Bakar Inuwa 77


 *_Episode 77_*

.........Bayan wucewar su Basma sai da ta tabbatar an gama shirya abinci a dining tabar sauran komai hanun mama ladi sannan ta shigo ɗakinta da yanzu ta dawo.

Abdull dake a bayanta goye ta sauke saman gado, dan Anne ta gargaɗeta matuƙa akan ta dinga goyasa yanajin ɗumin jikinta batason wannan halayyar da matan yanzu keyi naƙi goya yaro ko ace za'a bama masu aiki suyita faman raino ke uwa kina hutawa. Wanka ta shiga, fitowarta babu jimawa tana ƙoƙarin neman kaya marasa nauyi ta saka Abdull ya farka ya fara ƙananun kuka. 

        “Oh oh babban mutum yi haƙuri ina zuwa. Nasan matsalarka yunwace acici”.

       “Ai duk ke ya gado cin nan ba wani ba”.

   Ta tsinkayi amsa daga bakin Ramadhan da bataji shigowarsa ɗakin ba. Ɗan juyiwa tai tana kallonsa, dai-dai yana karasawa saman gadon ya dauka Abdull yana sawa a kafaɗa. Murmushi tayi da ɗauke kanta tana cigana da ɗakko kayanta. “ALLAH ya Ramadhan kaima kasan banda ci, sai dai in kai”. Ta ƙare maganar tana nufosu kaya a hannu.

     Kayan ya ɗanbi da kallo, cikin neman magana yace, “K har kina tunanin saka kaya a yau?”.

     Cikin rashin fahimta tace, “Kamarya? Kana son na zauna da towel ne na kwashi mura?”. Murmushi yayi mai ƙayatarwa, ya sauke Abdull daya koma barci saman ɗan gadonsa ya gyara masa kwanciya. Tana ƙoƙarin saka riga ya riƙeta. “Idan ma kinsa zan ciresu ne, minene na wahal da kai?”.

     Kunya ce ta kamata, cikin marairaicewa tace, “ALLAH ya Ramadhan ba kyau, kaifa yanzu ka girma sunanka Daddy”.

      Kai ya dungure mata yana murmushi, sai kuma ya zare ribbon ɗin kanta tare da tallafo kannata ya manne goshinsu waje guda suna shaƙar numfashin juna. “K miyasa kin iya fassara mutum. Ni karki lalatani bankai can ba”.

     Mintsini takai masa a gefen ciki, ya  janye jikinsa da sauri yana faɗin “Ouch yarinyar nan muguntar da kika koyo kenan a yawon arba'in ɗin”.

    Dariya Raudha ta ƙyalƙyale da shi da masa gwalo. “Ai kaɗan ma kenan”.

     Ƙwafa yay fuska a cuskule kamar gaske. “Haba yarinya zan rama ne idan kikazo hannu zaki gane kuranki”.

     Juyowa tai da sauri garesa fuska a narke, dan tasan wanene mijin nata. “Please Noorullah sorry”.

     “Ba wani sorry ai saina rama”.

  Da sauri ta nufosa ta ɗane masa baya duk da ta zama lukuta yanzun, “Ya ilahi, yarinyar nan kin koma biri ne?”.

    Ya faɗa yana juyota ta sakko suka faɗa saman gadon. “Gaba ɗaya kin zama ƴar lukuta amma ƙibar ta miki ƙyau”. Yay maganar a hankali yana busa mata numfashinsa a kan fuska. Kafin ta samu damar magana ya manne lips nashi kan nata. Itama a zalamen take, dan haka babu musu ta miƙa wuya ita shaidace mijin nata yayi haƙuri, kusan kwana hamsin ai ba wasa ba. Sai da taga zasu wuce hanyar da suka ɗakko ta fara ƙoƙarin janye jikinta. Amma ya nuna shifa sam bai yarda ba. Roƙon duniya da magiya ya nuna mata baiji bai gani. Dole ko ta miƙa wuya. Daga baya kuma ta shiga tsoro, dan tasan taji gyara babu ƙarya balle algus. Tafiya tai nisa Abdull ya sake farkawa yana kuka. Amma Ramadhan sam yaƙi nuna yama jisa, itako Raudha hankalinta duk sai ya koma kansa (uwa kenan. Uwa mafi uba koda uban sarki ne👍🏻).

