Daudar Gora Book 2 page 85
85
."Duk wanda ya sanni tun a kuruciya yasan ni yarinya ce mai yawn kirinki, nayi rashinji matuka, dan a fada biyar da za'ai dani cikin yara to da wahala ka samu daya a ciki da nake da gaskiya. Tun ina karamata na
kasance mutum mai son gain kowa ya zama a karkashin ikona. Hakan yasa ban yarda da abota da wanda muke shekaru daya ba ko ko sukafi gidanmu arziki. Duk kawayena na girmesu, na kuma fisu wayo, gidanmu kuma yafi nasu komai. Hakan yasa dole sukemun biyayya da bin abinda nake so koda ace su basa son sa. Mahaifiyarmu na yawan mun fada akan wannan halayyar, hakama mahaifinmu. Nakan nuna naji na dan wani lokaci amma da kura ta lafa sai na koma gidan jiya. A haka na taso da wannan rayuwar har girma. Kowa yasan Bushirat boss ce a cikin kawaye, idan kuma kana son ka zauna lafiya tilas ne kamun biyayya. Gidanmu gidane na manyan mutane, masu ilimi kuma Alhamdullah munada dukiya. Ina alfahari da hakan, amma kuma inada buri na kai da kai. Kasancewata kyakykyawa nayi samari kala-kala, duk da dokar mahaifinmu shike zabama kowace yarinya a gidan mu miji, a nawa bangaren babu wannan ra'ayin. Sai dai na shanye ban taba sanarma kowa ba. Duk wanda zai zo gurina sai nayi duk yanda zanyi na bibiyi nasabarsa da nauyin aljihunsa, idan ka kasance baka da ko sisi zan tattaraka na watsar, tare da kashedi mai girma na ka fita a hanyata. Wasu sukan barni cikin sauki, wasu ko saina yi jan ido kona hada musu tuggu a wajen yayuna sun kore su. A haka na kammala karatuna na boko, wanda na taso naga anayi a gidanmu kam shima na samu gwargwadon iko wat ilimin addini. Sai dai sam bana maida hankali garesa, dan ni salla ma sai mahifiyarmu tamun jan ido. Da girmana da hankalina nasha daukar azumi na karya batare da an sani ba, kawai dan inajin wata kaina sama can. A haka wata rana naji Akhi kazo ma da baba batun wai Miran Haysam mai jiran gadon karagar mulkin Shahan-shan ya baka zabin nema masa matar aure. Kai kuma kayi tunanin dubawa a cikin yarn gidanmu amma har yanzu baka gama yanke hukunci tsakanin ni da Hubba ba. Abinda ya girgizani shine, jin Abie kai tsaye ya furta ("Uhm-uhm Muhammad, ajiye maganar Bushirat gefe, bata jin magana, sakata a babban gida irin wannan zai iya zubar mana da kimar mu da nuna gazawar tarbiyyar da muka baku. Yarinyace mai kaudi da hange, ina tsoron al'amarinta. Akance a cikin yaya an fidda maka zakka, to tabbas Bushirat ni itace zakkata. Ka bashi Hubba kawai zamuyi alfaharin da ita") wannan bayani na Abbie ya tayarmu da hankali matuka. Dan ga koshi ga kwanan yunwa ne. Zama nai naita nazarin mafita, dan har wata zuciyar na bani shawarar kashe Hubba dan itace kawai matsalata.Naki karbar wannan shawarar, dan ko yaya ina matukar kaunar yan uwana, Haka na cigaba da saka ido a duk motsinka da na Abbie, sai dai shiru bakayi maganar ga Hubba ba balle iyayenmu mata. Dan duk da mahaifiyarmu ta rasu wajen haihuwar Jasrah bamu taba kukan rashin uwa ba ga matan babanmu, sun rikemu hannu biyu tamkar sune suka haifemu. A cikin dogon nazari dana bama kaina kwana biyu a samo mafita. Ranar na yini cikin farin ciki sosai dan inaji a raina na gama zama matar Shahan-shan. ALLAH kuwa ya yarjemin, dan