Yar Aikin karuwai 51-55

 


🌼'YAR AIKIN KARUWAI🌼

    LITTAFIN KYAUTA NE     

                51-55

Official


By

AsmaBaffa

SADAUKARWA NE GA DUKKAN YARAN TSUNTUWA 

Page naki ne

BINTA UMAR ABBALE








       Tunda ya tafi sai da ya kwashe sati uku sannan ban san zai dawo ba Ina kitchen Baba kulu ta tafi gidan Khaleel sai dare tace zata dawo,Ina cikin juya miyar kwan da nakeyi naji knocking gas din na kashe Fitowa nayi tare da bude kofa,kamshi ne na daban ya daki hancina Wanda ba shiri na dago nayi tozali da shi,yayi kyau ya Kara fari sosai dama gashi fari sosai duk haskena ya fini sosai,yayi kyau cikin kana nan kayansa riga farare ba karamin kyau ya zuba ba wandon Jean ne an yanka shi a gwiwa  gaskiya ya tafi da Imani na gashi dan matsashin saurayi,nace oyoyo yaushe ka dawo? Kin kafeni da Ido Kamar baki sanni ba bana son kallo,nace sorry kayi kyau ne sosai,Dadi yaji a ransa dan Kuwa Sabreen da ya dawo ko tace yayi kyau ai gashi ta bariki ta fada Masa,katuwar akwati ce nace yanzu ka dawo ne? yace Kamar wani marar Mata daga dawowata sai na sauka a nan,yana ajiye kayansa a gida ko Zama baiyi ba ya taho gidan Rabiah amma sai yace to tun 2pm Ina garin nan na sauka tuni sai Dana Yi bacci na huta na tashi nayi wanka da Sallah shine Kika ganni 4:50pm nazo,nace to Sannu da zuwa na shiga kitchen na fito da zobon da na hada dazu ya Sha kayan kamshi da abarba da ayaba a ciki in ka tace sai ka ganshi me kauri yayi Dadi matuka na kawo a juck da cup yayi sanyi sosai,na zuba Masa a cup na dauka na Mika Masa ya karba Yana Izza, kitchen na koma na karasa egg source din da nama sai Cous cous da na dafa tuni dama Baba kulu ce tace dan Allah nayi mana,Zubo Masa nayi zan Kai Dining yace ban iya tashi fa malama,gabansa na kawo na ajiye na dakko ruwa Eva,plate da spoon na dawo na zuba masa tare da Mika Masa ya karba yace wannan Yar iskar rigar da kika saka fa anyita doguwa kamar abin kirki tsaga ta gaba har cinya Kamar Yar arna go and change ya furta da tsawa, na kalle shi nace yo mu abin kunya ai gaba muka bashi ba baya ba,zan wuce daki yace dauki akwatinki tsarabarki ce harda na Makkah na hada lokacin Ina sauri ban baki ba,Kuma Allah yasa naga rigata daya a jikin Karuwar kawayenki,Ni dai murna nake Yi na ja akwati na Kai daki na bude Ina ta Shan kallo abina kamar me


    A ciki na dauki wata doguwar riga hadaddiya silver tayi kyau a gurguje nayi wanka nazo na shafa lotion na saka abata na shafa powder da lip gloss pink,gashina na gyara na Masa acuci sai mayafin rigar dama harda dan mayafinta na Dan yada shi a kaina nayi kyau tabi jikina shape Dina ya fito Kamar a sace ni na shafa turaruka na fito,har gama cinye abinsa tasa ya kwanta a kujerar Yana canja channel yaji kamshi na bai ko kalleni ba sai da nayi gyaran murya Ina murmushi dan ya juyo ya ganni ai Kuwa naci sa'a ya juyo ya kalleni kasa dauke Idonsa yayi a kaina,nace nayi kyau ko?kalli duwawuna a ciki gaskiya Wanda ya sameni yayi dace a'a kalli dan Allah ohhhh... baki ya tabe yace ni Zaki nunawa kyau kalleni na fiki kyau to me Zan gani, mikewa yayi zaune Ina so nayi control kaina na daina Kai kaina ga Namiji sai naji na kasa na rasa dalili sai dai naji Kawai naje Kamar ana fisgata.


    Mikewa yayi zaune Yana kamo tashoshi na karasa gabansa na sa yatsana a baki Ina ci Ina kallonsa yace ke kalau kike kuwa,da sauri na zauna Masa a cinya Ido ya runtse sabo da irin abinda yake ji a jikinsa gaba daya loosing control yakeyi sai ya kasa tureni sabo da irin turaren da Muka siyo a wajen Mazarkwaila na shafa dama ta fada Mana tace Namiji bazai so ya bar jikinka ba sabo da dadin kamshinsa,kyaleni yayi yaci gaba da canja channel ya diririce bai San ma Ina yake dannawa ba duk ya gigice hannuna na dora a kan nasa na cire remote din na ajiye gefe na juya na zauna daram muna facing juna nasan Ina magana watakil ya dawo hayyacinsa sai na rungumeshi tare da kwantar da kaina a kirjinsa,Ido ya lumshe nayi Murmushi dariya ta kamani yanda ya rasa inda zai saka Kansa,gemunsa na shafa da hannayena biyu na sauke bakina a nasa na Fara Masa kiss Wanda ke canja Masa tunani sai da ya bari yaji dadinsa sannan naji muryarsa da kyar tana rawa yace ta Allah ba taki ba nafi karfin kissarki shedaniya ya ture ni Saura kadan na Sha kasa na rike kujera da kyar na mike tsaye shima ya mike zai tafi nace I'm sorry sai lokacin naji haushin kaina sosai,yace cikin fushi bani bake tattaro kayanki ki koma inda na dakko ki I hate you,Ido na zaro yace kin ji me nace kije kiyi ta lalacewa tunda haka Kika zaba ni baza ki jefani a masifa ba wallahi ki koma can kici gaba daga inda Kika tsaya,na gaji sai Dora min bacin rai kike yi,baza ki jefani cikin fushin Allah ba ki tattara ki koma,mamaki ya kamani yace daga yau karki sake gobe na ganki a gidan nan, ya ja tsaki Kamar zai tashi sama ya bude kofa sai ga Baba kulu yace yawwa Baba zamanki ya kare tattara kayanki mu tafi,Baba ta kalleni taga na Dora hannaye a kai hawaye suna gangaro min a kumatuna bata ce komai ba tunda tare ta ganmu, Ina kallo ya saka Baba kulu a mota da kayanta Suka tafi ya maidata gidan Khaleel,Ni Kuwa kuka nake wiwi amma dan masifa sai da na ci abincina da ya rage na koshi na wanke komai da Muka bata Ina Yi Ina kuka Ina furta na cuci kaina sai da nabi ko Ina na gyara na rufe na kashe kayan wuta na tattara kayana har tsarabata a akwati biyu manya na jawo su na fito kuka nake sosai Kamar Raina zai fita,na rufe musu kofar gate na mike titi gaf da magriba Ina Jan akwatuna biyu hagu da dama,gashi unguwar ba abun Hawa na haya sai nayi tafiya me nisa Ina tafiya Ina kuka nace Rabi kin jawa kanki mutumin nan ba abinda ya raga miki gashi nan ai,sai da na fita Main road na shiga Napep ya kaini gidanmu na bariki sabo da kade kade da wasanni da nishadi yasa na Dan ji sanyi na goge hawayena na saita kaina kowa ya fito ga miracle sai yanzu ogan naki ya barki nace ae Ina dariyar yake,sai ga Yar zabil ta fito daga ita sai half vest da dogon tight wando tace Wai kice shegiyar sai yau Kika Gama Masa kwanakin ahh wannan ya daki harka,nace kin Sanni ai bama cin Kan jaki  tace for sure na true sis,nace Ina Sera? She dey inside na wuce sai rungumeni kowa yake har Yan daudu rungumewa mukeyi da su,Santana na rungume yace ahh ji kamshi kekam Karuwanci ya taimakeki,dukkan Yan gidan tunaninsu Ina yin sex Nima tunda bana cewa bana yi har Sera bata sani ba