          Lokacin daya kai inda yake buƙatar zuwa Abdull yaci kuka harya godema ALLAH, da ƙyar ta iya dauriyar tashi ta nufi bayi, Bata ɓata lokaci wajen gasa jikinta ba ta fito dan har yanzu Abdull bai bar kuka ba duk da tabar Ramadhan na ɗan shillashi cikin ɗan gadonsa.

     A yanzu ɗinma haka ta samesu, batace da shi komai ba ta yafa towel ɗin da take goge jiki a kafaɗarta ta ɗauka Abdull ɗin. Tashi yay shima batare da yace mata koman ba ya nufi bayin.

      Lokacin daya fito tana shayar da Abdull ɗin idonta kan yaron nata da ɗan wasa da sumarsa. Ramadhan ya zauna kusa da ita da riƙe kafar Abdull dake motsawa. “ALLAH sarki kakan Dadynsa kaji yunwa da yawa. Mamanka ce ta cika zalama da wuri take son a farauto maka ƙanne”.

   “Innalillahi... Kai Ya Ramadhan”.

“Ba wani Ya Ramadhan anan. Inba azalame kike ba miye daga zuwana duba Bappina zaki wani kadandaneni sai da nayi”.

      Ina kasa Raudha ta shige dan kunya. Ta ture kansa daga kafaɗarta, shiko ya ƙyalƙyale da dariya. “Uhhm tundafa kin samu kinmin kat aiƙyafa tureni, dama Ustazan nan shiru-shurunku aiba na lafiya bane. Yanzu haka nasa kina nan kina addu'ar a koma second r.......”

    Hannu tasa ta rufe masa baki, idanunta har suna tara ƙwalla. Ta dangwarar masa da Abdull a cinya zata miƙe tabar wajen ya riƙota yana dariya. “Yi haƙuri wasa nake my Partner, duk fa nine zalamammen”.

    Ita dai bata sauraresa ba, da ƙyar ya samu ya lallasheta cike da salonsa da yake kasheta da shi. Daga karshe suka ɗunguma falo sukai dinner aka sake dawowa filin daga....

 Rayuwa ta cigaba da tafiya cike da farin ciki da jin daɗi ga waɗan nan ma'aurata, hakama mulkin Ramadhan kowa nata san barka. Bayan sun gama amarcin jegonsu ta tattara ta koma makaranta. Ramadhan ya sake maida hankalinsa ga harkokin mulkinsa. Yayinda a gefe ya naɗa kwamitin bincike akan harin da aka kaima Bappinsa.

 Sai dai kuma mi a hankali rikice-rikice suka fara tashi a wasu yankuna na ƙasar NAYA. Ga yawaitar ƴan fashi a tituna da gidajen manya. Al'amarin kamar wasa sai ya dinga faɗi da gawurta harya fara fin ƙarfin jami'an tsaron dake a tsaye kan matasalolin. Sosai hankakin Ramadhan ke tashe. Tsabar ruɗani har wata rama yay yay duhu sosai. Ita kanta Raudha dake ƙoƙarin kwantar masa da hankali dauriya kawai take, dan zubda jinin ya fara yawan wuce hankali. Dan takai anabin manyan malamai ana musu yankan rago a cikin gidajensu. Komai daya shafi mulki sai ya fara tangal-tangal musamman manyan ayyukan da ake shimfiɗama talakawa. to ana ta rai waketa wani aiki. Mutane ma idonsu ya daina ganin ayyukan tashe-tashen hankulan kawai suke gani, akoda yaushe cikin zaman meeting ake tsakanin jami'an tsaro da masu faɗa aji, sai dai babu alamun samun wani sauyi. 

    Ba Ramadhan kawai ba, hatta su Anne hankulansu a tashe yake matuƙa, dan duk mai hankali ya kalla abubuwan da idon basira yasan ƙirƙirarsu akai da gayya.. Ramadhan na gab da cika shekara biyu a mulki Bappi ya bashi shawarar sauke duka manyan shugabanin tsaro, hakan kuwa akai, aka sauke su aka ɗakko wasu aka ɗora...

