Fulani 9
*9
Har suka isa be ce mata komai ba ita ba ce masa ba. Haka yake a duk lokacin da suka hadu sai ya rasa abunda zai ce mata, na daya dai yana ganinta yarinya kuma yana ganin
kamar akwai kurciya a cikinta sosai wanda be dace ya fara firan soyayyah da ita ba, na biyu kuma baya jin yana mata son da ya wuce na gida daya wanda kusan sun zama yan'uwan juna. Ya rasa yadda zai yi Hajiya ta fahimce shi ya rasa da wane baki zai mata magana ta fahimci yarensa, idan ma bata son Mansura zai iya hakura da ita ya auri wata amman why Nana? Why? Har yanzu ya rasa dalilin Hajiya na son ya auri Nana.Yana fakin ya bude inda yake ajiyar kudi a mota ta dauko 5k ya mika mata, sai ta bude motar da sauri ta fita.
“Ka jira ni a nan”
Shi dai kallonta kawai yai, daman can ya dade da ayyanawa a ransa Nana bata da hankali kamar sauran mutane wata kila kuma gata ne yai mata yawa. Jinginar da kansa yai jikin kujerar motar ya ciro wayarsa ya kamo hoton Mansura yana kallo.
Murmushi yai yana yinta sosai musamman idan ya tuna irin yadda suke mu'alama da kuma yadda take son shige masa jiki, yadda take yabon daukakarsa da kyausa, gashi ta iya drees tana son duk wani abu da yake so, tana gudun bacin ransa, idan wani abun ya same shi hankalinta zai tashi sosai, duk inda yake tana nan manne da shi, wannan dalilin yasa mutane da yawa suka san alakarsu, kasancewar fitattacen mawaki kuma mai tashe duk wani motsi nasa yan media da yan jaridu sun saka masa ido.
Cikin jindadi Nana ta shiga cikin restaurant din, kai tsaye ta wuce reception sai rabon ido take ko zata ga AA. Tsaye tai tana a gurin ta rasa abun da zata ce.
“Hajiya me kike so?”
“Wannan yaron nake nema, wani yaro fari dogo ba sosai ba be da jiki ana mishi lakani da Sardauna”
“Okay kwana biyu be zo ba, ya samu hadari ne ”
Ta dan yi shiru kamin ta sake kallon mai bata amsar ta ce.
“Dan Allah kana da number shi ka kira shi?”
“Okay”
“Yauwa Thank You”
A take ya ciro wayarsa yai dialing number AA ba da wani dade tana ringing ba yai picking.
“Hello Jafar”
“Sardauna wata yarinya ce ta zo nemanka yanzu”
Saurdauna ya tsaya daga tafiyar da yake yana mamaki gabansa kuma na mugun faduwa.
“Wata yarinya? Wacece?”
Jafar ya mika mata wayar.
“Hello”
Yana jin muryarta ya gane ta.
“Nana”
“Na'am na zo baka nan, kana ina ne?”
“Miyasa kika tambaya? Kama ni za ayi?”
“A a ba abunda za a maka, kawai na zo na ji ya jikinka ne, kuma na kawo maka kudi”
“Kudi....”
Dan murmushi yai sai yaji wani karfi da kuzari suna ratsarsa, sai dai tunawa da wani abu yasa tsoro ya kama shi, what if plan ne?
“Nana bana kusa na je Kano, amman idan da gaske kike ki bawa Jafar kudin ya saka min a account”
“To amman yaushe zaka dawo?”
“Sai next week”
“To zan karbi number ka na kira ka da wayar Hajiya Karama ko wata”
“A a ban yarda ba”
Ji yake kamar zata yi amfanin da number na sa ne a gano shi.
“To ka dawo da wuri ka ji”
“To”
“Zan aje wayar kuma zan bashi kudi ya saka maka a account 20k ne”
“Na gode”
Ya mikawa Jafar wayar.
“Jafar zata baka 20 ka saka min account 18k sai ka dauki 2k din”
“Ok ba matsala na gode”
Ta ciro kudin a cikin skirt dinta ta mika masa, sannan ta ba shi 5k din hannunta.
