Daudar Gora Book 2 page 83
…Babu wanda bai zaro ido ba a falon. Cikin bacin rai Iffah ta ce, "Na fika sanin wannan"Jikin matar na rawa ta cigaba da zayyano mata sauran. Yayinda tuni Ummu dake rude Iftihal mamuke da ita ta yunkura da niyyar zuwa ta nemi Kaka a waya, dan dazun da sukazo sun kawo mata wayarta shima Babiy yana amfani da nashi. Kin sakinta Iftihal tayi, dole sai tare suka tafi. Iffah kam juyawa tai ta dubi hadimanta da ke dauke da abincin data bada umarnin a biyota da shi, ta nuna na hannun amintacciyarta. "Ajiye musu shi suci"
Da ga Banou har abokiyar aikin nata kuka suka sanya, dan su suka san abinda suka gani a abincin. Ko kallo basu ishi Iffar ba, tana tsaye a kansu fuskarta kawai abar firgitarwa ce. Haka suka fara cin suna kuka da rokon tayi hakuri, a haka su Malikat Haseenat da akeje aka sanarmawa suka shigo hankali tashe. Dan can sun samu Malikat Bushirat tayi barcin da kyar bayan an rufu kanta da addu'oi. Kallon Iffah da su Banou din kawai suka tsaya yi cirko-cirko. Daneen Waheeda kam tuni ta koma bayan Mammah ta makale, yayinda Daneen Ammarah itama nata kamanin suka fara canjawa dan idanunta sun kada sunyi jazur. Ture abincin Iffah tai da ga gabansu, ta wani irin hankada Banou gaban Malikat Haseenat. "Jeki sakar mata kafafu!!". Cikin madaukakin mamaki Malikat Haseenat ke duban Banou da Iffah. Sai dai razananniyar tsawar da Iffahr taima Banou din ita kanta sai da zuciyarta ta shiga tsitstsinkewa. Banou dake kuka cikin rawar jiki ta kama kafafun Malikat Haseenat, wani fushin kumburi da kafafun sukai tsahon shekaru an kasa gane kansa sai gashi yau yana bajewa, Kusan minti biyu tace mata ta mike, mikewar tai jikinta sai kakkarwa yake, du da girman jikin nan nata ga tsaho amma Iffah dake yar digila gabanta ta zame mata dodo. "Na baki minti hudu, ki dakko tukunyar da kika ajiye a cikin flowers".
"Umarninki shine abin jirana ranki ya dade".
Banou din ta fada cikin sake gurfana. Suna tsaitsaye har yanzu babu wanda ya iya cewa komai sai ga Banou ta dawo da tukunyarta, A gaban Iffah ta zube, ta bude tukunyar ta shiga fiddo abubuwan da ke ciki. Abinne kamar tsokar nama, duk ta daure. Kwancewa ta shigayi tana sakinsu, firrrr suke tashi kamar tsuntsaye, wasu ko da kyar zakiga sun tashin saboda ta jima tana wahalar da su. Cikin
bada umarni ta dubi sauran hadiman ta ce, "Aje a duba duk wanda yake a halin ciwo ya mike a yanzu a kaimun shi tsakkiyar masarautar nan. Ina bukatar Ghazi guda biyu anan".
Cikin kankanin lokaci Ghazin data bukata suka shigo, su tasa suka tasa mata keyar su Banou.
*Tun fito da Hadimar da ta jibga a sashenta al'amarin ya fara zagaye masarautar. Abin mamaki sanda take fitowa su Malikat Haseenat biye da ita masarautar ta gama cika. Dan sashe-sashe an fito kamar busar kaho. Cikin kankanin lokaci duk wani mara lafiya dake gidan aka fito da shi, harma wanda ba Banou din ce ta tabasu ba. Tana kuka da faman rufe fuska ta tsatstsallakasu. Tana gamawa suma sawa tai aka daure mata su tare data farkon. Dai-dai nan su Baby suke isowa cikin masarautar. Hakama Tajwar Eshaan a rikice Malikat Haseenat tai kiransa ta sanar masa babufa lafiya a gidan da ya kamata ya
fito. Dama shirin fitowa yake, dan amintaccensa yazo masa a kidime babu dadewar nan, hakama Sayeed Fayzul-haq ya kirasa shima.