    Ina shiga dakinmu Seraline ta ganni na shigo da akwatuna na fada saman katifa na fashe da kuka me tsuma zuciya,kallo na tayi tana mamaki sigarin da take Sha ta kashe tace lafiya fada min menene? nace cikin kuka Sera korata yayi Wai karuwa ce ni Kuma Ina sonsa da gaske wallahi na sake fashewa da kuka,Sera ta fashe da dariya tace heyyyyy Hajiyar love me na fada miki,me na fada Miki karuwa bata aure ko kinyi baki Zama lafiya Sabo da zarginki zai ta Yi,danginsa baza su taba sonki ba,kowa zai kyamaceki ko da kin shiryu baza a fahimci hakan ba,rayuwar mu ba Daya bace data kowa bamu da kunya bamu da tarbiya,Kuma daga Namiji ya Gama cinyeki karshe korarki zaiyi karya yake ba son Allah yake Miki ba,gashi kin kashe abinda Kika tara a gidan marayu sai kiyi hakuri a sake sabon lale karki Manta karuwa bata taimako abincina bazan baki ba so kin Saba dare yayi tunda ke kullum tasallah ce sarkin Sallah sai kiyi Sallah a fara Shirin fita Neman customers,nace bazan iya fita ba ni in Banda tunaninsa babu abinda Zan iya hasalawa,kin San Allah ba Wasa nake ba abincina baki ci jiya Kika ce min dubu biyu gareki,nace yanzu ma Saura dari biyar Sera tace to gwara ki tashi.


    Ba yanda na iya tashi nayi bayan munyi wanka nayi sallar Isha nayi adduoi nace Allah ka daidaita tsakanina da Nawwar ka sa Masa salama a zuciyarsa,shiri nayi sosai na saka guntun Bumshort da riga me dogon Hannu me santsi gabanta da botin Fara da zanen fulawa baki,wandon Kuma Baki,takalmi da jaka bakake na saka hular gashi na me tsada Dana barsu a dakinmu,Muka shirya tsaf 11:30pm Muka fita,na tsaya a cikinmu gamu nan reras damu Mata iri iri daasu kyau da munana ana ta dauka,Ni Kuwa na tsaya a wajen kamar gunki Ina tunanin Nawwar,Seraline ce ta daki kafada tace love no dey tire you? Haba ki saki ranki fa Hmmm, hayyacina na dawo na daga hannu Ina cewa customer,Nyash dey,big breast dey, duwawu for sale,local government for sale,come with your cash hot lady dey,Su Seraline duk sun samu customers Ni Kuwa na gaji na tsuguna a wajen na hada Kai da gwiwa na saki kuka,sauran matan ko wacce ta tabe baki basu kulani ba,mota ce ta tsaya a gabana fyalleliyar da ban taba gani ba na mike wani dattijo me Kamala ya sauke glass yace shigo,kallonsa nake Yi kamar na sanshi,yace Yan Mata kinyi min,nace Alhaji dama harda irinku Kuna lekowa nan? Yace jefi jefi mukan zo,a tsorace na bude gaban mota na shiga,yaja muka tafi,Yana kallon cinyoyina Yana lashe baki,Hannu ya Kai zai shafa na rike hannunsa da sauri,na bata rai,yace lafiya? nace farashi na da tsada,yace Nawa kike? Nace na Kai million daya, na baka kaina saida million idan baza ka iya ba saukeni,Alhaji ya kyakyace da dariya yace na Kara Miki 2million nace good Man,har ga Allah tsoro nake ji sabo da ban taba yi ba,ganin haka sabo da ya sauke ni  sai ka Kara min million daya,yace an gama ai kin min ni ko nawa ne Zan biyaki Yana dariya, wani rantsatsen hotel ya kaini cikin lafiyayyen daki, Ina zaune nayi tsuru tsuru Nawwar Kawai nake tunani jira nake yi na gudu


   Muryarsa na tsinta yace bari nayi wanka ko nace to,wayarsa ce tayi Kara ya daga da sauri naji yace sorry zanyi waya da Dana,karaf naji yace Nawwar wallahi kaji na rantse idan har ka sake dukan Sabreen sai na tsine maka,akan Kawai ta sake daukan kudinka tayi cefane,baka bata ne shi yasa,Nawwar yace yanzu Baffa ta daukar min 2million ban sani ba dollars Dina fa ta kwashe tasan na mene,to kaji me nace kayi hakuri akan million biyu sai na biyaka tsiyarka banza sakarai ya kashe wayar,gaba daya zufa ce ta lullubeni duk kuwa da ac din dake dakin,naji har muryar Nawwar a waya wallahi shine,Baffa ya shige wanka bai kula da halin da nake ciki ba,Yana shiga na tashi na dauki jakata na lallaba na bar dakin a hankali a nutse Kar ace wani abu nayi na rashin gaskiya na bar hotel din da sauri Ina barin hotel din na shiga taxi sai gida.


