai ga alƙali. Batare da alƙali ya amsaba ya bashi damar karanto komai.
Tsayuwa Dawood ya gyara yana fuskantar su papa. Ya fara bayani dalla-dalla. a duk gaɓar da yazo ƙarshe alƙali zai ma su papa tambaya akan shin hakane sun aikata?. sukan ɗan nuna tirjiya kafin papan ya tabbatar da sun aikata ɗin. A haka aka dinga bin duk laifukansu daki-daki tare da shedun da suka gani da ido wajen tabbatarwa. Hakanne yaja shari'ar tai tsaho sosai aka jima ba'a tashiba.
Ƙara jin bayanan sai ya ƙara komawa mutane tamkar sabo a cikin kunne, wasu harda hawaye sukeyi, wasu ko kawai gani suke babu hukuncin da su papa suka dace dashi sai mutuwa. Da ƙyar Alƙali ya samu kotun nan ta lafa da ga hayaniyar data ɗauka akan cecekucen jama'a. Ya ɗauki ruwan dake a gabansa ya sha cike dajin gajiya da damewar tunani wajen yanke wannan hukunci.
Bayan kotu ta sake lafawa alƙali ya fara magana kamar haka, “Ya kamata kuyi hakuri ku bamu haɗin kai, nasan duk wani hukunci da zamu yanke anan bai zama lallai ya gamsar da waɗanda wannan mutane suka cutarba. Amma zamuyi iya bakin ƙoƙarin mu dan ganin mun yima kowa adalci. Sun tafka kura kurai da kowanne idan zamu ɗauka yanada nashi hukuncin ne, to amma kisan kai da suka shigo sun shanye duk wani laifuka nasu. ALLAH kaɗai yasan iya rayukan da suka salwantar, dan kosu a yanzu ba iya lissafawa zasuyi ba. Dan haka wannan kotu mai adalci, ta yankema waɗanan mutane hukuncin kisa ta hanyar rataya”. Yana gama faɗa ya doka gudumarsa.
A take kotun ta ɗauki ihun kace nace ɗin mutane. Har bakajin zancen wani. Sai dai duk wannan surutai babu mai goyen bayan su papa. Wasuma duk da an ambaci kashesun za'ayi su hukuncin sai bai musu ba. a ganinsu ayi gunduwa-gunduwa da su kamar shine yafi dacewama kowa ya huta. Kamar yanda kotu ke a harmutse haka jama'ar gari ke a harmutse dan ƴan jaridu nata kai rahoto live. A take duniya gaba ɗaya ta ɗauka. Inda wasu ƙungiyoyi kamar Masu kare haƙƙin ɗan adam suka fito suka nuna bore da wannan hukunci. Har suna iƙirarin ɗaukaka ƙara. Sai dai to bamusan zuwa wane kotu suke da burin ƙarar ta kaiba, tunda mudai anan Nigeria a babbar kotun ƙasa gaba ɗaya aka yanke hukuncin.
Duk yanda Yoohan yaso su mama debora su gana da Papa al'amarin ya gagara dan da ƙyarma aka fiddasu daga cikin kotun.
______________★★
Bayan kwanaki biyu da faruwar wannan al'amari da safe su Jay na tsaka da yin breakfast ya samu waya daga alƙali cewar sufa sun gama yanke hukuncin su papa. Dan sun fuskanci al'amarin neman canja salo yakeyi na ƙirƙirar rikici da hukumar kare haƙƙin ɗan adam ke neman haddasa musu. A yanzu haka maganar da ake ga gawarwakin su papa nan, a gaban ƴan jarida akai komi yanzu kuma zasu bada damar a saki labarin.
Al-amarin ya girgiza zuciyar Jay matuƙa, to amma shima hakan yafi masa sauƙi tunda dai shine hukuncin da aka yanke musu a gaban kowa. Koda sukai sallama da shugaban alƙalai bai iya yima su Yoohan bayanin abinda ya faruba sai Miemaa kawai. Ita kanta duk da tasan su papa masu laifi ne sai da tausayin mama debora ya ƙara kamata da su Victoria. To amma wannan shine dai-dai kuma abinda ya dace..
