Fulani 12


 12*


SIRLEEM POV. 


“Tun kwanan baya nai maka maganar, ya kamata mu fara hada lefe ba ka ce min komai ba”


Ya daga kansa ya kalli Mahaifiyarsa, kamin ya sake kallon Jarma wanda tun da suka gaisa be sake ce masa komai ba, sai kuma ya sake kallon mahaifiyarsa.


“Yarinyar da aka ce sai ta gama makaranta, idan mu ka ce za mu hada lefe yanzu ai mun yi sauri”


“Ba dole sai ta gama makaranta za ayi auren ba, ba zan iya jira har lokacin ba, idan muka hada komai mu kai musu su ce ba za su karba ba”


“Amman already an yi wannan alkawarin ai, be kamata mu tayar ba”


“To ni na tayar sai ya? Malam ka fara bada kudin da za a hada maka lefe kaji”


“To In-Sha-Allah”


Ya mike tsaye yana gyara rigarsa ya fice daga dakin. Da wani kallo mai kamar harara ta bishi har ya fice, sannan ta kalli Jarma. 


“Yaron nan idan ba mu yi da gaske ba, zai iya ba mu kunya”


Jarma yayi murmushi. 


“Karki ji komai Hajiya, ai yana da biyayya ba zai tsaba miki ba, yanzu matsalarmu guda biyu ce, Mai Martaba da kuma Shattima, kuma na sama mana mafita”


Hajiya ta mike tsaye duk da isar da take ji da kasaitarta ta isa bakin kofar ta saka mata key sannan ta dawo ta zauna. 


“Wace mafita ce?”


Jarma yayi murmushi a karo na biyu sannan ya ce. 


“Akwai wani gari can yamma da Katsina, garin wasu matsafa manyan arna, ance aikinsu kamar yanka wuka yake”


Hajiya ta dauke kai cike da kasaita. 


“Na saba jin irin wannan daga bakinka, sai mun gwada kuma mu ga ribar yar adan ce, ni yanzu masu yi da gaske na ke nema”


“Wannan karon masu yin da gaske ne Hajiya, domin su ba a musu aike sai dai mai sako ya isa da kansa, bari ki ji na fada miki a yadda aka ba ni tarihin garin basa bako, sai da sanin manyan gari gudun kar rayuwar bakon ta shiga hadari, wanda ba jinin garin ba baya zama garin. Sannan aikinsu kamar yankam wuka ne, sha yanzu magani yanzu, tun kan ki fadi bukatarki za su sanardar ke dalilin zuwanki da inda mafita take, ke bari na baki wani labari gaba daya jama'ar garin ba su yarda da wani abu wai cigaba ba, na zamani ko mai moriyarsa, in yanzu kika ce a kashe miki Shattima take za su masa harbin kasko su aika shi lahira, mayan yan siyasa da masu kudin garin nan ance can suke yada zango dan biyan bukatunsu”


Cike da gamsuwa Hajiya take kallon Jarma, yadda ya koda mata mutane da ace ba a gaske haka suke ba, zata iya yarda domin ta ji abunda ta dade tana nema. 


“A ina ka san su Jarma”


“Wani abokina Malam sa'idu ne ya fada min su, shi mutumen Bandalo ne wani kauye da ke Katsina, sai dai cirani yake a garin nan sai dai shi din amintaccen na ne”


“Mutumen da zai iya rike mana sirrinmu ne?”


“Idan ma zai tona mana asiri, sai dai ya fadi cewar ina nemawa yata maganin aure ne, domin na fada masa yata Nafisa ce take fama da bakaken aljannu da suka hana ta lafiya kuma suka hana ta, sai ya bani shawarar cewar da zan iya da naje can zan samu gani a take”


Murmushi mai kyau Hajiya tai tana kallon tv dakinta kamar da gaske hankalinta yana can. 


“Jarma sarki wayau”


“Hajiya kenan, wani ai be isa ya san sirrin mu ba, sai dai zuwan ne da kamar wuya a yanzu”


“Zuwa ba shi da wahala duk inda samu yake zan iya kai kaina, ba ni da kowa a katsina amman zan iya karyar zuwa wani gurin sai mu je can, matukar zan samu biyan bukatata Jarma, bana tsoron ratsa ko'ina zuciyata a bushe take”


“Zan neman takamaimen inda garin yake, da inda ya kamata mu sauka da kuma wanda zai magana jagora a cikin garin”


“Ka nemo Jarma amman ka tabbatar idan muka tafi ba zuwan banza za mu yi ba, za mu samo maganin ciwon mu”


“In-Sha-Allah”


Daga haka yai mata sallama ya fice daga dakin, ita kuma ta mike tsaye ta isa gaban windows dakinta tana kallon bayan gidan, ji take kamar ta runtse ido ta ganta a garin. 




