X World 6
***MAMANTEDDY***A
#Duniyar shahara# X World...**
Ba tare da Adnan yayi Wani tunani ba ko game da Aneesa Ko yaya zata kalli Al'amarin abun ka ga kaifi Ɗaya shi daman haka yake Wannan yasa Shi nufar Gidan shi kai tsaye
,hankalin sa a tashe don da fari yayi tunanin kaita Asibiti dake kusa amma tuno da Waye shi ,kuma Waye mahaifin sa a idanun mutane ,da kuma sanin sharrin mutanen Wannan zamani , abu fari ne Amma a nan take su mayar dashi bakin ƙirin da bakunan su yasa Adnan janyewa yana nufar Gidan sa kai tsaye . A zuciyar sa cewa yake yi " Wannan Wacce irin Yarinya ce ? , Sai Tsiwa da ƙiriniya amma kawai Dan Punishment da aka bata wai ta sume tana shirin mutuwa masu . Ƙara Gudun motan sa yayi yana tsayawa a dai dai Gidan sa inda masu Gadi Na Hango motan sa suka yi Saurin Wangale masa Katafaren Gate ɗin Gidan . Da Sauri ya shigar da Moton sa yana nufar parking space Wanda bai gama tsayar da motan mazaunin ta ba ya fito da Sauri yana kai hannun sa tare da Buɗe back Seat yana Ɗauko Zahra da hannun sa cak yayi sama da ita Kaman yar tsana . Yanda yaga ta sanƙare yasa shi tsorata Addu'oi yake a zuciyar sa amma a fuskar sa ba zaka ce ga damuwa ba ,don zaka rantse bai damu ba ko irin a damuwar sa . Juyawa yayi tare da kallon Wani Security yana cewa " Musa koma ka gyara mun parking din moton can . Ok Sir . Musa ya furta tare da Juyawa cikin Sauri yana nufar moton . Kai tsaye Adnan Falon Aneesa ya nufo yana Murɗa Handle Door tare da kutsa kan sa Izuwa Falon .**
Ɓangaren Zainabu kuwa A can Barikin Sojoji ihu take yi tana Ƙarawa tare da ƙirar Sunan Aminiyar nata Zahra . Don Allah Yallaɓai ku taimake Ni kar ku kashe mun Ƙawata Zahra . Ba tayi komai ba , taimako muka fito yi ba Wani Abu ba . Ga Wanda ya cancanci Kashewa can Ɗan me kunu Amma ba Ƙawata ba ,mu babu Ruwan da Wani Sarauta da zai Amsa amma talaka ne bashi da Wani kuɗi sai lalata Yara da ya iya ,kuma Ni ban san Ƙawata Wannan ne Hujjar da zata bada ba , da nayi mata bayani akan komai tun da Ita bata Sani bane . A duk tunani na Hujjar da take magana ta kama shi da masu sayar da Lemu ne ta Ɗauke su Hoto zata kai ma manya,ban san a iyaka nan Hujjar nata ya ƙare ba." Kallon Ta Shureim yayi Wanda tun da take zancen bai ce mata uhm uhm'uhm ba har ta dakata . Idanun ta ya kalla anan ya fahimci Ita tafi Zahara Wayo dama Shekaru , Ita kawai Zahra ƙiriniya ne da Tsiwa yayi mata yawa . Murmushi yayi mata ,wanda sai da Kirjin Zainabu ya buga dam. Don da Wannan murmushin nasa dama baiyi ba don da yayi Murmushin da Basawa yayi mata kama . Ki kwantar da Hankalin ki Ƙawarki tana cikin koshin lafiya , Adnaan zai dawo da ita nan ba da jimawa ba .
Shiru Zainabu tayi tana tunanin magannn tasa tare da tunanin Naɗar Muryar Da Zahra tayo wai wannan Shashancin ne Hujjar su , a cewan Zainabu don ita sam bata san Zahra Haka take ba sai a yau .Tuno da Halin da Inna Salame zata shiga a halin yanzu ,da kuma dadin da su Talatu zasu ji yasa ta Cigaba da tsiyayar da ƙwallah daga Idanun ta . Tabbas dana sani ƙyaya da nasan Wannan Al'amarin haka zai kasance da ban zo mata da wannan maganan ba . Yanzu ko labari aka ji Mun shigo barikin Sojoji to sunan mu fa watsatstsu . Ya Salam..! Shine Kalmar da ta furta tana yin ƙasa da kan ta . Shureim ne ya kalli sojojin dake bayan sa yana basu Umarnin su dawo da ita Inuwa .