Kafin shabiyun rana labari ya gama zagaye ƙasar dama duniya akan zartar da hukuncin da aka yankema su papa. Wasu kam sun ɗauki ɗumi akan hakan, dan duk da mummunan halin su papa suna samun magoya baya musamman masu irin halayyarsu da ayyukansu. To andai yita ta ƙare. labarin su papa kuma ya zama tarihi, sai kuma na baya garesu, dan yanda mutane. kirki basa ƙarewa hakama mutanen banza kullum sake yawaita suke.
Mama debora dai tasha kuka a ɓoye, dan ɗa da mahaifi sai ALLAH, musamman daya kasance mazan ƴaƴanta har uku. To amma tunda ta rasa mahaifin Yoohan da yafi sonta da ƙyautata mata tai haƙuri, dan ta rasa waɗanan azzaluman minene zaisa ta takura kanta kuma. Su Joy ma dai saida suka koka sosai. danma an hana Abraham da Victoria kallo sam.
Yoohan kansa sai da yay hawaye, koba komai yasan su ɗin jininsa ne. Nu'aymah ce kawai ta iya fahimtar shima kukan yayi, dan haka tana ganin ya fita itama ta bisa a sace ta ƙofar kitchen. Acan baya ta hangosa tsaye ya jingina da bango yay shiru idanu a lumshe. Ƙarasawa tai garesa ta kamo hannunsa cikin nata. Kusan a tare duk suka sauke ajiyar zuciya. Batare da yace da ita komaiba ya jawota jikinsa ya rungume. Luf kuwa tayi kusan mintuna uku sannan ya ɗagota yana murmushi. Kafin yay magana tace, “Silly boy! Kuka kakema waɗanda suka kashe mana su Abbabmu saboda son zuciya”.
A karon farko ya saki murmushi da shafa fuskarta. Murya a raunane yace, “Silly girl! Kin samin ido da yawa fa”.
Dariya tayi kaɗan ta kwantar da hankali, sannan ta ɗan marairaice fuska cike da kulawa tace, “Sai haƙuri Yah Maleek, haka rayuwa take, wani farkonsa yaji daɗi ƙarshen yasha wahala. Wani yasha wahala a ƙarshe yaji daɗi koba a duniyaba. Kaji labarin gwagwarmayar da Uncle Jay yasha shima shi da Miemaa. Amma bagasu komai ya wuce a garesuba tamkarma bai faru ba. Muma idan mukai haƙuri sai kaga komai ya zama tarihi insha ALLAH ”.
Cike da jin daɗi ya sake rungumeta da sumbatar laɓɓanta. Ya lumshe idanunsa ya sake buɗewa a kanta. “Thanks you Zeeynab. Kin gama bama rayuwata dukkan abinda take buƙata, ALLAH yay miki albarka ya albarkaci Deen, ALLAH yasa ya zama mai gadon baba malam. ALLAH ya gafartama iyayenmu ya ƙara mana haƙuri da abinda ƙaddara ta danƙa mana a tafin hannunmu”.
“Amin ya rabbi yah maleek”.
Sake rungumota yay jikinsa yana dariya ƙasa-ƙasa da fadin, “Sunan nan fa yayi daɗi Sweet girl”.
“Sosai ma, Mami da Abba sun iya zaɓen suna. Kaga yanzu ka zama mai suna biyu, danni kam daga yau Abdul-maleek zanke faɗa”.
“Silly girl! ki rage jan faɗa yanzu akwai Deen a gabanki”. Ya faɗa yana jan hancinta.
A tare suka sanya dariya, suna maijin farin ciki mai yawa a ransu.
A daren ranar kuma sai ga saƙon rasuwar Addah ya samesu. Duk da abinda ta tafkama rayuwarsu Nu'aymah sai da taji duk ta rikice. Tasha kuka kuma a daren ranar. Washe gari kuwa tunda safe suka ɗauki hanyar kano a mota harda su Jay, cikin sa'a kuwa suka samu jana'izar Addah, dan sai goma aka kaita masaukinta na gaskiya. Sai kuma aje a girba abinda aka shuka.