“Ka saka mishi wannan, wannan ka hada min takeaway ka dauki canjin”
Da mamaki ya karbi kudin ta dayan bangaren kuma yana jindadin canjin da tace ya dauka. Cikin sauri ya hada mata komai jalof da naman kaza da lemu da ruwa ya saka mata a leda ya mika mata.
“Please ka ce ya dawo soon ka ji?”
“To zan fada masa na gode Allah ya tsare”
Kai ta gyada masa ta fice cikin rashin jindadin ganin AA da ba tai ba. Sirleem na zaune cikin motar yana jiranta har ta iso ta bude motar ta shiga. Gaba jin tai kamar ta fasa kuka, yana ganinta ya san yanayinta ya canja gashi ta dade a ciki, sai dai be damu ya tambaye ta yai reverse suka dauki hanyar gida.
Da farko AA yai nufi zuwa restaurant din daga can ya tambayi ko ta zo nemansa, sai dai ganin kiranta da wayar abokinsa yasa ya fasa zuwa kuma ya ji duk be da natsuwa, hakan yasa na koma gida jikinsa na ta fada masa plan aka shirya masa wata kila ma za a fara bibiyar line.
Sai da Jafar ya tashi daga aikin sannan ya bawa mai POS din daje kusa da restaurant din ya saka ma AA 18k a account dinsa, AA na zaune yana wanki trouser dinsa wayarsa tai kara ta sauri ya dauka ya duba dan tun dazun yake jiran yaji kudin idan har da gaske ne zai ga kudin, idan kuma plan ne zai gane. Ganin kudin yasa shi murmushi a dubiya be da abun so kamar kudi, ko da Plan ne ake hada masa tun da kudin sun shigo shi be da matsala. Wani irin farinciki ne ya baibaiye shi kamar an masa albishir da gafara. Yana son ya kira Jafar din yai masa tambayoyi kuma tana jin tsoron kar ya kira a bibiyi line sa.
Kamar yadda suka zo dazu, haka ma gurin komawa babu wanda yace da wani uffan, Nana gaba daya mood dinta ya canja titi kawai take kallo, Sirleem kuma driving yake yana ta tunanin yadda zai kwashe da Mansura idan Hajiya ta hana shi aurenta, bayan irin alkawarin da yai mata. Yana ji a jikinsa Hajiya ba zata yarda ya aureta ba ko da bayan ya auri Nana saboda ta tsani Mansura sosai.
After yayi parking Nana ta bude motar ta fita, Bangaren Hajiya ta nufa ta shiga har cikin falon ta bata yi magana da kowa ba ta bude takeaway ta fara ci. Su ma yayyenta kuma kanen Sirleem babu wanda yace da ita komai tun da suka kalleta suka dauke kai ba su sake kallon inda take ba sai da Sirleem ya shigo. Yana kallon Nana ya dauke kai ya nufi corridor da zai sada shi da bangaren Hajiya.
“Bana son duk wani abu da za ace sai an ci, kin san yanzu wani babban aiki ne na ce zan shirya wani abu kuma na basu shi ya ci, ade samu samu wata hanyar, ki mayar masa da abunsa, ke fada masa yai masa wani abun da zai iya samunsa a can inda yake ba wai sai ya ci ba”
“To za ayi haka ranki ya dade, to shi na Mai Martaba fa?”
“Shi be da matsala zan iya dafa wani abun ya saka masa”
“To Hajiya, amman Hajiya zai na ke ganin kamar Talba be da farin jini a masautar nan kamar yadda Shattima yake da shi, anya ba sai an tashi tsaye ba?”
Hajiya ta yi murmushi tana kallon Talatu har na tsawon mintuna biyar sannan ta ce.
“Shattima ne ya hana shi tashe, ssboda Shattima ne babba shiyasa komai shi ake wakiltawa, kuma kin san mahaifiyarsa ba zata bar shi haka nan ba, da shi da duk son da Mai Martaba yake musu ai bana banza bane har ita uwar ta su, ba jin maganar kowa sai tasa komai sai ita, shiyasa na ke son nuna mata wannan karon bokanta sai ta yi kuka da hawayenta, mulkin mallakar da tai min a baya ba zai yiyu ba a yanzu, tana ji tana gani Sirleem zai auri danta Talba kuma ya hau sarautar na bayan na ta yaran sun lalace komai ya koma karkashin iko na”
Hajiya Talatu ta daga kai.
