Yar Aikin Karuwai Book 2 page 16-20


 🌼'YAR AIKIN KARUWAI 2🌼

               MATAFIYA


BOOK 2



               16-20



MASU AUDIO DUK WACCE TA JUYA MIN NOVEL ZUWA AUDIO WLH TA CI HAKKINA NA BAR KO WAYE DA ALLAH

NA RIGADA NA SIYAR DA NOVEL DINA.




Official


By

AsmaBaffa



SADAUKARWA NE GA 

ZAINAB USMAN





*👭GARKUWAR MATA👭*

*Ina Matan suke? mata na ke kira ba muna mata ba, duk wacce ta amsa sunanta na 'Ya mace ta na tattalin kanta da lafiyarta, Mace 'yar gayu ce  mace 'yar kwalisa ce, kuma aka ce mace bata tsufa 💯muddin tana gyara kanta, duk yawan shekarunki idan kina tattalin kanki za ki ci zamaninki sannan ki ce na wasu, Ka da na cika ku da surutu GARUWAR MATA👭 ta zo muku da ingantattun magungun mata masu kyau da inganci🌿🌿🌴🌴 Mussaman maganin  gyaran Nono da mafi akasarin Mata suke da damuwa da matsalarsa, to shakuruminki 'Yar uwa muna da sahihin maganin gyaran nono da zai dawo miki da martabarki duk lalacewarsa muddin ki ka yi amfani da maganinmu  za ki yi godiya,  sannan muna sayar da maganin sanyi mai kyau wanda yake kassaara kowane irin sanyi na fili da 'boye, akwai supplement gangariya masu kyau irin wadanda ba su da matsala sai dai su gyara garkuwar jiki.  Muna kuma sayar da turarukan wuta humra perfumes sabulan gyaran fata dilka   kayan gyaran jiki na amare dahuwar kaza da ciccibi zuma gumba garin daka tsumi turaran tsuguno miski da duk nau'in  abubuwan da suke kankaro da martabar duk wata 'Ya mace! GARKUWAR MATA 👭👭 fatan mu shine mu bada gudumuwa domin samun zaman lafiya a zamantakewa, Muna garin  Kano amma muna tura kayanmu kowane gari cikin farashi mai sauki da rahusa! kuma muna bada sari cikin girma da mutunci*

*GA*

*Kadan daga  cikin  abubuwan da muke sayarwa*

Rage tumbi💯

Nono💯

Sanyi💯

Karin kiba💯

girmar hips💯

Ni'ima💯

Sabulai💯 

Humra💯

Turarukan wuta💯

Matsi💯

Miski💯

Dilka💯

Gangariyar Supplement din da zai mayar dake tauraruwar mace fatarki ta yi luwai kamar kina rayuwa a turai😀 ke dai 'Yar kada ki yi kasa  guiwa cikin saukin farashi kalilan za ki kankaro da martabarki