Duk da abinda Addah taima Umm rasuwarta tayi masifar girgizata, dan saida takai an saka mata ƙarin ruwan daya sakata dogon barci saboda ruɗanin data shiga. Jikin kowa ya ƙara sanyi kuma a agidan harma da sauran ƴan uwa.
Da yamma su Yoohan suka koma Abuja aka bar Nu'aymah anan kano, sai bayan anyi addu'a Yoohan yace zaizo ya ɗauketa dan zasuje Oman wajen dangin mahaifiyarsa da ƙaddara ta maida can.
*_BAYAN SATI GUDA_*
Bayan sati ɗaya da rasuwar Addah da mutuwar su papa Yoohan yazo da kansa ya ɗauki Nu'aymah da Deen suka koma Abuja, zuwa yanzu kuma Alhmdllh Umm ta ɗan dake saboda kulawa da baba malam keta bata dan ganin ta samu kwanciyar hankali. Hakama Hajarah daketa fama da tsohon ciki sai Umm ta roƙu mijinta ya barta ta dawo nan gida harta haihu dan itama rasuwar mahaifiyar tata ta taɓata sosai. Bai musaba ya barta ta dawo, tana nan zaune wajen Umn yanzu haka. Zaman natanema ya ɗan ragema Umm raɗaɗi. Hajjo kuma koda yaushe takan yawaita shigowa ta sake kwantarma da Umm hankali itama, hakama Ananah da bata komaba.
*_OMAN_*
SU Nu'aymah sun isa Oman lafiya, inda suka sami tarba ga dangin Mami (Anum) dan tunkan zuwansu labarin komai yazo musu. Abin mamaki sai su Yoohan suka sami Dr Shikurah acan Oman, ashe kanwarta datake faɗa ɗanta na kama da Yoohan itace ke auren yayan Anum da suke uba ɗaya. Sun haɗune acan Oman da taje karatu, a yanzu haka yaransu kusan shidda. Mahboob mai tsananin kamanni da Yoohan shine yaronsu na farko. Idan ka gansu shi da Yoohan saika ɗauka tagwayene saboda tsabar kamanni da sukeyi da juna, abin mamaki har tafi har maganarsu iri ɗayane. Sosai abin ya birge Yoohan. Har yaji a ransa inama ya amince tun sanda Dr Shikurah ke masa kamanni da Mahboob ɗin ya amince ta kawosa yagansa. To amma ya ɗauka hakan kawai matsayin abinda ALLAH bai hukunta ba.
Da yake anzo dasu mama debora suma sai hakan yasaka dangin Anum ƙara jin daɗi, dan koba komai sun ƙara yarda IBRAHEEM mutumin kirkine shi. Ansha kuka da tunawa da rasuwarsu da yanda rasuwar tazo. tare da jifan su papa da kalmomin ALLAH wadarai danma ana ɗan tagawa darajar mahaifiyarsa dake a wajen.
Deen da Nu'aymah kam lallai sunga soyayya ƴar gaske, dan gatan da Yoohan bai samu ga dangin uwaba a yanzu kowa ƙoƙarin ganin ya nunama Deen yakeyi. Sunga gata kam sun kuma sha daɗi Alhmdllh. Satinsu uku cif suka dawo Nigeria badan ƴan Oman sunso hakaba.
Suna dawowa kuma aka shiga hidimar bikin Naser & Yusrah, Abdallah aka maida masa Adawiya suje su cigaba da haƙuri da juna. Amal da malam ƙarami. Ahmad da Nanah yayar ƙanwar Umm. Ansha biki an raƙashe an ƙwalle Alhmdllh, yayinda Abban Abdallah ke kwance yana fama da kansa shima. Dan shikam bikinma bazaice yasan anyiba. To dama haka rayuwar take ai.
Bayan an gama biki an miƙa amare ɗakunansu komai ya zama Alhmdllh Yoohan ya tattara matarsa da ɗan ɗansu da yay ɓul-ɓul gwanin sha'awa syuka koma ƙasar U.S saboda karatun Aymah, shi kuma zai koma aikinsa na hidima wa al'umma.