FADIME POV. 


A yau ma sai da ta rubuta domin ta yi mafarkinsu, sai dai a yau mutum biyu tai mafarki da nai busar sarewar nan da kuma dayan da yake tsaye a gefensa dukansu sun bata baya ne. 

  Daga bukkatarta ta fito ta nufo inda Inna da Amo suke zaune suna maganar sarautar garin.


“Ni ina ganin kamar abun nan zai zama rigima ne, tun da duka yayan suna son sarautar fa”


Amo ta lashi baki da wata uwar tsaga da ta bata mata fuska tace. 


“Mu dai na mu ido, ban da rashin hadin kai, yayan uku ba za su hakura su bar wa daya ba? Wannan ai ba burgewa ba ce”


“Ni ma dai haka na ce”


Fadime na zuwa ta zauna kusa da mahaifiyarta ta kwanta jikinta. 


“To mage sarkin son jiki daga ni”


Da sauri Fadime ta dago ta kalli Inna wacce tai mata maganar. 


“Inna jiya ma sai da mage ta zo”


Hanzarin tashi tsaye Amo tai ta dauki kwayar danyen manshanunta ta dora saman kai. 


“To muka zamu bunni sai wada hali yai”


Bata ko tsaya jiran abunda Inna zata ce mata ba ta saka kai ta fice daga gidan da saurinta, har kusan karo su kai da wata makociyarsu wacce ta kunno kai cikin gidan rike da takarda hannunta. 


“Maraba da Nene”


“Na yalle dam Inna Fadime”


“Janfelen”


“Na sukkaɓe?”


“Janfelen, na wurinde?”


“Janfelen”


Ta zauna inda Amo ta tashi tana mikawa Fadime takardar hannunta. 


“Fadime karanta mini injiya minana Mai samari yak aiko min”


Fadime ta karbi takardar ta bude tana karanatawa, gaisuwa ce farko sai tambayar lafiyar mahaifiyarsa sannan ya sanar da ita sakon kudin da ya aiko mata dubu bakwai ta hanyar abokinsa, dan rani. 


“Munafwuki amman be ba ni komai ba, sai wasika, yalla ya aza babu me karanta min ita, bari naje yanzu na iske shi, mugun ba'adare”


Inna ta saka dariya ita da Fadime dan sun san halin Nene da kudi bata jin has. Nene ta fita daga gidan sai fada take ko sallama bata tsaya yi ma Inna ba. 


“Fadime tashi ki tahi rahe ki samo mana diyam”


A take ta bata fuska ta fara shura kafafuwanta.


“Inna ko hutawa ban yi ba, yanzu na farka daga bachi ai”


“Wallahi ina sa miki sanda yanzu, wa zai dauko ruwan ni?”


Ta tashi tana zabure zabure ta dauki tulun ruwa ta fice daga gidan, tana sanye da kayan fulani riga da zane cigiyarta a sake kanta kuma babu dankwali sai dan xaren kwaliya da suke daurawa akai ta raba gashinta gida biyu ko wane tsoro ya sauko bayanta. 

 A maimakon ta taje zafin da ta saba diban ruwa sai ta nufi babban gulbi garin da ba kowa yake zuwa can ba, saboda nisansa da kuma girman da gurbi yake da shi domin gulbi ne da ya hada mayan jihohin yanki. 

  Baki baki ya tsaya ta saka tulunta cikin ruwan ya cika ta cire ta aje, tana waige waige ko zata samu wanda zai dorata kasancewar safiya masu kamun kifi sun gama sun tafi sauran mutane kuma ba su fara hada hada a gurin ba. 