“Lallai kam, na san Jarma da Ammy sun fi kowa farinciki da ciwon Mai Martaba, saboda ita tana ganin danta za a dora Jarma kuma yana ganin shi zai gaji kujerar babansu kuma kujerar dan'uwansa”
Hajiya ta yi murmushi.
“Sun wuni da shiri mu kuma mun kwana da shi.... ”
Kwankwaso kofar dakin da Sirleem yai ne yasa gaba daya hankalinsu ya koma can, Hajiya ta jefawa Hajiya Talatu kullin hannunta ta gyara zamanta. Talatu kuma ta saka komai a jakarta sannan Hajiya ta ce.
“Waye?”
“Ni ne”
Sirleem ya amsa cike da mamakin rufe kofar da Hajiya tai, abunda be taba gani ba indai tana cikin dakin bata rufewa sai idan fita za tai. Hajiya Talatu ta mike tsaye ta murda makulli ta bude masa kofar.
Why dan mahaifiyarsa za tai magana da Matar kanen mijinta, sai ta rufe kofar? Dan tsayawa yai kallon Talatu kamin ya shigo cikin dakin, ya nufi inda mahaifiyarsa take ya zauna kasa.
“Ya akai?”
Ta tambaya kamar ba ta jidadin shigowarsa ba, shi ma dai ba zai iya fadar abunda ya kawo shi ba kawai ya shigo ne.
“Na je na gaishe da Nana”
“That's good, Allah yai maka albarka, ina jindadin yadda kake bin umarnina Sirleem, zan fi kowa farinciki idan ka auri Nana kuma ka gama cika min burina”
Be ce komai ba ya mike tsaye yana satar kallon Hajiya Talatu ya fice daga dakinta Hajiya Talatu tana shi masa albarka.
“Ai Sirleem akwai biyayya Allah dai yai albarka”
Sai ya fice ya rufo dakin sannan Hajiya Talatu ta dawo kusa da Hajiya Babba tana fadin.
“Wai yanzu ya daina maganar Mansurar ne?”
Da sauri Hajiya ta daga mata hannu alamar tai shiru tana kallon kofar, sannan tai mata alama da ta dauki jakarta ta fice. Kai Hajiya Talatu ta gyada ta dauki jakarta tana mata sallama.
“To Ranki ya dade zan wuce sai kuma wani lokacin”
“To Talatu na gode na ziyara”
Hajiya ta amsa mata tana murmushi sannan Talatu ta fice daga dakin.
SHATTIMA POV.
After Sirleem ya fice Ammy ta ce.
“Tun daga lokacin da Sirleem ya nuna yana son Nana sai ka yanke alaka da shi, duk wani shiri da kuke sai ka maida shi gefe ka aje”
“Ammy ai yanzu ni surikinsa ne ko? Ya kamata na yi respecting kaina shine kawai”
Kallonsa kawai Ammy take, sai yai murmushi kadan ya shafa kansa.
“Tsakani da Allah Mama bana son Nana ta auri mutunen nan, not because yana mawaki, har da mahaifiyarsa kin fi kowa sanin yadda ta tsane mu a can baya then why yanzu zata bar danta ya auri Nana? A yadda na lura kamar shi kansa Sirleem din baya son auren”
“Bana tunanin Hajiya Balki zata cilasta Sirleem ya zo Nana? To akan wane dalili? Miyasa za tai haka? Kamin yanzu Sirleem da Nana suna shiri sosai wata kila hakan ne yasa soyayya ta shiga tsakaninsu, yanzu kuma ka kore mata kunne ta fara cewa bata son shi bayan a gaban kowa ta ce shi take so”
“Nana bata da wayon sanin irin mijin da ya kamata ta aura”
“Ya kake so na yi Shattima? Na ce ba za ayi auren ba? So kake a fara cewa ina jindadin ciwon Mai Martaba ne? Daman can ana fadar ni nake mulkin masauratar nan so kake hakan ya tabbata?”