Lokaci daya wajen ya dauki shiru sakamakon fitowar tasa, dan abunne da babu wanda yay zato. Kowa a wajen sai da yay kasa da kansa har Iffah, dan a zahirinsa yake kyakykyawar fuskar nan a bayyane, sai dai fa cinkus take babu alamar wasa ko sassauci. Amintaccensa ya ajiye wata yar kujera mai kyau dake a ninke aka budeta. Sai kuma katuwar umbrella da aka bude masa duk da bawani ranar nada zafi bane dan ta la'asar ce ma dake neman faduwa. Sai dai kuma a mamakin kowa ma bai zauna ba. Sai duban Iffah da yay na kusan mintuna biyu. A hankali ya furta, "Mike faruwa". Cike da irin girmamawar dake nuni da ba ita bace ba ta kai kasa gurfane gabansa. Gaisuwa ta fara mikawa,kafin dukkan abinda ke faruwa ta zayyane masa. Idanu ya dan lumshe da sake budewa. Kamar bazaice komai ba sai kuma yay mata nuni da ta tashi, tare da fadin,"Duk da ba itace a tare da gangar jikinta ba kuskurene kai Zawjata-almilk kuma * Malikat * kasa a kowane irin yanayi a gaban al'ummar kasar ta"
Wanna furici nasa ne yasa kowa fahimtar ba ainahin Iffah'r bace iskokinta ne yau suka bayyana kansu abinda basu taba yi ba, sannan kuma maganar cikin jikinta tabbataccene tunda har shi da kansa ya kirata (MALIKAT). Neman afuwa suka shiga yi, da tsayawa tsaye akan kafafun Iffah'r. Alokacinne Sayeed Fayzul-haq ya yafito Kaka dake tsaye kawai yana murmushi. Sai da ya fara mika qaisuwa ga Shahan-shan shima sannan ya duba Iffah, kamar yanda sukaima Tajwar Eshaan bayani haka shima kakan sukai masa. Kansa kawai ya jinjina da cire jakar hannunsa ya ajiye. Ruwa ya bukata, cikin kankanin lokaci aka kawo masa. Magunguna ya fiddo da yawa ya shiga zubawa a ruwan nan. Wani irin ihu su Banou suka dingayi da rokon yayi hakuri, bama su ishesa kallo ba ya fara dibar ruwan maganin yana watsa musu. Ihu na gaske suka dinga kwallawa da surutai suna girgiza da gunji. Sai da yay musu ligif sannan ya basu umarnin bayani da bakunansu. Biyun sun tabbatar da su ba mutane bane sun rikidane kawai. Kuma a yau din nan suka shigo cikin masarautar bisa umarnin uwa da Iffah ta raunata a dazun. Banou kam mutum ce ita, sai dai akwai aljanun maita tare da ita, irin kusan duk zuri'arsu ke da shi, dan itama cikin zuri'ar uwa take. Cikin galabaita ta shiga fadin tun sanda take tare da su.