“Kai kado, ware”


Ta kwalawa wani bahaushen mutum da ta hango can nesa da ita. Amman ko kula ta be yi ba. Zaune tai a gurin tana ta wasa da ruwa da kafafuwanta, kamar ance saurara ki ji sai ta fara jiyo busar sarewar nan can nesa da manyan duwatsun da suke gefen gulbi, da sauri ta mike tsaye, ta fara waige waige sai kuma ta fara gudu tana nufar inda duwatsun suke, gudu take sosai kafafuwanta babu talkami domin a can ta baro su gurin da ta cika tulun, manyan duwatsu ne wanda hanyewa samannsu ma wani sabon aiki ne amman a haka ta rika dafa tana rarrafe kamar dole har ta haye sama, mikewa tai tsaye tana kallon mutumen da take hange a saman wani dutsen da ke can nesa da ita yana busar, jikinaa babu riga sai walki sanye a kugunsa, ba zata iya tantance fuskarsa ba domin baya ya bata kamar yadda ta saba mafarkinsa, wani irin gwalo ido tai waje ta hangame baki tana kallonsa, ya mata nisa sosai bare ta jira shi ya jita ko kuma ta jarasa kusa da shi, sai dai busar da yake ya karade ko'ina saboda yau a saman dutsen yai ta sabanin a da fa yake yinta a kasa ko a saman ice. 

Sai da ya gama busar sannan ya juyo ya fuskanci inda ya bawa baya, sai ya hango wata yarinyar da be tana gani ba ba kuma zai iya tantancewa ba tana kallon inda yake. Gangarawa yai ya sauka daga saman dutsen yana kallonsa tun tana hangoshi har ta daina ganinsa, a lokacin ne ita ma ta sauko da wani irin gudu kamar sabuwar mahaukaciya, tana isa gurin tulunta ta zubar da rabin ruwan ta dauki tulun ta dora a kai ta saka talkaminta ta nufi gida da sassafar zuciyarta na bugawa da karfi kamar zata fito daga kirjinta, numfashin ma daker take yinsa. Ta kasa yarda cewar abunda take gani a mafarki shi ta gani a zahiri, mutum ne ko aljanani? Miyasa yake zo mata a mafarkinta? Kuma a irin busar da ta ji yana yi a yau? Why ba shi da tufafi a jikinsa? Why yake busar a kusa da inda zata iya jinsa? Wanene shi? Duk tana bukatar wadannan amsoshin a yanzu. A bakin bukkar Inna ta aje tulun ta shige bukkarta, ta dauko littafinta ta fara rubutawa abun ya zame mata kamar wajibi. 



AA POV. 


Ba karamin dadi ya ji ba kudin da Nana ta saka masa a account, sai dai ko kadan hakan be bashi natsuwar ya cigaba da zama a unguwar ba, domin a ganinsa kamar ana dana masa tarko ne, line ma cire shi yai ya aje ya daina kira da shi ya dauko wani tsohon line sa ya saka a wayar. 

  Baya tafiyar da zai yi nisa da gidansu, ba dan komai ab sai dan ganin yake kamar idan ya bar unguwar za a iya kama shi, ita kanta Anti Rabi ta lura da rashin natsuwarsa har take ganin kamar ma ya fita tsoro.


“Idan kana jin zaman ka a nan ba zai yi ba, ka koma cikin gari gurin Kawo ka zauna na kwana biyu tukuna, duk da dai na ga kamar ba za a maka komai ba”


Ya sauke ajiyar zuciya ya kalleta. 


“Anti bayan faduwar da mu kai yarinyar ta sake ba ni kudi fa”


Anti ta zaro ido.


“Yaushe ka hadu da ita har ta baka kudi”


A dolen dolensa ya labarta mata yadda komai ya gudana da kuma irin tsoron da yake ji da kuma zargin an dana masa tarko da yake. 


“Ai Allah ya kara maka, AA wani irin mayen kudi ne kai? Sai ka jawa kanka fitina ko? So kake azo a kulle mu gaba daya kuma kasan ba mu da gata sai Allah, idan ma ba tarko ne ta dana maka ba, wata kila yarinyar sato kudin take ko kuma tana samo su ta hanyar da be dace ba, duk ranar da dubunta ya cika kai zata nuna”


A take AA ya ji kamar ya saki fitsari domin shi be kawowa kansa tunanin tana samun kudin ta hanyar da be kamata ba ne, sai yanzu da Anti ta fada. 


“Anty yanzu ya za ayi?”


“Ina na sanar maka? Ai kara ka koma can unguwar Waziri gurin Kawo Bala, idan ma wani abun za maka kara ace kana kusa da wani babba namiji”


Shiri yai ba dan yana so zai bi shawarar tata ba sai dan be da yadda zai yi, idan har sata take tabbas zata jefashi a cikin matsala kara ma ya koma unguwar da bata sani ba ko da ta zo gidan ta tararda baya nan. A take ya shiga cikin dakinsa ya hada kala biyar ya saka a jakarsa ya fito. 