      Hakan ya tada hankalin su Alhaji Haladu Gwandu matuƙa, dan shirine da babu wanda yasan dashi wayar gari kawai akai shugaban ƙasa ya zartar da hukunci. A gefe kum aka tara matasa takowane yanki aka basu aikin sakai sai dai gwamnati zata dinga biyansu albashi mai tsoka. Sannan aka saka maƙudan kuɗaɗe ga duk wani farar hula daya kawo sunan ɗan ta'adda uku ya tabbata kuma ɗan ta'addanne. Wannan shirifa ya zaburar da natasa da talakawa, burin kowa ya samu wani maraji ya kwafe sunansa a takarda da mafakarsa yakai hukumomin sirri da aka baza a kowace jiha ta ƙasar NAYA. Sai gwamitin bincike na musamman da aka ajiye su kuma a gefe akan son sanin ta inda makamai ke shigowa ƙasar ta NAYA.

  Lallai wannan shiri ya zaburar matuƙa, dan ya maida kowa jami'in sirri mai himma. Takai har ƙananun barayi ma basu da wata sakewa yanzun, dan kan barci ne makwafcinka na maka minshari. Burinsa kayi kuskure kaɗan yakai sunanka a sauke masa kuɗaɗensa. Tofa inji masu jimamin fitar magana, bincike fa ya fara daukar hanya, dan wasu sunaye da ba'ai zato ko tsammani ba sun fara bayyana kansu ta hanyar yaransu da aka fara cafkewa. Bincike yanayin nisa firgici da ruɗani na sake bayyana ga su forma president. Har wani zama na sirri suka ƙirkira da Ramadhan, bai musaba ya amshi baƙuncinsu, ya kuma saurari dukkan soki burutsinsu daya sake tabbatar masa lallai sune ke ƙulla komai kamar yanda yake hasashe shi da Raudha. Ƙin cemusu komai yayi hakan kuma sai ya ƙona ransu.

     Sunma rasa inda zasu saka hankalinsu suji daɗi dan sai tsinci ɗai-ɗai akema yaransu, abinda zai baka mamaki harda wanda suke cikin mulkin dumu-dumu. Ta ɓangare ɗaya suke ɗan jin sassauci idan suka tuna ta Ramadhan ta kusa ƙarewa tunda sunada tabbacin ya shaƙi gubar da suka shirya ya shaƙa ɗin ta shekaru biyu. Ya kuma sha a drinks sai dai ganin bai taɓa kwanciya ciwo ko canjawar jikinsaba na ɗan saka musu wasuwasi.

    Sai dai a randa suka bama zukatansu salama da wannan madogarar a ranar jami'an tsaro suka cafke Aunty Hannah a dalilin maganar drinks da kuku ya tabbatar itace ke bashi. Ranar Raudha taci kuka sosai, Ramadhan yayta aikin lallashi. Ya tabbatar mata dama sun gama da kammala wannan bincike shiyyasa aka cigaba da riƙe kuku. A ɓangaren Hajiyar Birni ma hankalinsu a tashe yake, dan Raudha ta kira tana kuka saboda zuwa yanzu kowane kafar yaɗa labarai babu wani sabon labari sai na kama matar vice president da ake zargi da haɗa kai da kuku domin halaka shugaban ƙasa. Asabe ma ta kira Raudha, hakan sai ya sake rikitata har Ramadhan yama rasa ta ina zai lallasheta. Kukan da taci ya jaza mata zazzaɓi sai da Dr Hauwa tazo dubata, a gwajin farko kuma ta tabbatar musu Raudha nada cikin wata biyu.

     Sake rikicema Ramadhan tayi, tayama za'ace tanada ciki bayan shekarar Abdull ɗaya da watanni huɗu. To shi dai abun yafi karfinsa. Ga rikicin mulki ga nata sai kawai ya haɗata da Anne............✍


No comments

Powered by Blogger.