a randa na gama yanke wanna shawara a bibiyar Akhi da nakeyi da Abbie na samu jin Akhi zai tura sako ga Miran Haysam ibn Abdul-majeed Aliy Qutb na zabin matar da ya nema.Tuni na garzaya na rubuta wasuka mai nutsuwa tare da saka hotunana a ciki da dama na tanada. Dakin Akhi na lallaba batare da sanin kowa ba, nai sa'a kuwa yana wajen karatu dan haka a shiga bincike dakinsa. Na samu nasarar gain hotunan Hubba da ya shirya tura masa cikin jin dadì na kwashesu na ajiye nawa da wasikar nan na sake sabon manne envelope din. Gudun a yanka ta tashi na kone hotunan Hubba a cikin toilet batare da sanin kowa ba…. Kamar yanda Akhi ya fada ya aika sakon Miran Haysam batare da sanin na canja hotuna ba. Kwana biyar tsakani sai ga masu neman aure sunzo. Hankalina ya tashi naita kaikawo da neman hanyar da zanji yaya akai amma ban samu ba. Dole na hakura har bakin suka tafi Abbie da Akhi suka shigo gidan. Cikin muryar damuwa najiyo Abbie na sanarma Ummu cewar maganar da sukayice ta taso, sai dai sabanin Hubba da su suka zaba shi yanzu ya aiko cewar Bushirat, harma sun rasa a ina ya sanni. Kokwanton da suka shiga yasa Akhi tashi da kansa zuwa masarauta dan tabbatar wa. Amma magana daya ce dai Bushirat ya zaba. Babu alamar damuwa akan fuskar Ummu tace ai duk kai da kaya mallakar wuyane ALLAH yasa haka shine mafi alkairi, dan itama dai batai magana bane kawai amma abin na damunta. Kar ace dan Hubba yarta ce aka tsallakeni aka bata alhalin nice babba. Oho ko dar banji da kalamanta ba, ni dai tunda burina ya cika damuwa ta kare. An shiga shirye-shiryen biki, yayinda niko keta nokewa kamar bana so dan harda kukana. Sai gashi su Abbie sun zubda makaman su sun koma lallashina. Da wanna salon nai amfani na cinye wasan akan bikina cikin kwanciyar hankali kowa na lallabani. An kawoni masarautar ruman masarauta mai abubuwan kawa da na birgewa. Duk da na tashi a gidanmu akwai kudi sai naga ashe muma yayan malam Shehu ne dukiya na'a inda take. Abu na farko da bai munba shine dole na zauna a kasan ikon Malikat Haseenat mai amsa sunan mahaifiya ga mijina, sai dai kuma babu yanda zanyi dan ta hakanne kawai zan samu yanda nake so. Na hakura na mika wuya anan dan koba komai tana nunamin kauna babu bambanci da yayanta. Abu na biyu shine Ashwaq a matsayin uwargidana wadda kowa ke jingina zamanta Malikat. Na shiga damuwa matuka a kanta tare da neman hanyoyin dakile al'amarin ta. Ban gama da itab ba aka auro Danish-Ara. Wannan shine mataki na farko da ya hada alakata da UWA. Dan tun sanda naji labarinta da dambarwar dake faruwa tsakaninta da Mammah a daura dammarar neman kusanci da ita. Nako sami nasara ta hanyar amintaccen hadimin Haysam, bayan na shaka masa makudan kudade amma ya nunamin har abada bazai ci amanar shugabansa ba, raina ya baci dan haka na koma barazana akan iyalansa, harma na aikata masa a aikace ta hanyar sakawa matarsa ta kawo min diyarsu daya da suka haifa sashena. Na tabbatar masa zan kasheta wanna shine dalilin amincemin badan yaso ba ya hadani da uwa. Na razana a ganin farko dana mata, dan mutumce mummunar gaske, da zaka iya rantsewa badaga yankin wanna kasa ta fito ba koma na dake zuciyata. A ranar batako kulani