Basubar ƙasarba sai da ya nemawa su mama debora gida anan kusa da su Uncle Jay aka saya musu, dan mama debora ta rantse bazata sake zama gidan can da papa ya gina ba. Hakan yasa aka saidashi suka dawo nan. Gebrail da Joy an nema musu makaranta a ghana. Mama debora zata cigaba da zama dasu Victoria dasu mama Destiny da suma suka dawo nan tare da mazajensu. Dan zaman can kauyen kam bazai yuwu yanzu a garesuba.
_____★
Tunda su Nu'aymah suka dawo fa sai ta ɗaura ɗammarar dagewa akan karatunta, haka shima Yoohan ya sake dagewa akan neman iliminsa na addini. Ga renon ɗan ɗansu daketa ƙara girma masha ALLAH.
Soyayyarsu da shaƙuwa kuwa sai abinda yay gaba. Yayinda Hajiya Nu'aymah aketa ƙara canjawa ana hankali da rage fitsara kamar ba itaba. Ga jikinta sai buɗewa yake tana ƙibarta masha ALLAH.
Haka rayuwa ta ciga da gunguramawa waɗanan bayin ALLAH, yau asha zuma gobe asha maɗaci. Da sun sami hutu sukan shirya suje Nigeria, hakama ƴan Nigeria ɗin lokaci-lokaci Yoohan kan ɗakko wasu a cikinsu suzo su musu hutu.
Daga Deen dai Nu'aymah shiru, da alama kuma dai sune asuka tsarama kansu hakan, dan a yanzu haka ga Deen da shekara ta huɗu, Nu'aymah kuwa na shirin kammala karatunta. Yaro ya girma yay wayau, ga miskilanci ga zuciya ko kuturu haka ya gansa ya bari.
burin Yoohan dama nu'aymah ta kammala karatunta ya tarkatasu ya maida Nigeria, cikin amincin UBANGIJI kuwa sai gashi ta kammala lafiya cike da nasarorin rayuwa. Wannan karon kuwa Umm da baba malam ma sunzo U.S, taso azo da hajjo baba malam yaki dan tsufa sosai ya ƙara kamata, ga ciwon ƙafa dake damunta. Kowa ya taya Aymah murna da nasarar data samu daga ita har mijinta, bayan kammala komai suka tattaro zuwa ƙasarsu ta haihuwa, inda Yoohan ya saya musu gida suma duk da su Jay sunso Yoohan ɗin yay zamansa anan gidansu, amma ya ƙi, dan gaskiya yanajin kunyarsu ainun.
Ƴan uwa da abokan arziki sun tayasu murnar gida. Dan ƴan kano ma duk saida sukazo, harda su Aunty Kubrah da zuwa yanzu tayi haƙuri a gidan aurenta duk da ba daɗin zaman takejiba dai.
A wannan dawowane kuma kowa ya fahimci Nu'aymah laulayin ciki takeyi. Anko tayasu murna da addu'ar ALLAH ya raba lafiya.
Dawowarsu baifi da wata guda ba ALLAH yayma abban Abdallah rasuwa shima. Ansha alhini ansha kuka, daga baya kowa ya rakasa da addu'a.
*_A KWANA A TASHI_*
Lallai kam akwana atashi babu wahala wajen UBANGIJI, dan yanzu shekarun Auren Nu'aymah da Yoohan goma kenan. Zuwa yanzu ALLAH ya azurtasu da ƴaƴa uku, Deen, Ibrahim, sai auta Anum. Jay ne ya hana a ɓoye sunan yaran, yace a bari ake kiransu da sunansu hakan zaisashi farin ciki. Dan haka aka barsu kuwa da sunayensu ana kiransu da shi.
Abubuwa da dama kam sun faru a waɗannan shekaru, masu daɗi da akasin hakan sai dai kawai muce Alhmdllhi ala kulli halin.