    Baffa Kuwa Fitowa yayi tsirara haihuwar uwarsa Yana cewa Baby na fito yaga wayam ya duba ba kowa bakin ciki ya Kama shi yace ya zata min haka gashi yau bazan iya jurewa ba ga Amaryata bata nan,akan ya kusanci Mami gwara ya nemi karuwa dama haka yake Yi mutum ne me tsananin sha'awa da bukata ko yaushe baya iya jurewa ko kadan,haka ya rasa ya zaiyi sai waya ya bugawa tsohuwar karuwarsa Star,tabbas Star ta gidanmu ya Kira tasan akwai kudi ai da gudu ta bar motar Wanda ya dauketa tace a gida ake nemanta ta tafi wajen Baffa a hotel din Dana bari tirr da masu Hali irin na Baffa na dawo gida na kwanta Ina ta mamaki amma ya damu sai na bar gidan dansa ashe shima dan hannu ne.


    Ina kwance a dakinmu nayi lamo abin duniya ya min zafi Banda tunanin Nawwar ba abinda nakeyi na kwanta Ina ta sharbar kuka,kofa naji anyi knocking sai ga Malika ta leko tace kunyi bako gashi zai shigo Kawai naga Nawwar ya shugo,kaina na maida saman katifa naci gaba da kukana,Murmushi yayi yace to kukan fa? Nayi masa banza,baza ki kulani ba,yace bari na bar Miki dakinki,da sauri na dago Ina hawaye nace ba...ba...bakina nane ya jawo min,da me? da nayi maka kiss,dama kace na daina na daina naki ji Ni ban San me yasa nake maka ba,na daina kaji kayi hakuri na fada cikin kuka,Bai ce komai ba na sake cewa ka yafe min na fashe da kuka tare da tashi na rungume shi ta baya,yace wayyo Allah ya rintse Ido da karfi ya furta zata kasheni a ransa a fili yace yanzu fa Kika ce kin daina a haka zan yafe miki,jikina na janye da sauri ya juyo muna facing juna yace fada min Rannan da bana nan Ina Kika je min da mota Kika Yi kwana biyu?


     Hannuna na yarfe Kamar wacce ta Kama wuta a hannun nace baza ka min fada ba? Yace yeah,nace karya Muka yi da motar Muka je kauyen Kano can inda na girma,Ido ya zaro yace Kano a mota? Nace ae Ina murmushi,kin iya mota dama nace kaji ka Ina Yar bariki ai mu komai mun iya ko Dan karya,ai mu Yan karya ne,In fada maka a motar Wise Muka koya itace ta koya min,da Seraline Muka je,Muka Yi dinkuna masu tsada kala uku,Muka tafi Kano Saurayin Sera ya Kama mana dakuna biyu ni Daya na kwana ita Kuma tare suka kwana,ya ganni yace Nima Yana ciki Wai ta bashi ni ya shiga local government dina zai biya Mata Makkah,Dan majalisa ne amma nace idan taje Makkah da kudin bariki to ba lada,tace ai Dan tayi show zata je tayi pic ta saka a media,in fada maka da Yamma na Kai mota wajen wanki taci wanka na Sha shaddar nan ka ganni kamar Yar gomna wanka ya Kai wanka, nace dole muyiwa maza kwalele masu zaman banza,a birnin nan Muka dinga burga da motar nan naci glass munyi pics a iPhone din Sera Zan tura maka kaga wankan ko Kai wallahi sai kace Excellent, Muka dinga bi majalisa Muna dan yin parking mu fito mu dan shiga shago muyi Yar siyayya mu fito,kaga idon maza duk an zanci yaran masu Hannu da shuni ne basu San da zasu ji tarihinmu to wallahi jefe mu ya kamata yayi,dariya ta Kama Nawwar Jin shirme Muka tafi Muka yi,Ina bashi labari nima Ina dariya cinyarsa na dakawa duka Kamar kawata mace Ina cewa sai da Muka girgiza maza masu zaman banza sannan Muka nufi kauyen,wayyo na saka hannuna na sakalo ta wuyansa nace zo kaga Rabi a Kauye ta waye dariya Nawwar ya saki ba shiri nima nayi dariya tare da dan dukan cinyarsa kadan da sauri nace sorry Ina dariya Ina sake dukan cinyarsa kadan Kamar dai yanda akeyi da kawa mace,yace to Ina ji nace haba na dinga fyalla Naira Ina yiwa Dagaci da su Gwaggo kwalele,Kuma nace Ina nan sai nayiwa Dagaci fidiyar dan akuya sai na koma Zan fita da fitata.


     Kudin da ka bani na cefane naje nayi karyata a Kauye Dagaci ya turo su Gwaggo suzo suga yanda na koma a gabansu ko kallonsu banyi ba ban ma nuna na sansu ba,nan dai na bawa Nawwar labarin komai har zuwan mu gidan marayu nace Naga Yan Uwana na fada Masa abinda Muka siya Muka kai,Yana Gama ji yace uhm ta wani bangaren kunyi dai dai ta wani bangaren Kuma Baku yi ba me yasa kuka je kauyen? nace karya ta kaimu,yace ai zarginku za ayi Kuna karuwanci za ace zaman kanku kuke yi tunda an San ba miji ne gareku ba,nace ai basuyi karya ba,mu abin kunya baya Muka bashi ba gaba ba,ransa ya bata sosai ba Wasa yace yanzu kaf kudinki sun Kare? Nace ae yace good  tunda a gidan marayu Kika karar ko ba komai kinyi abin kirki,kayi hakuri abinda nake maka ban San Sanda nake Yi ba sai naji kamar ana ja na,ya sake daure fuska yace kina so na hakura? da sauri nace ae,yace ki min alkwari duk abinda nace Zaki Yi babu musu Kuma dole kiyi,nace nayi Alkawari,yace in na furta ba musu ya Zama Dole,nace komai na yarda Indai zaka hakura,yace Marry me,Ina ji na furta kace me? Nace ki aureni,ji nayi kamar ya zuba min wuta a jikina ni bana son zancen aure a duniya sai naji tsananin damuwa daga lokacin na rasa farin ciki,nace ai ban San aure zaka ce ba ni bana son aure ko mene na yarda zan baka a duniya banda aure,taya Zan taima miki taya Zan zauna dake babu aure kina rungumeni kina min kiss ba aure tsakaninmu idan munyi aure Kuwa babu damuwa sannan ni karki tunanin sonki nake bazan taba iya rayuwar aure da karuwa ba,bazan iya saduwa da Karuwa ba inda maza da yawa Suka Shiga ba bazan iya Kai kaina nan ba,sannan magana ta Allah zai wahala na yarda da Yar bariki ko yaushe Ina zarginta,Kawai Ina so ne ki taimaka min kawai na karya dokar gidanmu daga kaina a daina auren dangi auren dole shike nan in kin min haka muka dan zauna komai yayi settling Zan iya sakinki in kina so,sabo da haka ko kin aureni ba sex ba feeling karki ji komai a kaina so ko wani sex bana so kisa a ranki babu wannan Kawai ga abinda nake so ki yarda ki bada Amanna na aureki shike nan