**
Jin kiran Sallahn Malam me Unguwa na ƙarfe Hudu wato la'asar yasa Hankalin Malam da Inna Tashi maƙura . Don Inna yau sam ta kasa sayar da Amincin nata ma baki Ɗaya . Rabi ce ta taya ta Sayarwa ita ta amshi Ragamar sayar da Abincin . Talatu kuwa tun Wancen maganan da ta gama yadawa har yanzu ba ta ƙara magana ko taji halin da ake ciki ba . Hankalin Inna a tashe ta saka Mayafin ta tana shirin fitowa daga Zauren gidan ne suka haɗu da Hadiza Mahaifiyar Zainabu wacce idanun ta suka yi dulu² . Alamu tayi kuka har ta Gode ma Allah .kallon Inna tayi babu mutunci take fadin" Wallahi nayi nadamar barin Zainabu tana rayuwa da Yar ki Bara ji da Tarbiyya . Ina Danasani Wallahi daga yau na raba Zainab da Yar ki Zahra har Abada babu ita babu Ƴa ta .
Cikin Sanyin Murya Inna ta furta ' Kiyi Haƙuri Hadiza Laifin nawa ne dana barsu suka fita ,amma ki daina faɗin haka inshallah zasu dawo babu Abin da zai same su . Kallon Inna Hadiza tayi tana faɗin " Ai dawowa ya zama dole su dawo , dama ba cewa nayi sun ɓata ba , kawai Abin da nace ɗaya ne shine Na yanke duk wata Alaqa tsakin Zainabu da Zahra . Ki ja ma yar ki kunne. Da kike maganan zasu dawo yo idan ma basu dawo ba aike ce cikin matsala Don Wallahi sai nasa an daure ki har Igiya tayi Rara . Aikin banza aikin wofi , Aure nake so Ɗiyata tayi kuma indai tana tare da Zahra baza tayi ba wannan yasa na yanke Hukuncin komai .ke da kike son Ganin yar a gaban ki ai sai kiyi ta barin ta . In yaso ki tsuma ta ki sha ."
Tana kare maganan tare da juyawa a fusace tana shirin barin Zauren Gidan . Hummm Jan numfashi Inna tayi mai karfi mai tattare da damuwa . Rabi ne ta leko tana cewa " Inna Wai wacce Ce take Wannan maganan tamkar bata san Ƙaddara ba . Tsakanin Zahra da Zainabu babu Wanda bashi da kalon nashi Rashin jin ,amma kawai akan yar ki ki taho kina faɗa mawa Mata magana marasa Dadi.? Shin yar Kice kadai ba'a gani ba ko har da ita nata Yar . ? . Au Ashe dama bakin Gidan naku speaker tana nan .? To fitowa zakiyi ko Nine zan biyo ki sai mu gwangwaje .
Kayya".
Inna Salame ta furta tare da fadin " A'a Rabi kar ki fito dakata daganan don Allah ki koma . Zuciyar Rabi na zafi tamkar zai fito ya tsarwatse yayin da Talatu ke Ɗaki abun tana ararrewa da Yaran ta . Ya Adam ne ya shigo Soron yana ganin Abin dake Faruwa ya furta " Meye Wannan kuma, meke Faruwa ne?. Wani kallo Hadiza ta Watsa masa tana juyawa tare da ida barin Zauren . Girgiza Kai Inna tayi tana faɗin " Adam har yanzu babu Wani labari ko..? Inna Ki kwantar da Hankalin ki don Allah kar maganan kowa ya tada Miki da Hankali Zahra zasu dawo .
Adam zasu dawo tun tuni basu dawo ba .? Kama ta Yayi tare da cewa " Inna kiyi Haƙuri ina ji a jiki na komai lafiya . Rabi kama Inna ku shiga daga ciki kar a kara barin ta ,ta fito don Allah . Tahowa Rabi tayi tana kamata tare da cewa" Inna Kiyi Haƙuri kar Wannan ya tada Miki da Hankali mu koma Gida ."
**
Turus Aneesa tayi tana kallon Adnaan da Yarinyar dake Hannun sa baƙuwar Fuska wacce bata santa ba . A 2 str ya kwantar da Zahra yana kallon Aneesa wacce suna Haɗa ido cike da masifa da bakin kishi ta fara tuhumar sa ." Half World Ina ka samu Wannan yarinyar ? Wacece ita ? Me kakawo ta gida na tayi?. Kan Zahra ya gyara yana kallon Neesa tare da cewa " Aneesa kiyi gaggawar ceto mun Rayuwar ta yana da muhimmanci sosai a halin yanzu .
Allah sarki.!
Aikin banza , Sannu Adnan yanzu Lalatan naka ya kai har ga yara under 18? Na shiga Uku Ni Neesaa , Adnaan me na rage ka dashi ? Meye ban maka taste dina ne bai maka ba ko mene? Wallahi ba zan ceto Rayuwar ta ba , kayi mata fyaɗe kazo kana cewa na ceto rayuwar ta?. To a yanda ka kawo ta a haka zata mutu ka ɗauke ta ka kaita inda zaka kai ta . Cikin miskilalalliyar Muryar sa ya furta " Aneesa me kike nufi.?