“AA ka rika hakuri da rayuwa, rashi ba hauka ba ne, kai maraya ne kana ta neman jefa kanka a cikin matsala, kai kawarda idonka daga neman kudin nan dan Allah, idan kai hakuri sai ka same su cikin sauki, amman wannan bude idon da kake sai ka ga ka samu kudin ta hanyar da be dace ba, idan kai hakuri zaka samu duk abunda Allah ya rubuta maka cikin sauki”


Anti ta fada cike da damuwa, ta san kanenta ba irin yan iskan samarin nan ba ne, ba zai aikata wani abu dan neman kudin ba, amman tana tsoron shedan da zuciya, domin son kudin AA ba na wasa ba ne ita kanta ta sani.


“Shi ma wannan yana cikin rabo na ne Anti, yarinyar Allah ya kawo ta ne dan na yagi rabona”


“Ko kuma ka yagi rabon wahala ba, gashi nan ai ka fara boye boye ka kasa komawa aikinka, ka kasa natsuwa”


“Ke dai ke yi ta min addu'a kawai, Allah ya sa kar ta tona mana asiri, amman fa ko gobe ta bani sai na amsa”


“Idan an kama ka kar ma ka fadi sunana Wallahi”


Ta fada a fusace sannan ta shige dakinta, shi kuma yai murmushi ya fice daga gidan.




HAJIYA KARAMA POV. 


“Abun da kike yi be dace ba Zainab, taya Shattima zai yi magana ki musa masa, a iya tunani Shattima ko cewa yai ki dauki wuka ki yanka ni za ki iya”


Da mugun mamaki Zainab ta kalli Iya. 


“Iya kin san abunda kike fada kuwa?”


“Na sani, biyaya ya kama ace kina musu ta kowane hali kamin ki gina kanki”


“Ba ki wulakanci da akai miki ba ne”


“Wannan duk mai wucewa ne, ki koyo juriya da hakuri Zainab ki koyi kaskantarda kai sannan za ki samu nasara a komai, shakarata talatin a gidan nan na san ko waye Shattima kuma na san waye Ammy”


“Ba fa siyasa na ke ba, balle ace na nemi soyayyar wasu, abun da akai miki be kamata ba sam”


“Idan har kin ji zafin abun da aka min ya kamata ki fara kishin mahaifiyarki ki taya ta yakin da take, har mu ci nasara, kuma ki fara tunanin gina kanki, ban yarda ki yi ma Shattima rashin kunya ba domin shi din wata rana shugabanki ne”


“Na fara tunanin gina kai na Iya, tabbas zan yi aure na bar gidan nan”


Ta karasa tana kara zare manyan idanuwanta, Iya ta girgiza kai domin ba haka take son ji ba. Zainab ta mike tsaye ta isa gaban madubi inda wayarta take aje tana ringing ta dauka ta kai kunne. 


“Hello Ra'ees”


“Na'am Hajiya ya kike?”


“Lafiya Kalau ya ake ciki?”


“Komai kalau, MBS ne suka shigar da gasa, suna son hoto da zai dace da kamfaninsu a week din nan”


“Miye hadina da kamfanin MBS?”


“Sun bada damar photographers su turo hoton da suke ganin ya dace ya hau, idan kai nasara kai za su bawa ambassador na kamfanin na shekararar na  kuam kin san ba kana nan kudi za a samu ba”


“Zan yi tunani a kai”


“Na turo miki komai ta whatsapp idan kin hau za ki gani”


“Okay”


Cike da gadara ta aje wayar ta ja stool din madubin ta zauna tana kallon kanta. Iya ce ta zo bayanta ta tsaya tana kallon irin kyau da yarta take da shi.


“A yadda kike da kyau nan, kamata yai ace Sarki ne ya auri ki, ba mijin kawa ba”


“Mijin kawar nake so Iya, ba zan iya auren tsoho ba”


“Ni ma ban ce ki auri tsoho ba, amman kina iya auren mutumen da za ku tsufa kuna cin moriyarku”


“Shiyasa na ke son na auri Auwal ai....”


“Kashiiiii kin kasa ganewa”


“Babu fa abun da zan gane Iya, ni shi nake so kuma aurensa zan yi”


“Allah ya taimaka ya kai mu lokacin”


Iya ta fada fuskarta ba yabo ba fallasa, sai Zainab ta juyo ta kalleta tana murmushin jindadi. 


