Tayi Min Kankanta Complete Hausa Novel

 


*TAYI MIN ƘANƘANTA*

🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀🎀

*Zahra Surbajo*

*Sadaukarwa ga Ahalin Sharoo Gambo Yako,mazan su da matansu,alherin Allah

yakai muku a duk inda kuke,nayi tawassali ga Annabi Muhammadu (SAW),Allah kai ruƙo da hannayena dan alfarmar ahalin manzon Allah (SAW)*


_Bissimillahirrahmanir raheem_


_wannan littafin nawa ƙirƙirarsa nayi banyishi dan wani ko wata ba,duk abinda kaga yayi dede da rayuwarka arashine_


_wannan daban yake da sauran,salonsa na dabanne,akwai abun dariya,zazzafar soyayya,tausayi,ƙiyayya,da ɗumbin danasani,karku bari abaku labari,kubishi sannu a hankali dan kwashe darasin dayake tafe dashi_


_surbajon ce de har yanzu,salo da basirar duk nata ne,nice da kaina ba saƙo ba,ga me_


*Ummu Aymana*

*Surbajo*

*Kano to jiddah*

*Karen bana*

*Sanadin kidnapping*

*Ɗan karuwa*

*Cin Amana Ko Fansa*

*Giɗaɗo ba Shege Bane*

*Allah Gatan Bawa*

*Ƴar Bautar Ƙasa*

*Aure Da Haihuwa*

Da de sauransu.ku kasance da wannan banufiya domin ci gaba da samun nishaɗi.😍



*1*




"Zahra'u ya kamata ki fito haka fa kizo ku wuce,tun ɗazu su hanne ke tsaye suna jiranki,bana son sakarcin banza fa"cewar wata dattijuya dake zaune kan kujerar zaman tsakar gida tana ɗaure nono a ledar siga.


Daga can cikin bukkar dake kusa da dattijuwar wacce aka kira da Zahra'u tace "Inna do Allah Do Annabijjo,ki barni in sa jambakina cikin kwanciyar hankali,ke bakisan in bakayi kwalliya ba ko kallonka ba'a yi?"


"aykin kawai,yo tun bara kike sa jambakin amma har yanzu ba mashinshini,se asarar kuɗin siya miki da nike yi"cewar inna daga wajen da take zaune.


Fitowa tayi daga cikin bukkar tana gyara ɗamarar da ta ɗaura a ƙugunta,ko ina a fuskarta kwallliyace irin ta fulani.

Laɓɓanta shafe  cikin jan janbaki,yarinyace da bata wuce shekaru goma sha biyar ba.


"kede Inna kinada matsala,bakin ki be taɓa faɗin alkha'iri,se sharri,ni ɗoramin mu tafi"ta ƙarasa maganar cikin turo ɗan ƙaramin bakinta gaba.


Gammo ta ɗora sannan ta ɗora mata kwaryar nonon akanta,ta miƙa mata ledar viva da aka sa ludaya da ƙorai aciki,ta juya gun su Hanne dake tsaye zaman jiranta tayi murmushi kumatunta suka lotsa,siririyar hushiryarta ta bayyana atsakanin fararen haƙoranta masu kyan tsari,tace "na ɓata muku lokaci kuyi haƙuri,mu tafi kar mu sake ɓata wani lokacin"


Murmushi sukai mata,sannan suka rankaya suka fice bayan sunyiwa inna sallama.


Tafe suke suna hirar su ta yau da kullum,ɗaya daga cikinsu Me suna haule tace"wai duk ƙawancen nan namu muna aure inba riga ɗaya muke ba se ya ragu ko?"


 Dariya Zahra'u tayi sannan tace,"Allah ya kyauta,ni aradu ko birnin sin naje aure bazan dena ƙawance daku ba,bare ma dukanmu muna ruga ɗaya ba inda zamu"


Hanne ce ta amshe zancen da cewa"ni Auran ma tsoro yake ban,kunga de Ma'u kamar abun arxiƙi Rabi'u ya Aureta amma ku dubi wulaƙancin da yake mata yanzu"


"shiyasa na shiga makaranta dan bazan yarda namiji yamin wulaƙanci ba,"cewar Zahra'u tana murmushi.