     Sai lokacin naji sanyi a raina nace tunda ba Zama zanyi ba ai da sauki,yace Kuma sai kinbi dokar aure abinda Allah yace kin nutsu,sannan auren nan yaki ne sosai kafin ma Baffa ya amince ayi shi,nace Baffa ne matsalar auren? Yace kwarai sai kinyi hakuri,Murmushi nayi nace wallahi yafi komai sauki Kuwa karka damu ka kwantar da hankalinka kaje gobe direct kace aure zaka kara idan ka fada masa Kawai ka kirani ka sanar dani, dariya yayi ya zaci shirme na ne a ransa yace wannan bata san waye Baffa ba,ai shi baya Wasa da kowa baida lokacin kowa ma daga aiki sai amaryarsa,a Raina ni kuma nace oh Namiji ba a mallakarsa dole ta wani bangaren Amaryarsa ta mallake Baffa akan Mami ta Zama ita ce on top amma bata mallake shi akan karuwai ba,ta zaci ita daya ce,ta hanashi kula matarsa ta sunna amma gashi Yana bin na banza,yace kin amince? Nace tabbas Ina da waliyyina a Kauye can kano, Kawai ka shirya ka fada Masa sannan ka sanar min,yace mun shirya to,Murmushi nayi yace wannan Yan iskan kayan da Kika saka fa? Nace shakatawa nake kafin na koma prison gidanka,yace bikin nan fa bazai wuce nan da sati biyu ko Uku ba Kawai ku shirya abinda zaku shirya ku fada min Baffa ko ya yarda ko bai yarda ba za a daura bai sani ba,nace karka damu da Kansa zai karbi aurenka,duk Wasa yake gani,skert na dora a saman wandon Nawa na rako shi har jikin wata motarsa red, kudi ya dakko 50k ya bani yace kudin abinci na sanki da shegen zuwa Saloon,nace to ya zaka Yi ka hadu da Yar duniya Yar bariki Local government guda muke siyarwa fa,yace jeki ni kudin na rike Ina fifita da su Ina ce masa Saurayina Dan dolo ya bada kudi ko nono bai tabawa ehhh ehhh ahhh nabi wani kida dake tashi a layin Kamar zai fasa dodon kunne da kyar ake Jin magana,na koma gaban motar Nawwar na dinga karkada masa mazaunai ina fifita da kudin,naki matsa Masa yayi reverse ya fita a haka ya bar layin,Malika ce tazo ta dana min duka ta Kara gaba dariya nayi nace yanci dadi, Santana yace kekam Karuwanci ya taimakeki kinfi kowa sa'a a gidan nan har yaushe Kika Zo garin nan da tsumman kayanki kina warin Kauye Wai gashi kinfi kowa samun me kudi kowa yazo neman ki sai me kudi Kuma sai kinwa kowa yanga,nace haka lamarin Allah yake wani baya sonka ya jefar da Kai wani sai yayi kuka akanka na wuce daki na kwanta sai bacci.


     Amarya Gaji Kuwa amarci Kawai suke Sha da Danbinni,angon bata wani so da kaunarta yake yi Yana Jin bazai iya rabuwa da Gaji ba,itama ta dan hakura ganin yanda yake bata kulawa,Zayya Kakarta da kanta tazo gidan ta kwantar Mata da hankali tace ba a kishi da fada baza kici nasara ba ai kwantar da Kai Zaki ki dinga hada Mata tsiya ta karkashin kasa cikin tuggu,sannan sai a hada da malamai ayi Mata Wanda zata bar gidan nan ai baza mu taba Zama ba baza mu barta ba Amma karki sake takalarta da fada ko ta kulaki da fadan ki maida abin Wasa zata ci ubanta,Zayya taji dadi tun daga ranar Gaji ta samu lafiya da Zayya ta zaci ta hakura,shima Danbinni haka har Yana murna, Kakar Zayya Kuma wani rubutu ta kawo wa Zayya a boye tace gashi kin ganshi sai kinyi wanka Zaki shafe jikinki da shi ki tabbatar ranar ya sadu dake in kinyi shike nan ita da miji shike nan,Gaji Kuwa washe gari Mairo tazo wani abin Hannu Kamar awarwaro na guru tace gashi inji Baba yace a hannunki Zaki daura babu ke babu masu tsafi ko me kishiya zata Miki a banza,yace karki Wasa da shi sai da ya siyar da gonarsa ya iya karbo shi tsada gare shi kusan dubu dari biyu ya kaiwa Malam sai da aka yanka rakumi,Gaji nan take ta daura abinta a hannu, duk akan miji suke sunnawa kansu tsafi,Zayya tana ta faman kashe kudi magani yaki cin Gaji sai amarci da love akeyi Kamar ma Kara kaunar juna suke yi,ganin haka Zayya ta gaza hakuri ta dawo da bala'inta,Gaji ma ba jira,Haka Kawai Zayya tayi girki Gaji ta fito ta bude miyar ta dandana tace gishiri yayi yawa ga shegen yaji ke a gidanku haka aka koya miki taki tarbiyyar kenan? Oh no wonder goyon kaka ce tasa kafa ta daki tukunyar Miya ta watse a kasa zayya ta taso Suka kaure da kokawa har waje kofar gida suna kokawa,mutane sun cika damkam ana kallo anyi anyi su bari sunki ji,Gaji harda ja da baya kamar wata rago ta taho da gudu Zayya ma ta taho Suka hade gwaraf Kara Suka saki zafi ya ishe su ko wacce tana sosa goshi da hanci,aka kwashe da dariya da ihu Suka sake rukumuwa Gaji tace sai na kashe ki nice ajalinki,Zayya tace nice ajalinki kafin ki Gama dani zan gama Dake bazan yarda ba Danbinni ya dinga Kwanciya dake Yana cika gida da ihu ba Ni Kuwa sai yayi Shuru a dakina,gaji tayi tafi tace heeee ba Maggi baki da Maggi Ni Kuwa ajino moto ce harda curry,Mutane da Yara sai ihu da shewa akeyi ana dariya zamani na waya ana ta musu video kafin kace me Abu ya cika tik tok sai gani akeyi har WhatsApp wasu sun saki ko waccensu ba mayafi suna ta fada kamar kaji anci dariya ganin Gaji tana dukan kirji tana cewa itace Maggi ajino moto harda curry ana ta yanko wajen ana sawa a media,Haka ana saka wajen zayya da tace ita Danbinni baya ihu da kuka idan Yana kwanciya da ita sai Gaji,Danbinni ransa ya baci ganin matansa sun baza media a ranar da kyar manyan Mata suka sasanta fadan.