ba, hasalima korani tai wai ban shirya ba. Naji zafi amma na daure harda dukawa kasa ina bata hakuri akan laifin da ban san nayi ba. Bata dai kulanin ba haka na taso na taho. Na shiga damuwa dan tun daga wanna ranar bata sake yarda mun haduba har tsawon wata uku. A haduwa ta biyu ma dai bata kulanin ba sai da ta mula dan kanta sannan ta dubeni a kaskance da fadin, "Kije ki daina sallar la'asar dan kin shirya kasancewa da Uwa mai share kukan masu kuka". Na mata godiya na taso. Banyi wani tunani ba na fara bin dokarta har tsawon watanni uku. Kawai wata rana sai gata da dare ayam ta bullomin ta bango. Hankalina ya tashi na tsorata amma tsawar data mun ta sani nutsuwa. Cikin jan tsaki ta furta a haka zaki iya zama tare da uwa kina matsoraciya, Sosai na dake zuciyata wajen bata amsar ni ba matsoraciya bace. Ta sake maimaita min nima na maimaita mata nawa. Munyi haka har sau uku kafin ta kyalkyale da dariya da fadin, (Ke abokiyar tafiya ce. Mike tafe dake wajen uwa?). Cikin matukar farin ciki na qyara zama, na shiga zayyano mata haihuwa nake so, dan ina son zama Malikat bawai Zawjata-almilk ko Ameera kawai ba. Ni wannan matsayin duk yamin kankanta. dariya sosai ta shiga babbagawa har sai da na koa dan haushi amma dai na hakura na shanye. (Lallai ke abokiyar tafiya ce). Ta fada tana nunani har lokacin fuskarta da sauran daiyar. Murmushi nai mata cike da jin dad. Ta cigaba da fadin, (Nice da kaina na hana Haysam haihuwa saboda abinda uwarsa ke mun, idan tana takama ita Malikat ce dan ta haifi Miran mai jiran gado na shirya tabbatar mata komai a gidan nan sai da karfin ikona yake tabbata). Hakuri na dinga bata nidai, dan babban burina kawai bukatata ta biya nidai. Cikin tabe baki ta furta, (Ai kin wanke komai yar gari, indai zaki iya bin sharadinmu ki dauka kece Malikat a wannan karnin). Babu wani tunani nace na amince da duk wani sharadin ta tunma kan ta fada min su. Nan ma dariya tayi sosai kafin ta ajiye min wata takarda da koko mai dauke da jini wai a saka hannu da wannan jinin, itama zata saka wannan itace yarjejeniyar mu ta farko, Banji ko wani dar ba na saka ta saka. Ta bani daya ta dauki daya tana fadin, (Daga yau sunanki a wajenmu shine *_Ta-kurya_" ta kurya sa maza kurya kenan). Yar dariya nai ta farin ciki itama tana tayani. Ta wuce a ranar batace dani komai ba acewarta sai zama na biyu. Na matukar nustuwa a sati na uku da babu ita babu labarinta, dan haka na shiga bulayin nema. Harma a fiddla rai ranar kawai sai gata ayam ta kawo min ziyarar dare kamar wancan lokacin. Kafin nace komai ta tabbatar min doka ta biyu bayan suna dolene a duk sanda ta bayyana a gareni zansa gwiwuna kasa dan girmamawa a gareta, sunan da zan dinga kiranta da shi shine uwa. Nan ma babu musu na amince mata. Nanma dariya tayi kafin ta ajiye min kullin garin magani guda biyu. (Wannan sune maganin matsalarki Ta-kurya, daya zaki sha daya ki shayar da Miran Haysam. Ina mai tabbatar miki kafin watan ya mutu zaki samu ciki) na matukar kasancewa a farin ciki, sai kuma nai sansarakwai da ga baya na jeho mata tambayar to amma idan ya kasance wata a cikinsu nada ciki fa ko kuma muka samu cikin tare na haifi mace ita namiji?…✍️
Leave a Comment