Da wannan hirar tasu suka ƙarasa fitowa daga cikin dajin falgore inda rugarsu take,suka miƙo tsawon titin zuwa inda barikin sojojin dake cikin dajin yake,sabida ankawo sababbin sojojin da ake ba training gurin acike yake da mutane kamar kasuwa,dan motocima in sun zo gurin da ƙyar suke wucewa sabida yawan sojojin.


Basu jima da zuwa ba kowa kayanta ya ƙare sabida ƙarancin abincin gurin,a hannu a hannu ake siyan duk wani abun ci na gurin.


gurin me saida burodi suka ƙarasa kowa ta sayi guda ɗaya sannan suka juya cike da farincikin sun sayi burodin da zasu ci yau agurin alibidin sunan Zina,wata ƙawarsu data haihu.


Karo suka ci da wani matashi sanye da wandon sojoji,hannunsa riƙe da bindiga,se riga tshits army green da hular sojoji,ba laifi kyakkyawane,raɓewa sukayi zasu wuce ta gefenshi yayi sauri yasha gabansu yace yana murmushi,


"don Allah kuyi haƙuri mu baƙi ne anan,kuma abinci mukeso mu ci,isowar mu kenan daga Abuja,amma mun rasa" 


Harara Zahra'u ta galla masa sannan tace"amma dan baƙin hali ay kuna gani muka kawo tallan nono, in yunwar kukeji me ya hanaki siya?"


Murmushi yayi dan ya fahimci yarinyar akwai tsiwa,cikin taushin murya yace"Bamu lura bane ƙanwata,ayi haƙuri"



"to yanzu me kukeso muyi muku,tunda mude ba abinci bane bare ku cinyemu"cewar Zahra'u batare da tsoron komai ba,dan ita ba ƙaramin abu bane ke firgitata.


"in anan kuke don Allah ku taimaka mana, kuɗin cefane zamu baku ku dafo mana abincin ku kawo mana nida abokina,"


Shuru sukayi sannan hanne tace"gaskiya rigarmu da nisa nide bazan iya zuwa gida in dawo ba"


"yo inba wahalalle ba waye zeje gida yadawo nan"cewar haule.


"don Allah ku taimaka abokina yanada lalurar gyambom ciki be jure yunwa don Allah ku taimaka ku yi mana kamin yafara jin yunwa wallahi zamu biyaku ladan yi"cewar matashin kamar zeyi kuka.


Zahrau tsintar kanta tayi da tausayawa abokin nasa,sabida itama tana da lalurar gyambom cikin tasan azabar ziwon,dan haka tsintar kanta tayi da cewa


"kawo kuɗin,zan dafo muku,sede muna da nisa zaku iya jira?"

Da sauri matashin ya gyaɗa mata kai,sabida tun ɗazu yake neman wanda ze dafo musun amma be samu ba,ga abokin nashi shegen taurim kai shiba jure yunwa ba amma ko ze mutu baze ci abincin siyarwa ba,shiyasa duk yabi ya damu.


Hannu yasa a aljihu ya ɗebo kuɗin dashi kanshi besan adadinsu ba yabata,juya kuɗin take a hannunta tana mamaki,amma batace komai ba ta ɗauka da yawa suke so, dan haka ce mishi tayi"zan kawo ma insha Allahu ka tsaya a bakin titi de inda zan ganka da wuri"


Godiya yay mata sosai sannan yace"mu haɗu kawai anan,zefi sauƙi,sunana Capt Jameel Ahmad zan jiraki anan"



Bata ce komai ba suka juya suka wuce ita da ƙawayen nata,wanda gaba ɗaya haushinta sukeji,cikin fushi hanne tace.

"nufinki de bazaki gidan sunan ba ko?shiyasa kika amshi girkin gardawan da baki sani ba"


Batare da damuwar komai ba aranta tace"dan bakusan ciwon ulcer bane da kuma kun tausaya kun musu,nide zan musu sabida Allah".tana kaiwa nan tai gaba ta ƙyalesu a baya.


No comments

Powered by Blogger.