*_“Sweet girl! Sweet girl!!”_*
Nu'aymah da ke a can backyard tana shanya kayan su Anum data wanke tana mita ta jiyo Yoohan na ƙwala mata kiran mafarauta. Kanta ta dafe dan ta tabbatar su Anum ne suka hanashi barci. Dawowarsa kenan babu jimawa daga asibiti a gajiye matuƙa. Sabodama kar yaran su gansa su hanashi hutawa a wajen gate yay fakin, ya shigo gidan a saɗaɗe saima yay sa'a su suna a can garden suna wasa Nu'aymah ta korasu itama ta huta. Shiyyasa itakam batama cika son weekend tai musu a gidanba. Tafi buƙatar su wuce gidan Uncle jay ko gidan Aunty Little ko wajen su maman Destiny.
Jin ya cigaba da ƙwala mata kiran yasa ta ajiye abin matse kayan dake a hannunta ta nufi ciki da sauri. Ilai kuwa samun duk yaran tayi a bedroom ɗinsa ɗane-ɗane bisa gado kusa da shi kowa na ihun sai ya tashi an kaisa gidan Abie (Jay). Kai Nu'aymah ta dafe sannan ta ɗaure fuska ta daka musu tsawa. Tsitt kuwa sukayi kowa na kwaɓe fuska.
Sai a lokacin Yoohan ya janye filon daya cusa kansa a ciki ya tashi zaune, kallon yanda yaran duk suka zuba tagumi yay, ya kuma dubi yanda Nu'aymah tai bala'in tsare gida. Sai shima kawai yay tagumi kamar yanda yaran sukayi ya zuba mata ido. Hararsu tayi su duka ta ida shigowa cikin ɗakin. Da sauri Ibrahim dake da shekaru shida ya matsa jikin Yoohan ya lafe, sai itama Anum dake da uku ta matsa ta lafe. Duk yanda Yoohan yaso daurewa sai ya kasa ya saki ƙaramar dariya yana kama kunnuwansu yaja kaɗan.
“Wato kuɗinnan fa nagama ni kuka raina a gidan nan, ita Mie-mie kuna tsoronta, amma ni kunma maidani Uncle Jay kakanku ko?”.
Yanda yay maganarne ya saka Nu'aymah yin dariya itama, ta yamutsa fuska da faɗin, “Dan ALLAH ka tattarasu ni kama kaisu gidan Miemaa, abar min Deen kawai anan”.
Cikin ɗage gira Yoohan yace, “Oh, saboda kinga yarona mai hakuri kina samin shi aiki ko. To naƙi wayon, waɗanan tom and jerry ɗin zan bar miki anan, Abbana kuwa kano ma zan kaisa yayma Umm Hutu da Uncle Muhammad. Inama yake?”.
“Haba Yah Maleek dan ALLAH kar muyi haka da kai, waɗanan mi suka iya banda takurama mutane”.
“Hhhh kunfi kusa ai. Kai mai jan kunne ina Abbana yake?”. Yoohan ya faɗa dajan kunnen Ibrahim.
Ƙwaɓe fuska yaron yayi yana tashi daga jikinsa ya koma wajen Nu'aymah. “Mie-mie ALLAH nama fasa sayama Dada birthday gift ɗin da nace miki tunda bazai daina cemin maijan kunne ba. Gashi nan har Wannan Anum ɗin ta kama bayan itama jajayen kunnen ne da ita”.
Sosai Yoohan da Nu'aymah suka kwashe da dariya. Cikin dariya Yoohan yace, “A to indai hakane bazan sakeba Abban Mie-mie. Zomu shirya kaji”.
Ɗan jimm yaron yayi, sai kuma ya kalli Aymah. “Mie-mie kin yarda na shirya da shi?”.
“Hhhh haba Abbana wake fushi da babansa dama inba shashasha ba”.
“Ai dama nima bana fushi da shi ko Dada?”.
Yay maganar da matsawa jikin Yoohan dake kallonsu da murmushi. Rungumesa yayi sannan ya dubi Aymah da wani narkakken kallo. “Wai ina Abbana?”.
Miƙewa tai tana bashi amsa. “Yana ɗakinsufa yana gyarawa, dukansa nai shiyyasa yaƙi fitowa, yana can yana faman haɗiyar zuciya uwa budiddigin ƙwaɗo”.
Sakkowa Yoohan yay daga gadon ɗauke da Anuma yana faɗin, Ayyah Mie-Mie mi mukayi haka ne harda taɓa mana lafiyarmu?”.