     Nawwar ne ya samu Mami da zancen aurensa,tace mashaallah Allah yasa ka Zama sanadin shiriyarta amma ka dakko da zafi zaka jawo min bacin rai,Matukar Baffa yaji zaka auri bare to mun shiga Uku ba zai yarda ba watakil ma ya sakeni,Nawwar yace Wai Rabiah tace na fada da Kansa ma zai daura auren ban San dai mene ba amma na yarda da ita ko ma mene gwara Kawai ayita ta kare,Mami tace tab Nawwar bari na hada kayana nayi Shirin barin gidan Yana cewa tafi sai tafiya, Sultana suna Jin labarin Nawwar zaiyi sure Kuma bare wai ma karuwa Rabiah wacce akan zamanta a gidansa Kawai an kusa ayi yaki a gidan su kansu sun San zaman Maminsu ya Kare a gidan tunda komai danta yayi a kanta yake karewa tuni Suka Fara kuka suna addua.

    Nawwar Kuwa sai da ya tara kowa na gidan har Sabreen sai da ya Kira ga Baffa,ga Papa,Mama,Iyamami,ana  jiran aji Nawwar me yazo da shi ya tara kowa haka, Mami tayi Miki Miki kusa da yaranta,Nawwar Kuwa Yana gaf da palon ya kirani a waya lokacin na tara su Sera na sanar musu komai har daukana da Baffansa yayi zaiyi sex dani,Star tayi shewa tace ai ni na dade da sanin Baban Nawwar Yana bin Mata tsohon kwartona ne shine ma ya siya min gida a Kaduna ya kaini makka,na more shi sosai Kawai fada Miki ne banyi ba,wannan ta kwana gidan sauki blackmailing nasa zamuyi mu biyu ni da ke muce lallai idan bai amince ba sai mun kawo video dinsa gida mun nunawa Amaryarsa Ummyn Haidar,sai Mun nunawa Dan Uwansa Baban Sabreen da Sabreen da Iyamami har Nawwar sai ya gani da kowa nasa sannan dole ki zauna gida daya da Sabreen da wannan gidan duniya ne Aljannar duniya ne,sannan idan yayi Masa baki ko ya saka Miki Ido a aurenki zamu saki video,tafawa mukayi su Santana Yan daudu Suka saki shewa,Sera tace Miracle da aure mu Kam aure sai dai a lahira waye ma zai aure mu sai dai muyi Ashawon mu,nace nima na dan wani lokaci ne zan dawo bafa son auren nan nake ba dole yayi min,Wayar Nawwar ce ta shigo,na daga da sauri yace yanzu Zan shiga ciki na Tara kowa Zan fada Kiyi addua,Murmushi nayi nace an gama, Yana datse Wayar Muka dauki shewa.


    Nawwar Yana shiga ya zauna,Papa yace Muna jinka Nawwar mene ka tara mu sai kace zaka raba Mana kadararka,Nawwar yace zuwa nayi na fada muku dan Allah kuyi hakuri ku yafe min Zan Kara aure,da sauri Sabreen ta shide tare da dagowa da sauri,Iyamami tace Yar gidan wace a dangi tunda ka damu uwarka ta zugoka ka nuna mana bamu Isa ba,dama ya tsaneni Iyamami cewar Sabreen ta fashe da kuka,Nawwar yace banyi Dan na batawa wani ba sai don na raya sunna,Kuma Allah yace ayi idan kana da Hali zaka iya adalci, Mama ce tace Kai dalla rufe mana baki zaka Kara aure dai sabo da baka son Sabreen jininka,Baku da aiki ku maza iliminku baya tashi da hadisin ku da Jan aya sai zaku Kara aure duk maza haka suke ba yau Muka taba ji ba,Papa yace zaka samu a gaba ka Raina mana hankali sai shegiyar Isa da mulki da mallaka da izza ana fada uwarku tace ai Kun gaji sarauta kakanta ne fa ya taba rike me unguwa tun irin sarauta ta kauye karka Zo Mana da gadara a nan wacce ka gada a wajen uwarka,Mami tace ai dai jininmu daya,yace ke ba Yar uwar mu bace can kisan danginki,Baffa ransa ya baci ya nuna Mami yace kece munafuka karki ce komai ke Kika zuga shi algunguma Ina jinka cikakke isasashe wacece a dangi kasan mu babu bare a cikin aure, fada mana wace,Nawwar ya gyara zama dan rainin hankalin Nawwar sai Kawai ya dakko musu labarin Rabiah yanda ta bashi tiryan tiryan sai da ya Kai aya yace wannan ba abar a taimaka bace wannan ba abar da za a tsaya a duba lamarinta bane,Ran Baffa idan yayi dubu to ya baci, yace na farko kasan a tsarinmu babu auren bare,amma dan ka maida mu wasu Yan Iska sai ka dakko bare a baren ma ba Yar asali ba sannan ma Yar tsuntuwa,karshen muni Kuma itace wace Muka sani ka Kai gidanka muke zarginta da karuwa,ai ba zargi bane karuwa ce cewar Sabreen tana kuka wiwi,ba a San Yar waye ba,Yar shege ce,mayya ce,jininsu babu na kirki,Basu da Nasaba bata da kowa, komai babu Kawai sai mu kawota cikin zuriarmu ta haifa mana mugun iri yaran zina cewar Baffa, to ka sani ni Sulaiman....kirrrrrrrr Wayar Baffa ta dauki ruri ya dakata da magana ya dauki Wayar sai ya ga Star ce take kiransa dama yau ma Yana so su hadu sabo da Amaryarsa bata nan ta tafi ganin gida,dagawa yayi ya mata Sallama tare da furta Ina meeting Zan nemeka anjima ya Kira star da Namiji Wai zan nemeka anjima dake Karuwan sun San irin wannan,sai tace bani minti daya hope ba a Jin maganata a fili yace ae da sauri