Wani dogon numfashi yaja ya sauke a hankali. Ya kasa cewa komai.
“Kai ma ya kamata ka fara tunanin aure yanzu”
“Akwai wacce zata so ne Ammy?”
“Akwai da yawa, kuma zaka samu In-Sha-Allah, mun yi magana da Waziri, yace kamata yai aje can wata uwa duniyar a dauko samo wata matar ko yar ruga ce”
“Karka a cuci yar mutane kamin a aura mata ni a barta ta san ko kaddarata dan Allah”
Ammy bata ce masa komai ba, shi ma din be shirya yin wata maganar ba hakan yasa ya mike tsaye ya fice daga dakin. A backyard ya fito ya tsaya yana ta kallon harabar gidan, zuciyarsa cike da tunani kala kala cikin har da makomarsu idan aka rasa Mai Martaba, and me ke damun mahaifinsa shi ya fi komai tsaya masa a rai, why baya son haske? Why baya son mutane?
Jin an dafashi ne yasa ya juyo a hankali sai suka yi ido hudu da Zainab, ta sakar masa murmushi tana tsosar mintin dake bakinta.
“Me kake tunani?”
“Ba komai”
Ya amsa mata yana juyawa fuskarsa ba yabo ba fallasa.
“Na binciko wani kauye, BANDALO a cikin Katsina yake, ba a san mutanen kauye sosai ba, ma fi yawa mutanen kauye Fulani ne makiyaya, sai dai ance akwai wasu Kabilu da yare kala kala a kusa da su, so i decided zan je can na yi aikina”
Juyowa yai ya kalleta.
“Hajiya tun daga Yola ki je har Katsina?”
“Yeah aiki ne ai you know”
“Yeah amman kasar na cikin matsala tsaro kin sani ai”
“Okay zan yi magana da Ammy sai ta ba ni police su raka ni”
Ya dan tabe baki.
“Fine Allah ya bada sa'a”
“Amin excuse me....”
Ta fada tana kokarin barin gurin rike da wayarta dake ring. Dakinta ta dawo ta manne da wayar a kunneta.
“Hey Baby ya kake?”
“Lafiya kalau, ya gidan... ”
Sun dauki kusan thirty minutes suna waya da Auwal mijin kawarta kamin daga karshe su yi sallama cike da saukin juna. Zaune ta tashi tana wani irin shu'umin murmushi, ita kanta bata jin son Namiji kamar yadda take son Auwal ba, ko Maybe saboda ita ta nemo shi da kanta ko kuma saboda yana da kyau ne? Or maybe saboda ya waye kamar yadda take son namiji? Domin after ta karbi Number shi kamin ta kira shi shi ya fara kiranta suka gaisa ina ya samu number ta shine abunda bata taba sani ba har yau, kuma bata tambaye shi ba.
Tashi tai ta fita daga dakin zuwa dakin Iya, ta tararda falonta babu kowa sai tv hakan yasa ta wuce dakinta kai tsaye, sai ta same ta zaune saman gado tana kokarin falla goro ta ci. Kusa da ita ta zauna cike da shauki.
“Iya gobe surukin ki zai fara shigowa masarautar nan ya mu gaisa me kike ganin ya dace na masa?”
Iya ta kalleta kallo na tsab domin har hanjin cikinta tana gani da yadda jini ke tafiya a jikinta.
“Duk abunda kika shirya masa a dole ya so, wa zai ki abun masarautar nan?”
Ta saka duka hannayenta biyu ta dafa mahaifiyarta cike da nishadi.
“Na sani, kawai na rasa da me ya kamata na tarbe shi ne, Wallahi ina son shi sosai”
Iya ta yi murmushi tana dauke kai daga barin kallon yar tata.
“Zainab har yanzu ba ki fara kwadayin aure a cikin masarautar nan ba?”
“Wannan karon da gaske aure zan yi, ba zan ma dauki lokaci ba”
Ganin Zainab bata gane inda ta dosa ba yasa bata sake ce mata komai ba akan hakan ba.
“Ba kya jin kunyar ki auri mijin kawarki? Ba ki son ki auri mijinki wai mijin wata? Ba ki so mijinki ya rayu da yayanki kawai? Kin fi son ki rayu da wasu yaya?”
