Babban Goro 4
Episode___4
8:37PM.......
Saif ya shigo gida, part ɗinshi ya fara wuce wa,
Sai da ya watsa ruwa ya ɗan huta sannan ya nufi part ɗin Momi,
Da sallama ya shiga sanye da jallabiya, babu kowa parlor sai tv dake da aikin shi, kai tsaye ya nufi upstairs ɗakin Momi.
Zaune ya tararda ita sanye da glasse a idonta tana duba wasu takardu, sallamar da yayi ne yasa ta ɗago kai ta kalleshi tare da amsawa,
“Wa'alaikumussalam Saif”
“Na'am Momi ya gidan?”
“Gida lafiya kalau daman ina nemanka”
Zaunawa yayi yana faɗin “Toh gani Momi Allah dai yasa lafiya”
Glasse ɗin ta cire ta aje sannan ta fuskanceshi
“Akan maganar matarka ne Saif shi fa Aure ɗan hak'uri ne kaji ka k'i ji ka gani ka k'i gani ita mace dole sai anyi hak'uri za aji daɗin zama da ita ballantana yarinya kai kace kana sonta Auren soyayya kuka yi bai kamata a ce har saki ya shiga tsakani ku da ita ba”
Nisawa Saif yayi,
“Shaidan ne amman kuma ai na maida Aure na”
“Naji ka maida Auren ka amman miyasa ka hana matarka ta dawo ɗakinta?”
“Momi ni halinta ne bana so duk na tuna sai naji nafi sha'awar zama ni kaɗai ba tare da ita ba”
Ajiyar zuciya Momi ta sauke
“Kana yabo Huddallah da mugun hali wadda ni ban taɓa ganinta da shi ba, kuma idan ma tana da wani halin ai yanxu zata daina tunda saki ya shiga tsakanin ku,
Amman ace abi yak'i ci ya k'i cinyewa har iyayen ta su kai ga magana”
Shiru yayi kanshi a kasa wadda hakan ya bawa Momi damar cigaba,
“Ina son dan Allah ka mayar da matar ka ɗakinta ba zai yiyu ka dawo nan ka tare ba dan ka saki matarka kaje ɗan Allah ka ɗauki matarka ku kuma gidanku hankalin mu ya kwanta nata ya kwanta na iyayenta ma ya kwanta”
Gefen fuskar shi ya shafa “Shi kenan Momi insha Allah yau zanje na ɗauko ta ko Dad yayi min magana indai shine matsalanku daga yau ya wuce”
“Haka nake so Allah yayi maka albarka ya baku hak'urin zama ya kawar da fitina.
Amman a'ce dan ka saki matarka sai ka dawo gida ka tare sai kace mace”
Da dariya Momi ta k'arasa maganar,
Shi ma tashi yayi yana dariyar yayi mata sallama ya fice,
Yana fitowa ya nufi dining area,
Zaunawa yayi ya zuba ma kanshi abinci, sai da yaci yayi nas sannan ya dawo saman kujera ya zauna sai tunane tunane yake.
Sai kusan goman dare sannan ya tashi ya nufi part ɗinshi, ruwa ya sake watsawa ya shirya cikin shadda blue color da bakar hula bayan ya ďauki car keys ďinshi ya nufi parking space,
Yana tada motar ya ɗauki hanyar da yasan zata kai shi gidansu Huda,
A hanyarshi ta isa can ne ya kira wayar Dad yana labarta mishi yadda sukayi da Dr. Salamatu,
Murna Alhaji Aminu Ibrahim. Yayi sosai ganin Saif yazo ya tafi da matarshi,
Huda kan sai da nuna halinmu na mata wai ita ko a jikinta alhalin a zuciyarta farinciki ne falau,
Har taso tak'i zuwa sai kuma wata zuciyar ta hana ta dan tasan halin Saif duk tayi kuskuren k'in binshi ba zai sake dawowa ba sai dai ta kai kanta,
Nasiha sosai Mahaifiyar Huda tayi musu Hajiya Ramatu sannan ya ɗauki matarshi suka nufi gida,
WASHE GARI..........
Ziwww (vibration) kake ji wayar Saif dake saman bedside drawer tana yi,
Daker ya mika hannu ya ɗauki wayar saboda nauyin bachi da yake ji,
Huda na kwance saman kirginshi, ba tare daya duba mai kiran ba yayi picking ya kara a kunne,
Bansan mi akace mishi ba na dai ya buɗe ido da sauri ya zabura wadda har yayi sanadiyar tashin Huda “What?”
Abinda ya furta kenan yana kokarin saukowa saman gadon,
Tashi yayi tsaye yana faɗin “Ok gani nan zuwa”
Nan ya kashe wayar ya ɗora ta saman mirror,
Kallon Huda yayi dake mika ya sakar mata murmushi.
Bathroom ya nufa, a gaggauce ya watsa ruwa ya fito
Wardrope ya nufa ya shirya cikin kanana kaya Black Jean and white t-shirt anyi mata zane blue,
Huda dai sai kallonshi take ganin yana kokarin saka takalma yasa ta tashi zaune tare da jan bargo ta rufe jikinta,
“Dear wai lafiya dai?”
Dagowa yayi ya kalleta
“Wani ɗan aiki ne ya taso”
Fuskar mamaki tayi,
“Yanzu da safe nan dear yau fa weekend kuma ko breakfast bakayi ba”
Rika ta yayi ya kwantar saman gadon
“Cigaba da bachi ki i will be right back ok?”
Kiss ya manna mata saman goshi ya shafa fuskarta ya fice,
Cikin yan mintuna ya isa gidan, a parlor ya tararda Dr. Salamatu tare da wata budurwa da bazata wuce sa'ar Minal ba.
Dr. Salamatu na ganinshi ta tashi tsaye da sauri hawaye na bin fuskarta,
Gurin ya samu ya zauna zaiyi magana ta riga shi
“Saif bani da wadda zan kira ya taimaka min sama da kai Saif yata zata iya shiga cikin wani hali bani da kowa sai ita, ita kaɗai na haifa Saif ka taimaka min karna rasa ta dan Allah”
Cikin kuka ta k'arasa maganar har muryarta na rawa,
Kanshi ya shafa ya sauke ajiyar zuciya,
Sam bai jidaďin yadda ya tararda Dr.Salamatu tana kuka ba ko kađan baya son kuka ko na yaro balle babbar mace,
jin kukan nata yayi yawa yasa ya ɗago kai ya kalleta “Yanzu ya kike so nayi?”
Da sauri buduwar ta kalleshi tace
“Koma minene kayi mana ka taimaka mana”
“Tana ina yanzu?”
“Tana Airport munje bamu samu ganinta ba ance Kasar zata bari kuma kaga zata iya shiga ko wane irin hali tunda zuciyar ta a rufe take”
Wannan karon Dr. Salamatu ce take maganar cikin kuka,
Shiru yayi ya tsurawa carpet ɗin ido har na tsawon lokaci...
Can wani tunanin yazo mashi da sauri ya tashi ya fice ba tare da yace dasu komai ba.
Leave a Comment