“Miskilancin da kuka saba mana. Yaron nan a gabansa na gama gohon gyara musu ɗaki wai dan wulaƙanci yana zaune a ɗakin su Anum suka sake hargitsashi bai hanasuba shi shugaban miskilawan Najeriya. Shiyyasa na dakesa dan gobe idan sunyi ai ya hanasu ko”.
“Aiko a kansu zansa ya rama. Abbana kana ina?”.
Kafin Aymah ta bashi amsa Deen ya fito daga ɗakinsu baki cike da iska. Yana ganin Yoohan sai gashi da gudu yazo ya rungume Dadan sa.
Cike da so da ƙauna Yoohan yace, “Oh my sweetheart so sorry yeah. Bar Mie-mie anayin hutu Kano zan kaika wajen Umm da Uncle. Aiko cike da jin daɗi yaron ya hau murna. Yayinda su Ibrahim suka koma jikin Aymah suka lafe wai sunan jealous ya motsa. Dariya Yoohan yayi suma ya miƙa musu ɗayan hannunsa. Da gudu kuwa suka ƙaraso ya haɗasu ya rungume yana maijin farin ciki a ransa da samuwarsu a garesa matsayin ƴaƴa. Waɗanda suka fito daga tsatson Nu'aymahrsa mai rigima da tsiwa. Shikam babu abinda zaicema ALLAH sai godiya kuma, dan ya gama masa dukkan rahama. Ko a musilinci n daya tsunta kansa a ciki bayan dulmiyar da shi da su papa sukayi ai ya gamacin ribar rayuwa. Balle kuma daɗin daɗawa ga ƙyautar mace ta gari da ƴaƴa nutsatstsu da ALLAH ya bashi. Wanda ya tabbatar tarbiyyar mahaifiyarsu ma tana taka rawar gani wajen samuwar tasu. Shiyyasa akace ka nemawa ƴaƴanka uwa ta gari, matama su nemawa ƴaƴansu uba na gari. Fatansa ALLAH ya raya masa su da baiwar ilimin addini tamkar mahaifiyarsu. Duk da shima zuwa yanzun Alhmdllh, ya sauke alkur'ani mai girma haryayi nisama a hadda. Yasan littatafai masu yawa na addini, bai kuma tsaya a hakaba yana cigaba da neman ilimi babu dare babu rana. Dolene ya kasance mai yawan ambaton Alhamdulillahi ala kulli halin a kowanne dakiƙa na rayuwarsa, suka kalli juna shida matarsa suna murmushi, hannu ya miƙa mata itama tazo ta haɗasu ta rungume cike da godiyar UBANGIJI mai rahama mai jinƙai.✍😭🤗👌🏼.
To nima bilyn ku dolene na kasance mai yawaita ambaton ALHAMDULILLAHI ALA LULLIHALIN a kowacce daƙiƙa ta rayuwata.
*_ALLAH na gode maka da dama daka bani da iko kammala wannan littafi, abinda na rubuta dai-dai ALLAH ya bamu ladar amfanuwa da shi da ikonsa. Wanda nayi kuskure ALLAH ya yafe mana ni da ku masu karantawa. Ina fatan zakuyi watsi da duk abinda bai kasance mai amfaniba sai dan ƙayatar da jin daɗin karatunku. Duk wanda na ɓatama rai a lokacin rubuta wannan littafi ya gafarceni. ALLAH ya haɗamu a gaba da alkairi😭🙏🏻🤗💋._*
*_ZAFAFA BIYAR na sake miƙa ɗumbin godiyarsu a gareku. Mun gode da ƙauna da kuka nuna mana, ALLAH ya bar zuminci ya cigaba da bamu ikon sauke haƙƙin junanmu. Muna fatan zaku sake kasancewa cikin shirin zuwan ZAFAFA BIYAR NEXT LEVEL insha ALLAH anan gaba kaɗan. Mun gode, mun gode, mun gode💋💋💋💋💋🤗🙏🏻😭_*
Harna fara kewarku silly guys😹😂🤣😫⛹🏻♀️⛹🏻♀️⛹🏻♀️😭🙏🏻
Leave a Comment