GARKUWAR MATA👭 Tana maraba da masu siyan daya da kuma masu bukatar sari

DOMIN NEMAN K'ARIN BAYANI

*08089965176*

*07084653262*




PAGE NAKU NE 

BINTA UMAR ABBALE

MRS ALEEYU

MOM SANI

SALMA

AMMEY LAYLAH

INDO

LA REINA

BELLOMARYAM

MARYAMBELLO

AMATULLAH KAMSHI

A'EESHA

AISHA S MAIBANKEEY

MAMA GEE

ZAINAB HASSAN

RUKAYYA ABDULKADIR







     Sultana da Nasira gulma suke yi Sultana tace kinji wai me yasa aka saki Mami nima a wajen Kawayen Mami naji suna gulmar da naje gidan Hajiya Suwaiba wai mijin da Mamin mu ta aura Hariji ne shine tace sai ya saketa,Nasira ta rike baki tace shi yasa kwana kadan aka sako Mana Mami duk ta rame tayi wani iri,Auta ne ya shigo palon daga wajen Nawwar direct gida ya dawo yaji ma hirar su Sultana amma ya nuna ma bai ji ba,yace wai me aka dafa ne? baka ci a gidan Yaya ba? matarsa tana da cikin zanci abincinta taje garin girki ta zuba yawu a cikin abinci,dariya sukayi Wise ce ta shigo sanye cikin Less gown tayi Matukar kyau dinkin manyan Mata sai walwali take yi,Aunty Ina yini dukkansu Suka gaisheta Banda Auta shi ai tsohuwar budurwarsa ce sai Yace Wise dama kina gari,ban sani ba dan banzan yaro ni kake wa wannan Iskancin taso muje dama aikenka zanyi ,Fuska ya bata yace da girman nawa amma muje zanje ya zanyi nazo a karami,Wise tana gaba yana binta a baya,Auta yaga mazaunai yace Ki tsaya a bayana mana ya za ayi ki wuce gaba Babu hijab Ni ba muharraminki bane Yana Kunkuni ya wuce gaban Wise Yana cewa za a lalata mutum,Wise a ranta tace inama banyi aure ba da yaron nan ya raina Kansa a fili tace Auta Ina da kanwa in kana so,akai kasuwa Ni ba a min tallan mace sai dai na gani nace tayi min ko Ido Kika fini,Papa ya aureki ni na auri kanwarki a gidanku zamu kare dama Miracle tana da kanwa ne to dama dama,Wise tayi dariya Kawai Suka shiga har bangarenta ko Ina sai kamshi ke tashi Yana sheki,Nawaf ya zauna a kujera yace su Papa an samu sabon jini ko kunya ya aureta uhmm Papa anji kunya.

  Wise ce ta fito tace yawwa kaga Nawaf Kai ka waye ba ruwanka magani Zan gwada idan na gaske ne please,Auta yace wanne irin maganin karfa kiyi tsafi dani,Wise tace a'a maganin ciwon Kai ne,Kuma sai a gwada a kaina,tace please babu yaron da Zan gwada da shi sai kai ni da Kai fa 5 and 6 ne karka fadawa kowa kaji,yace to ba Alheri bane duk abinda akace Kar a fada to ba abin kirki bane,Kash Auta  Wai mene haka Kawai rikewa zakayi a hannunka abinda kaji ka fada min,Auta yace kawo ya Mika Mata Hannu,ta Mika Masa wani Abu Kamar tsohon nama bushashe maganin mata ne idan me kyau ne da maza ake gwadawa ta bawa Nawaf, Nawaf ya rike magani nan take Antena ta mike ya Fara hada zufa ya Mika Mata abinta da sauri yace Yana Yi na gaske ne Papa ya shiga Uku,Dariya Wise tayi tace ka San na mene wai? baki ya tabe yace ke Kika sani me magani dai taci kudinta Yana yi sosai ya furta Yana Sosa Kai,tace ai ba a gama ba ga wannan rike,ya karba yaji baiji komai ba yace baya Yi wannan na karya ne,Wise tace bana son karya yace ko a Bude Miki ne ki gani Zan Miki karya ne mufa duk mun san abin nan Kuna rainani  , ya tashi ya fice ball dinsa ya tafi.

     Wise Kuwa Su star ta Kira tace na gaske ne Yana yi Auta ya gwada min,Star tace gaskiya Baki da mutunci yaron mutane zaki bawa suna dariya Wise tace ai Auta Yana da hankali babu me Jin zancen.