Zainab ta mata kallon Mamaki.
“Ita fa ta saka mijin nan na gani na ji ya min to miye nawa a ciki? Ko matansa 99 da tara ni zan iya zama ta 100 domin ya cika yadda na ke son mijina ya kasance, ba ruwana da matarsa da yayansa, rayuwata zan yi da dabam ita ma nata rayuwar dabam”
Iya ta tabe baki tana kallonta kamin ta girgiza kai.
“Har yanzu ba ki da hankali Zainab tun da baki fara tunanin gina kanki ba”
Ba ta ko jira iya ta karasa ba ta mike tsaye ta fice daga dakin, daman can indai irin wannan maganar ce basa jituwa da iya. Da kallo Iya ta bita har ta fice.
“Ba ki da mijin da ya wuce Shattima Zainab, ba zan yi zaman banza na kararda shekaruna a masarautar a banza ba, ina burin zama sukukar Sarki kuma ina da burin na juya masarautar nan ta yadda na ke so da bakina da kuma ikonki, dole ne Mai Martaba ya kwanta dama, Shattima ya hau mulki ki kuma ki zama matarsa Sarki, da ke kadai Shattima zai rayu, ke kadai sa ki haifa masa yaya, daga lokacin ne komai zai dawo karkashin iko na Ammy da kowa ya dawo bin umarnina, idan har kika dage sai kin auri mijin kawarki to sai dai ke da kawarki ku rasa shi...”
Babu wasa a kalamanta kamar yadda fuskarta ta nuna, domin gaba daya ranta a bace yake da maganar da yarta ta zo mata da ita, tana ta nuna mata inda gabas take amman ta ki ta gane.
Mikewa tai tsaye ta nufi kofar dakin ta rufe da makulli ta dawo can karshen dakin ta hanye wata katuwar dorowa dake gurin ta daga carpet din ta fara tonon kasar gurin, ko ina na dakin tiles ne sai gurin ne kadai ke da masa hakan yasa ta rufe shi da carpet kuma ta dora durowa sama.
Sai da ta haka dan madaidacin rame sannan ta mike tsaye ta koma karkashin gadonta ta janyo wata kwarya ta bude kwayar ta dauko wani abu mai kamar mutun amman an nade da shi da zaren makauniya, har da yan tsorayensa, ta dauko wata karamar wuka, sannan ta dauko lighter ta dawo gurin ramen ta tara abun ta kunna lighter ta fara kara shi, a take Luna dake dakinsu ta kwala wani irin ihu ta ta fara fisge fisge tana kuka iya karfinta. Iya ta yi saurin janyewa hakan yasa tai shiru sai kuma Iya ta sake karata a take ta kara falla ihun tana kuka. Kashe lighter Iya tai ta tara abun ta saka wuka ta janka gurin wuya, ta cikin zaren jini ya fara zuba har ya bata mata hannu, sai da ta bari jinin ya tsare tsab sannan ta rufe kasar ta gyara komai yadda yake, sannan ta shiga bandaki ta wanke hannunta ta wanke abun da ta wanke ta warware zare ta saka a cikin masai tai bi shi da ruwa, sannan ta dawo karkashin gadon ta dauko wani kwano mai murfi ta bude ta saka abun da ta yanke mai lamniya kamar nama kuma ba nama ba ta saka cikin kwanon ta rufe ta mike tsaye ta maida kwanon mazauninsa sannan ta mike tsaye ta nufi kofar ta bude ta fita ta saka makullin daga waje sannan ta nufi bangaren Ammy.
FALMATA POV.
Ba karamin dadi Tumba ta ji ba, da Falmata ta fada mata cewar sun ce sun hakura har ma ta yi musu aikin.
Sai da Falmata tai karyar sannan ta fara tunanin idan wata yai ina za ta samu kudin da zata bawa Tumba? Anya wannan karyar zata haifar da da mai ido kuwa? Ko dai ta sake jefa kanta cikin wata matsalar ne? Idan kuma ta ce bata koma aikin ba za ta iya mata wani shekarin. A take ta fara tunanin ko dai ta koma ta ba su hakuri ko za su hakura? Idan ma ta je ba su hakura ba ya za ta yi? A take idonta ya cika da kwalla ga yunwa sai cin cikinta take domin tun abincin da ta ci a gidansu Khadija da safe bata sake saka komai a cikinta ba har dare.