     Star ta furta ka tuna wacce jiya ka dauka a titi street din da muke tsaiwa? yace kwarai,tace to itace wacce danka ke son Aure Kuma kawata ce wallahi ka yarda tun wuri a daura aure Kuma idan an daura ba ruwanka da safgar Aurenta da mijinta Kuma tare zasu zauna da Sabreen din Kuma kaje kayiwa danka walicci idan ba Haka ba wallahi Muna da video dinka Wanda muke sex tare na dauki wasu Ina da su Matukar baka amince kawata aminiyata ta auri danka Nawwar ba wallahi kaji na rantse har gida sai nazo da kaina na nunawa Ummyn Haidar Amaryarka,Iyamami,Papa,da Nawwar Kai da dukkan family dinka kuma kasan Zan iya idan kana musu kazo mu hadu a hotel din jiya yau na nuna Maka videos din ka gani da idonka,yanzu ma ka bude WhatsApp dinka zaka ga wasu,Baffa gumi ya Fara hadawa da kyar ya iya magana yace Zan Kira anjima ya datse Wayar ya kalli Nawwar yace kowa ya tashi ya tafi na sallami kowa zanyi magana da Nawwar akan aikin gidan gonata da Zan bude Zan sake tara meeting,tunanin kowa har Nawwar a Kamfani aka Kira Baffa yayi asarar wata kadara yanda ya gigice yake hada zufa,har Iyamami fita Suka Yi da yakinin aure baza ayi shi ba,Baffa WhatsApp dinsa ya bude yaga videos dinsa guda uku tun daga Kansa har kafa tsirara Yana Sex da Star,bai sani  ba Su Star Indai zasu kwanta da mutum sai sun saka wata camera a boye Kuma baza ka gani ba,komai sai ta dauka incase ko zasu hadu da wani shege ya Raina musu hankali sai suyi blackmailing dinsa da shi,har su Sera duk haka suke yi,Baffa hankalinsa ya tashi da sauri ya goge na wayarsa gaba daya,ya kalli Nawwar yace na yarda ka aureta abinda Allah yace ba yanda za ayi idan na matsa karshe Allah zai iya dauke ni Kuma ayi abin bana raye,Kuma na duba naga abar taimako ce tabbas na yarda Zan Shige gaba Allah yasa Albarka amma da sharadi daga ni sai Kai Sai Mami zasu sani a gidan nan bayan haka ko kannenka Kar su sani gudun Kar Iyamami taji ta hana,idan an Riga an daura sai nace Nima ban sani ba munafuntata kayi na maka fadan karya nace lallai sai ka sake ta to karka saki abarka kuyi zamanku,jeka abinka yaushe ne bikin muje wajen waliyyin nata? Nawwar Kamar an dasa shi haka mamaki ya kamashi jiki a sanyaye yace Baffa ka Zama waliyyinta,Ni kuma Zan karbi aurena da kaina kaga shike nan tuwon mu man mu ya furta Yana dariya,Baffa a ransa Kamar ya fashe da ihu amma haka yayi yake yace acan kauyensu zamuje a Tara mutane a daura, yace an gama mun shirya Nan da 2weeks yayi? Baffa yace ai sati daya ma me kake jira tunda a shirye kake kana da gida da komai,Nawwar ya dinga mamaki maimakon murna sai da Suka gama tsarinsu sannan ya koma Yana bawa Mami labarin abin mamaki,ita kanta tace to lafiya kuwa anya lallai akwai wani abu a wayar da Baffa ya daga,tabbas Wayar nan ce da yayi akwai wani abu a kasa babba,ko ma mene Rabiah zata fada maka Watarana,yace tabbas daga nan fa Nawwar direct gidanmu yazo,Ya same mu Muna shirya gagarumar dinner da zamuyi har kala biyar Kuma shi zai biya ,sanye yake cikin shadda sky,na karaso jikin motarsa cikin abaya Ina karasowa Ina murmushi nace barka da zuwa Angona, Ido ya lumshe yayi Murmushi,nace ya kuka Yi? yanda Kika ce ya faru,nace Alhmdllh shike nan,Wai meke faruwa ne me kuka ce masa? nace karka damu Indai nice ana zuwa gabar da zaka ji Zan sanar da Kai kasan bana boye maka,nacewa yayi lallai sai na fada Masa nace tunda ka damu sai kaji to wata kwangila ce Suka fara da Saurayin star,Baffa ya Gama kashe kudinsa yayi domin wajen billions ya kashe shine Muka saka Saurayin muka ce yace idan bai yarda ba lallai zai janye kwangilar yasan shine da asara Kuma mutumin Sakataren gomnati ne na federal,shine ya yarda kaga munyi sa'a, Nawwar dai Yana mamaki yace Naga Baffa ne ya Saba da asara Kuma shi bai fiye son kudi haka ba akan kudi ba a tursasa Baffa yayi abinda baiyi niyya ba,nace to a nan sai yaso kudin Kam domin munyi nasara dan sai da mutumin yace ma Sai yasa EFCC ta bincike shi tunda Yana hada harka da gomnati kaga Kuwa kudin gomnati ba Wasa,Nawwar yace idan wannan ne Zan yarda dan Yana harkalla da gomnati sosai,Murmushi nayi dan Kuwa na tsara yanda star tace Yana harkalla da gomnati suna bashi kwangila, sabo da bai kamata dansa ya San ubansa yana Neman Mata ba,sannan bai Dace mu iya fadawa Nawwar ba in munyi haka ba Amana,da ace Baffa gonarmu ya shiga to zamu iya keta shi ta ko Ina ba ruwanmu da duk Wanda zai sani mu dama bamu hada Hanya da arziki ba bamu sanshi ba bare mu kyale.