"Ni shekarata goma sha tara anan, tun bayan korar uwa da akayi da ga wannan masarauta. Ina daya daga cikin zuriarta da aka kora shekaru masu yawa da ga cikin wannan alkaryar, a da kakanninmu wannan filin masarautar shine garinsu. Amma sanda za'a kafata sai aka tashesu aka canja musu waje. Ransu ya baci matuka da wannan al'amari, dan tunda suka taso anan suka samu iyayensu da kakanni suma, nan kadai suka sani matsayin kasarsu kuma gari, ga abubuwan bautarsu masu tsahon tarihi tsahon shekaru duk an ruguza musu. Dan haka sukaji zafin tashinsu da akai da bata musu wajen bauta da abubuwan bautarsu saboda gina masarauta bayan akwai filaye da yawa da babu kowa a cikinsu miyasa baza ai acan ba. Wannan haushin yasa sukaki zama inda aka basu sukai hijira zuwa cikin jeji. A haka suka cigaba da sabuwar rayuwarsu wadda da kyar suka saba da wajen, sai ya zam duk wanda aka haifa a cikin zuri'ar mu wannan
shine labarin da za'a raineka a kansa, da kuma kiyayyar wannan gida. A haka duk muka rayu da burin daukar fansa. Mun dade da shiga jikinku muna muku illa da suffar bokanci, hatta lokacin da kuka samu ambaliyar ruwa a kusan kasar baki daya zuri 'armu ne suka balle wani yanki na kogin da ke zagaye da ku. Mu bamu taba jingina da ku domin mu taimakeku ba sai dan mu ruguzaku, a haka iyayenmu da kakanninmu suka dinga shudewa. Uwa ta kasance mafi girman hatsabibanci da yin tasiri a al'amuranku a cikin duk wanda suka zo da nufin masu taimako a gareku a cikinmu. Duk da dai akaf zuri'armu daga maye sai matsafi, kuma kowannenmu nada abinda yake yi domin ku. Jajircewar uwa da zamowarta mafi iyawa a kan iyawar kowa cikinmu yasa ta zama shugaba a garemu, kuma ita muke fata da gain ta kusa karbo mana wanna masarauta data kasance tushenmu ta koma tamu. Amma sai abubuwa suka fara canja salo a dalilin tsohuwar can (ta nuna Malikat Haseenat) ta kanainaye komai tana faman rushe duk wahalhalinmu da muke gain saura kiris komai ya kare. Dan haka mukaita kawo mata hare-hare amma bam samu nasara a kanta ba. Ana cikin hakan rana tsaka ma sai ga Uwa mun tsinta a yashe cikin mawuyacin hali anci zarafinta a dalilin wanna mutumin da mahaifinsa (ta nuna kaka). Hakan ya mana ciwo matuka, ga uwa nakan gangarar mutuwa, a take muka tattara duka karfinmu wajen cetonta, dan duk karfin dake tare da ita na tsafinmu na gado da ma wanda ta samarwa kanta wannan mutumin ya lalatashi. An bada umarnin wasunmu su sake dawowa cikin masarautar nan, duk da zuwane na kasada ni a kasance a daya da ga cikinsu. Kuma nice nan a kashe Shahan-shan Abdull-Majeed a cikin suffar maciji, dan inada maita mai karfin gaske fiye data kowa a cikin zuri'armu. Bayan mutuwarsa na cigaba da bibiyar rayuwar war masu gida, sai dai na kasa kaita kasa saboda abubuwan kanta, nadai samu nasarar nakasar mata kafafu ta hanyar ciyar da ita abubuwa a cikin abincinta. Amma tun randa na had da Zawjata-almilk abubuwa da yawa suka lalace min, dan tanada iskoki masu karfin gaske, itace ta dakusheni akan abubuwa masu yawa. Ta kuma min daurin da bazan iya barin wannan gidan ba duk da naso yin hakan tun a ranar farko dana hadu da itan. Uwa tayi iya kokarinta itama na son ganin ta fiddani amma ta gagara".
Ajiyar zuciya kawai kakeji na sauka da al'ajabin wadan nan abubuwa wai kamar wata almara. Banou da kowa ya sani mafi zama kololiwar amintacciya ga Malikat Haseenat dai, wadda inba abincin data girka mata ba batacin abincin kowa sai Daneen Ammarah. Kai to ai yanzu kowama ba abin a yarda da shi bane hatta hadiman nasu.
Kaka ya jefama Banou tambayar, "Mutane nawa kika cutar a shekarun zaman nan naki?"
"Ni ban san adadi ba. Amma na halakasu da yawa, dan akwai ayyukan da na dinga ma uwa da yarjewar wata babba a gidan nan. Sannan akwai wadanda na kashe dan radin kaina da wanda na dinga cinyewa cikinsu. Na karshen nan dana cinye shine na Jasrah a randa Zawjata-almilk bata da lafiya…..✍️
Leave a Comment