Au baka fahimta abun da nake nufi ba? A matsayin ka na Soja Tayaya kuke kama tsagera a jeji? Baka fahimta ba har yanzu . To ina nufin nice kadai matar Adnaan duniya da Lahira babu kofa babu hanyar shigowar ko wacce mace cikin rayuwata dana miji na . Idan kana ma wannan tunanin to kar ka fara kar kuma ka soma ina nufin kaa dakata da yin wannan Shashancin . Wani irin zafi zuciyar sa ke masa . Oho saboda taga Gadon barcin sa shine yau har take da zarrar masa wannan Magannn.? Tunanin hakan yake yi a zuciya kamin ya furta " Ni kike faɗa mawa Haƙa Aneesa .? Kawai sai taga ya taka da ƙafafun sa yana barin falon tare da nufa rest Room ɗin shi . Tsayawa Aneesa tayi tana jin zafi tare da bakin ciki a duk lokacin da ta kalli fuskar Zahra . Fashewa da Kuka tayi tana faɗin " Ina zai Soni ko yyi rawar jiki a kaina bayan yana Sex da Yara Yan under 18 Wanda suka fini...maganan ta ne ya maƙale sakamakon Ganin sa da tayi ta fito daga Shi sai boxer Gajeren Wandon sa na Soja , Da farar t.shirt na shan iska . Hannun sa Riƙe da Karar Sigari yana buƙawa tare da fidda Hayakin cike da Shahara. Kirjin ta ne ya buga Dammm tabbas tasan Adnaan yana shan Sigari Amma sai yafi Watanni bai sha ba , A kuma fahimtar ta shine Baya sha sai idan yana cikin damuwa ko yana shirin Tanfatsa maka .
Zama yayi a daya daga Kujerun falon yana Cigaba da Shan Sigarin kusan na dakiƙu biyu kana ya kalleta yana furta " Aneesa indai Wani Abu ya sami Wannan yarinyar ki aje shi tamkar Auren ki ne ya samu . Kuma ki sani kyaƙyƙyawar Albishir Ni ba'a mun Gadara don haka Maganan kece dani kadai ya kau ki tada mun ita daga suma kuma ita zan Auro Miki idan tazo ki kashe ta.! Ni Adnaan ba'a yi Wata ya mace da zata faɗa mun magana na saka mata ido ba ,bare ke da kika gama zubda mutuncin ki a duniya. Tarin Zahra ne ya katse su inda take wani tari tamkar Zata bar duniya . A hankali ta ware idanun ta tana kirar sunan Inna tare da fadin " Wayyo Inna Ruwa , Ruwa zan sha zan mutu wayyo ."
Laɓɓan sa na ƙasa Adnaan ya ciza kaɗan tare da yi Ma Aneesa kallon kin san me kuma zai faru next . Ruwan Faro ya bude mata yana zuba mata a wani Glass cup tare da miƙa mata. A hankali Zahra ta buɗe idanun ta tana sauke su akan fuskar Adnaaan . Wani irin uban ihu ta saki mai amsa kuwa tana faɗin " Zai kashe Ni Wayyoo Inna Zai kashe Miki Ni .!
Ɗauke Wuta Aneesa tayi kawai sai ta fashe da kuka tana yin kukan kura tare da cafko Wutar Zahra tana kokarin kai mata Mari . Da miji na kika yi iskanci shegiya yar tallah yar matsiyata watsatstsiya . Juyowa Adnaaan yayi yana kife Aneesa da Wani irin Mari tare da furta " Neesaa....! Yana kirar sunan ta Cikin Muryar sana tijara . Saurin sakin Wuyar Zahra tayi tana nufar under ground room . Kallon Zahra Adnaaan yayi yana cewa " Ga ruwa ki sha , Bara nazo yanzu . Ya ƙare maganan yana cillar da karan Sigarin hannun sa tare da bin bayan Aneesa zuwa Under ground room . Bin bayan su Zahra tayi da kallo tana kai cup din ruwan bakin ta tare da kyankyamewa Tassss. Wuri² tayi tana gano Hanyar fita kawai sai ta juya da gudu tana kokarin barin falon ,juyowa tayi a karo na biyu tana tunanin Wani irin barna zata aika ta masa Wanda ba zai manta da ita ba . Kawai sai ta danga Centre table din Tsakiyar falon tana rotsawa da Ƙasa. Tare da bin wani Glass Door ɗin sa kaman Corridor tana ɗaukar karfen shima tana rotsawa yanda taji karar ya wuce tunanin ta na fashewa yasata Saurin juyawa da gudu tana barin Falon tare da nufar Farfajiyar gidan . Kallo Daya tayi ma sojojin ta furta " Ku buɗe mun gate na fita ." Jin haka yasa su bata hanya tana ficewa .
#X world Duniyar shahara".
Leave a Comment