Duk kiran da Tumba take mata ba ta ji har sai da ta dauki abu ta jefa mata, ba dan tunanin da take kadai ba har da rashin da take fama da shi a yanzu wanda har sai anyi magana kusa da kunneta ko kuma an daga murya sannan take ji. Zabura tai ta kalli Tumba hankalinta a tashe idonta kamar za su fito jikinta sai rawa yake.
“Tashi ki fita ana miki sallama na ce”
Ta fada da karfi, da sauri Falmata ta tashi ta shiga daki ta dauko Hijabinta ta saka ta fita waje. Umar ne natsentsen saurayi kuma dan wanka, ba mai kudi ba ne amman yana da rufi asiri domin yana tsaron shagon wani mai saida kayan shaddodi a ciki yake samun na lalurarsa. Dukan samari da suke zuwa gurin Falmata tana fitowa ne kawai saboda Tumba tana matsa mata ta fito din dan ta samo abun hannunsu wasu kuma saboda suna kunna mata wakar M2 amman ban da Umar Falmata tana son umar sosai ba dan wani abu na shi ba ba dan kuma yana kunna mata wakar Sirleem M2 ba, no so ne dai na Allah.
Murmushi tai masa wanda ta saba masa a duk lokacin da ta fito sai ya kunna wayarsa ya haska fuskarka duk da kasancewar akwai hasken gulob a gurin. A take na sa murmushin ya kushe.
“Falmata me ya samu fuskarki?”
Bakinsa da ke motsi kawai take kallo, kunnuwanta sun kasa jiyo mata muryar masoyinta a yau. A take ta rufe bakinta ta fara kuka marar sauti hakan kuma ba karamin daga masa hankali yai ba.
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un me ya same ki?”
Nan ma bata ji me yace ba amman tabbas magana yake.
“Bana iya jin komai Umar sai idan ka yi magana kwarai ko kuma ka yi kusa da kunnena... ”
Ta fada cikin kuka, sai ya nuna mata dakalin dake kofar gidan alamar ta zauna, after ta zauna shi ma ya zauna yana kallonta cike da tausayawa.
“Me ya same ki?”
Ya fada yana kai bakinsa kusa da kunneta. Bata boye masa komai ba tun daga kan korar har dukan ta karasa tana kuka. Shi ma sai da idonsa ya cika da kwalla, sosai yake jin tausayinta da ace yana da hali a yanzu tabbas aureta zai yi ta raba ta da gidan ta huta, sai dai be da halin aure yanzu domin shi da iyayensa duka talakawa ne kusan ma shi yake taimakon iyayensa kuma dan abun da yake samu ba wani mai yawa ne sosai ba.
Ajiyar zuciya ya sauke ya shiga gallery wayarsa ta kamo mata wakar Sirleem dan ya san ita ce kadai zata saka ta yin shiru a yanzu. Yana mika mata wayar ya saka hannunsa aljihu ya ciro airpiece dinsa ya mika mata, sai ta share hawayenta ta karba ta saka a kunne tana kallon wakar hawaye na sauko mata. Ta dauki lokaci kamin hankalinta ya tafi gurin wakar har tai murmushi.
Yau be bata kudi ba sai siyayyar kayan marmarin da yai mata, wanda ta saka ran ya bata kudin ta cire wani abu ta siye gari da suga ta sha domin yunwar ta matsa mata fiye da kima a yau. A gaban Tumba ta aje kayan marmarin da ya bata Tumba tai mata na kurame wai ta dauki ayaba daya lemu daya, sai Tumba tai mata alama da ina kudi?
“Be ba ni ba”
Tumba bata ce komai ba ta dauki ledar ta shige daki. Falmata ta koma gefe ta zauna tana ci, babu komai a zuciyarta sai tunanin mahaifiyarta.
__________
Hope dai ba ku manta da Fadime ba ta kauye? Na ga kamar za ku rikice ne shiyasa na raba muku labarin biyu.
Leave a Comment