    Nawwar na mikawa paper nace gashi mun tsara yanda bikin zaiyi,karantawa yayi yaga uban miliyoyin da Muka tara Masa,yace ku duk harkarku ba sauki a ciki yasa biro yayi cancel dinner yace guda daya za ayi tal bana son wannan shirmen party din Ni ba Dan bariki bane,nace to ai dai za ayi dayar ko? yace Inshaallah,nace sai lefe gidan su Sera za a Kai a Kauye,yace ba damuwa,karanta paper din ya sake yi yaga na rubuta kudin gyaran nono ba wani sakayawa sai lokacin ya kula ma,dariya yayi a ransa, yasa biro ya rubuta Boobs ki bar wannan a hannuna Ni Zan gyara shi da kaina,ya duba kasa yaga na rubuta Local government Kar a manta da kayan shaving dinsa,sai Kuma kudin siyen kayan gyara wajen sabo da wajen ya Kara lipton duk da wajen cewar yaji Lipton dama,Ya rubuta ke ga Lipton a wajen ango ai Yana nan zai tsoma shi a ciki,a ransa yace Yarinyar nan tayi balain rainani gani takeyi Kamar ban San komai ba ma irin ga wani ajawo,kwafa ya ja Ina jinsa nace Wai rubutun me kakeyi Kai? In kin karba Zaki gani, ya gama soke Wanda zai soke ya bani takardar yace zanyi transfer hole Kuma za a kama,karba nayi nace thanks ya shiga mota ya tafi,ni Kuma na koma na zauna a saman bench din da muke zaune Muna shirin biki.


    Takardar Muka karanta Muka ga abubuwan da ya rubuta shewa mukayi da ihu nace yeeeeeee shima Dan duniya ne yeeeeyyyyyyyyyy Muka tafa da su gaba Daya Muka hada hannaye waje Daya harda Santana Dan daudu yace Warrrrrrrrrr inji gwanja za a daki ganga wallahi aci uwar gayu ranar sai na saka bra katuwa ko na samu mashinshini,dariya ya bamu Muka kalle shi,ai ba jira washe gari tuni mun buga gate pass,gyaran jiki kuwa munyi shawara kayan kamshi da sauransu za a min a dafa Ni da kamshi yanda duk inda na zauna ma to fa kamshi zaiyi kwanaki bai bar wajen ba,sai gyaran skin sai maganin infection kawai,shi na Fara gaba daya Sera ce ta biya kudin Wai gudun muwarta gashi komai namu me tsada muke Yi dan mu ba garorin Yan bariki bane kucakai layinsu daban,kafin kace me kowa yasan zanyi aure a barikin duk shiri akeyi Mata da maza Wanda muke harka,duk Wanda ka gani dan wanka ne da karya da kashe kudi sune a bikin,anko ma wani materials me tsada aka fitar kala hudu kowanne agroup da Kalar nasu a wajen,maza Kuma shadda Muka fitar kala hudu irin na kalolin material din,sea blue,milk,purple sai silver,su Star nasu Sea blue Suka zaba, duk wata karuwa sai da ta gayyato Saurayinta data fi good time da shi Kuma yayi ankon Kalar na group din da take,Karuwan sun min Kara akwai hadin Kai ko wacce da kudin data bani sun tara min kudi sosai har maza.


   Tuni mun fadawa Inna a waya ta sanarwa Dan uwanta Jangudo me tausayina sai Murna yake shi ya bawa dattijai da su liman Alawar daurin aure ya fada musu ranar,shi Kansa Dagaci sai ji yayi an Kai Masa gida ana gayyatarsa a masallacin Juma'a na garin, yace ashe za ayita asirina bai ci Yarinyar Nan ba aure ma zata yi,to wallahi ko anzo sai na sa Iyayen yaron da kansu sunce sun fasa yanzu haka basu San Yar tsuntuwa bace,Gwaggo tace ai nima nan sai inda karfina ya kare,Aunty Amarya mamaki da bakin ciki ya hanata magana Sam,mu Kuwa ana jibi daurin aure ranar Friday zamu Yi dinner Saturday ana gobe aure zamu tafi Kauye idan an daura daga can za a dakko Amarya,Saura kwana hudu biki Nawwar ya hada lefensa Mami ce ta hada komai akwatuna set biyu guda goma Sha hudu ko wacce da kyar take rufuwa, Abin a sirri ake yinsa dole Mami da Seraline suka tafi can Kauye a jirgi,suka sauka a airport dake kano taxi Suka shiga me kyau har Kauyen Suka Kai Lefe,ai Kuwa Sera har gidan su Gwaggo taje tace an kawo lefen Rabi kuzo ku kalli abin farin ciki ko yarinya me iyaye  bata isa ta Kama kafar Rabi ba, kawai ta juya tayi tariyarta,su Kuma da son gulma da wuri Suka fice har Mairo ita da Aunty Marya ga Gwaggo Suka je tun daga ganin Mami Suka tsorata sun San ba talaka ne ba yaron,suka ga Kaya iya Kaya Saratu tana daga musu tana cewa Kudirar Allah ta sauka a kauyen nan idan da hankali ya Isa izina,Rabi yanzu tafi karfin mota sai dai yawo a jirgi, Gwaggo hassada ta motsa kasa karasa gani Suka yi harda cewa komai sai anyi karya ai Zamanin nan ba lefen ba ciyarwar shine aikin,Mairo tace uhmm ayi mu gani Suka juya Suka fice,Mami Murmushi tayi tace sune Suka rike Rabiah lallai dole taci wahala, da Yamma Suka koma a jirgi aka bar lefen a dakin Inna.

   Dagaci sabo da bakin cikin Jin labarin ya nemi Yara Yan daba ya biyasu kudi yace suje cikin dare su zarewa Inna wuka su sato Masa kayan lefen tas,Kamar Inna ta sani a daren tasa Jangudo yazo da yaransa maza samari Suka kwashe lefen tas aka maida gidansa,tana bacci cikin dare sai gasu sun banko kofarta dama bata rufe ba,makamai Suka zare Mata,Inna ta saki Salati tana hawaye suka ce Ina lefen da aka kawo wani ya shaki wuyanta,Inna ta rafka salati tace ai sun koma da abinsu inda Amarya take me za a bar lefe a nan ayi da shi,ku duba dakin,dakin gaba Daya Suka caje ba komai sakinta suka yi Suka koma a daren suka sanarwa Dagaci Suka Kara gaba abinsu.