“Yauwa yanzu na ji magana, Amin thank you”


Dan murmushi kadan Iya tai mata sannan ta ce. 


“An jima ki samu Shattima ki ba shi hakuri”


“Zan yi hakan In-Sha-Allah”


Iya ta gyada mata kai sannan ta juya ta fice daga dakin. 




NANA POV. 


Tun da ta dawo school tana cikin dakinta bata fito ba sai la'asar, duk mutanen da ke zuwa gaisuwa sai dai su lekota ko kuma su tambayi lafiyarta Ammy tace musu tana ciki. 

  Tana fitowa daga dakinta ta nufi dakin Ammy, kai tsaye ta tura dakin ta shiga babu ko sallama, Shattima na zauna saman kujera Zainab na gefensa ita ma zaune, shigowarta yasa ya dago ya kalleta Zainab ta miko mata hannu. 


“Hey Baby zo nan...”


Nana ta karasa kusa da ita ta tsaya, dan ba zaman take son yi ba, Ammy dake bandaki take jiran ta fito. 


“Waya taba ki?”


“Ni bana son School bus tana kai ni makaranta”


Ta fada a shagwabe, tana dan satar kallon Shattima da yaki ya sake kallonta. Kamin Zainab tace komai Ammy ta fito daba bathroom din fuskarta jike da ruwa. Kallo daya tai ma Nana ta dauke kai ta karasa bakin gadonta ta zauna, sai Nana ta matsa kusa da gadon tana turo baki domin kwata kwata yau bata jidadin yadda aka kaita makarantar ba aka dawo da ita. 


“Ammy ni bana son school bus tana kai ni makaranta”


Kallonta kawai Ammy take. 


“Nana wai me yake damunki, tunanin ki dabam, ki duba yarinyar da take zuwa gyara dakin yaran can ba ta wuce warinki ba, amman aiki take zuwa nan, kina tunanin ita bata son gata nan? Ko bata son karatu? Me kika nema kika rasa ne? Tun da kika dawo school kika shige daki kika zauna duk masu shigowa sai tambayarki ake amman kin zauna a can kamar ba ki san rashi mu kai ba? Abinci ma ba ki fito kin ci ba, what is wrong with you?”


Ta yi shiru bata ce komai ba, domin bata da abun cewa ita dai karatun ne bata so. 


“Driver na ke son a daukar min”


“To ba za a dauka ba, kuma dole ki je makaranta, Islamiya ma yaushe rabonki da zuwa?”


Ammy ta amsa mata kai tsaye. Sai ta kara bata fuska. 


“Wallahi ba zan karatun ba, indai ba a daukar min driver ba ba zan sake zuwa makaranta ba”


“Idan kin yi karatun ni zan karu ko ke? Shashasha, ba ki son a fada miki gaskiya, kin fi son a barki ki yi ta hauka, kuma Wallahi kika ki zuwa makaranta sai na sa sarkin bulala ya zane miki jiki”


“Ai daman ba so na kike ba, shiyasa kika saka Baba Waziri ya kwashe komai na dakina....”


“Eh bana son ki, je ki nemi wata uwar da take son ki, idan ba ki bata min rai ba hankalinki ba zai kwanta ba, idan so kike na miki ba ki wata rana zan miki, duk ranar da bana raye sai ki nemi mai fada miki gaskiya ki rasa, sakaryar kawai nai kukan ciwon Mahaifinki na yi na ki...”


Ammy ta karasa cikin fada hawaye na sauko mata, da sauri ta tashi ta koma bandakin. Nana na juyowa Shattima ya wanke mata fuska da mari. 


“Stupid girl, wuce ki je ki hada kayanki yanzu nan driver zai kai ki gidan Baba Waziri”


Fashewa tai da kuka ta fice dakin da gudu. Zainab ta mike tsaye tana kallon yadda ran Shattima ya bace.


“Shattima ka rika daga mata kafa yarinya ce”


“Ta fara wuce gona da iri, abun ta gaba yake ba baya, i hate nonsense”


Ya amsa a fusace sannan shi ma ya fice daga dakin. Ko kadan Zainab bata jidadin abunda ya faru ba, amman ita tana kallon Nana da kurciya ne da kuma shagwaba, a gurin ta aje wayarta ta fice zuwa dakin Nana.

No comments

Powered by Blogger.