  Kayana da ango duk mun dinka na fitar biki kaf, ba Wanda yasan ana biki a gidan Baffa sai Mami sai Baffa,yau ta Kama ranar dinner tunda aka sa bikin banga Nawwar ba komai Khaleel yake aikowa,ya Sha tsiya wajen Khaleel Kawai share shi yake yi, itama Sufia tace ai Dole nabi Mijina Khaleel musha kallon bikin Yan bariki dole akwai show,yace ai komai shigar dai hausawa za ayi inda kisan kina Kano, ranar 8pm za a fara sabo da haka wajen make up kowa cikinmu da inda ya tafi, nikam tawa inda sai wane da wane ke zuwa nan naje Wanda Ango ne ya biya,su Sera suna can tasu,abinka da masu samari kala kala dukkan matan kusan kowacce ta karbo shegiyar mota a wajen samarinsu,mota ce da mota ke tashi sai wadda ka gani,har wasu masu abota da yaran masu kudi duk an gayyato su sunyi anko Kuma Yan Mata na kece raini ba a magana Sabo da masu kawaye ma sun gayyace su, Kai kace bikin wata Yar wani ce da, waje ya hadu dama na manya ne, 8:30pm an gama min make up, munsha kayan namu Kalar decoration din wajen da aka yi Fari da dark pink sai Silver gaba Daya wajen walwali yake, ni rigar Amaryar tawa gown ce daga kasar waje yayi order online dark pink tana Jan kasa daga baya,sama ta kamani me dogon Hannu Net,sai gogoron da aka daura min Silver da takalmi da jaka silver Kalar shaddar jikinsa,hularsa da takalminsa duk Kalar shaddarsa Yar gaske an Masa babbar riga ta matasa dai dai shi, Khaleel ke driving dinsa a bayan sabuwar motarsa ta bugawa a news fara duk ta Sha adon flower da zare pink kana gani kasan ta Amarya da ango ce, daga wajen makeup din na fito wacce ta min ta rike min kasan rigar har motar na shiga ta rufe tana mana murna Khaleel yaja Muka wuce,hannuna wata a layinmu bahaushiya ta iya lalle tana yiwa hausawa karuwai, ita ta zana min ta gani ta fada ja da baki hannu da kafa nayi kyau abin ba a cewa komai, Khaleel yace Amarya kinyi kyau sosai wlh dama me kyau ce,nace na gode Friend


   Nawwar yace mu ganki na juyo sosai harda fari na lumshe Ido dan Wai yaga gashin idon da aka saka min sosai, hannayena da ya Sha lalle da abin hannu na amare na daga Masa ya gani na juya Masa tafin hannun ya gani,Khaleel yace kaiiiiii gaskiya lallen yayi,Nawwar yace Wai mene haka bana son munafunci,dariya yayi yace to sai ka bari a daura sai mu daina fada amma yanzu bata zama taka ba,Murmushi nayi na zare takalmin kafata tare da dago kafar daya nace ka gani, Khaleel ya leko da Kansa ya maida Kansa wajen tuki,Nawwar yace Allah ya kyauta maka Khaleel,kafar ya gani tayi kyau yace good, maidata dan Allah kin dameni,sai da na maidata yace muga hannun naki na Miko na dama,yace na hagu,na Miko masa hannunsa yasa a aljihu ya saka ya zaro gidan zobe ya bude naga zoben gold me tsada Dan karami hannuna ya rike ya saka min zoben a yatsana na kusa da karamin yatsan da kyar ya shiga yayi min cif cif,na washe baki nace yayi kyau thanks gidan zoben ya saka min a jaka tare da kudin liki masu yawa Yan dubu dubu sababbi,Khaleel yace gulmamme abinda kakeyi kenan,Bai kulashi ba, tun kafin mu karasa wajen event din muke jin kida na tashi Kamar hauka Yan gayu ana ta Shiga Su Sera Amarya suke jira suna waje wajen su goma sauran Kuwa an gama cika ana cashewa rawa suke ta rashin kunya ta fitsara Amma da aji ake yinta ba hauka ba yau ranar nutsuwace da yanga da aji, Yar zabil tana ciki itace MC ma,akwai wasu masu rawa a gidan karuwai ba rawar da basa Yi Mata da maza Yan rawar Solo ne ai kuwa sune suke takawa gwanin nishadi ana ta kallo suna mimimg wakokin hausa, a ciki Mc tayi magana da turanci Amarya da ango sun iso tayi da hausa kuma,kowa Zama yayi aka nutsu, mu Kuma muna mota me camera ya Mana pics iya Amarya da ango,Muka fito aka Yi mana harda frnds a wajen sannan a waje abokan ango sunfi su goma ga Mata kawayena Sufia ma tana cikin ayari mun gaisa da ita,Fara tafiya mukayi zamu shiga ango ya rike min hannu, Sera da wise suke rike min riga ta baya,Muna zuwa bakin kofa aka canja kidan Amarya da Ango muna tafiya ana fesa Mana snow da golden burzer kanana har sit dinmu na musamman.


    Dinner ta Matukar kayatar duk da an zubar da daraja a wajen amma yanda muka tsara anyi abin da iyawa a tsari da birgewa kowa zaice wayewa ce tayi yawa a wajen, anci an Sha an zubar da liki,Ango har daloli ya lika ana ta sawa a tiktok da sauran media, Allah yasa Sabreen tana ta bacci Jamcy ta watso Mata pics da videos Amma tana ta baccin asara ta kashe wayar gaba daya an Sha kwaya, sai da aka gama Dinner angwaye a guess house dinsa aka sauke su komai a gidan Su Khaleel akayi Mami ma tana can duk da ba Wanda ya sani.


    Washe gari Sunday Muka Yi Shirin tafiya Kano kauyen mu ai a ranar da yawanmu Mata munfi ashirin Muka dira a kauyen ango ya biya jirgi Muka zo Kano Muka shigo a taxi, angwaye sai da safe zasu zo a jirgi su ma da Iyayen Ango,Sabreen an manta da waya ana ta bacci in ta tashi ma wanka take taci abinci tayi Sallar da Zata iya ta koma bacci,gamu iya karuwan da yawan mu Muka dira Wise tace dole Dagaci yasan mun shigo gari.


AsmaBaffa

08061929616

No comments

Powered by Blogger.