    Washe gari dukkan su Cele makara sukayi,Ahsan ya Dade da tashi Yana ta Kiran Maheerah zaiyi Sallah amma Shuru lokacin Cele tana saman Sallaya tana Azkhar ta mike tare da Fitowa tazo Palo inda yake,hannunsa ta rike ya mike Yana duru duru tana jansa har toilet sannan taje Daya bedroom din ta samu Maheerah tana bacci,Tsaki Cele ta ja tare da tashinta tana bubbuga bayanta da kyar ta tashi,hannunta ta fisgo tace kizo ki kula da mijinki Yar iska idan kwana da namijj ne kin iya burinki a sa Miki itace a fadama ta jawo Maheera ta kaita toilet tare da nuna Mata Ahsan ta kula da shi, Maheerah a gabansa ta tsaya tana yatsina Masa Fuska tana galla Masa harara tana masa kallon banza,Hannu takai Wai zata mare shi sai ta fa ta Kai Masa naushi nan ma ta fasa wata uwar harara ta Masa tare da jansa tana Jin haushinsa har yayi wanka da brush tare da abubuwan bukata,Alwala yayi Suka fito ta shimfida Masa Sallaya tana zabga masa uwar harara sannan ta jawo shi saman Sallayar tana kukan karya Noorul Qalb kayi hakuri mutumin kirki da kai an jarabceka da wannan Lalaura  gwalo ta Masa ta yatsina fuska ta sake Kai Masa Mari sai ta janye hannunta ta zazzage shi kasa kasa, Sallah ya tayar bayan ya Mata godiya, itama wanka tayi ta fito tare da gabatar da Sallah,bayan ya idar har azkhar cikin larabcinsa yace na gode matata Allah ya bani mace me kaunata me kula dani, Maheerah ta wani yatsina Masa Fuska tace idan ban maka ba wa Zan yiwa amma fa Ina bukatarka sex nake so ni bani da hakuri ka sani,Ahsan yace kina kallo bani da lafiya,oh nufinka sabo da ka makance baza muyi rayuwar aure ba yau kwana biyar fa rabon da ka min wani abu kasan kuma ya nake tunda baka gani ai wannan waje ba sai me Ido ba ma zai gane Hanya,Banda ni bazan gane ba cewar Ahsan,ba sai na saka a Hanya ba,bakinsa ya dan tamke yace bana mood yanzu baki da hakuri ki bari na samu nutsuwa a zuciyata bakya ganin halin da nake ciki.


      Maheerah kwafa ta ja ta manta ta kori Ayusha ta kwanta baccinta ta barshi a kasa saman Sallaya, sai 11am ya tasheta yana fada Mata yunwa nake ji ya kamata ki sama min wani Abu naci tunda kin kori mai aikin naki,ko kulashi bata Yi ba Wai bacci take yi bayan tana jinsa, a hankali da lalube ya samu ya fito Palo tare da Zama a kujera,lokacin Cele ta gama girkinta tsaf ta fito ta ganshi yana hamma,tace karka cinye ni da hamma haka  yunwa yake ji ne,tarkacenta ta kawo gabansa ta rike hannunsa tace Cele Rufaida,Murmushi yayi tace Sabahul khair,Kai ya jinjina Mata kawai, tea dinta data hada tasa spoon ta rike hannunsa tare da dawo da shi kasa ya zauna saman carpet yanda Suka saba cin abincinsu, Shayin ta ebo a Spoon sai da ya huce ta Kai bakinsa yaji spoon a saman lips dinsa bakinsa ya bude ta zuba Masa ya shanye,Ahsan a ransa yace Anya Kuwa bazan Yi Mata biyu ba,ai Mata biyu sunyi a rayuwa idan wannan ta Bata maka sai wannan ta faranta maka Allah yayi gaskiya mu larabawa da kudin ma Sai dai mutum ya Kara aure a boye  bayan ga abinda Allah da manzo Suka ce,Rufaida ta Zama Masa Kamar matarsa sai kace kishiyar Maheerah,a ransa yace gata da tsafta ga tausayi da Imani,nan take ya maida sunan Cele Iman wai tana da Imani, Cele Kuwa tana bashi shayi ga chips da kwai sai da yaci da yawa sannan ya nuna Mata ya koshi, Cele dai harda Dan zuba ruwa kadan a hannunta tare da gogewa Ahsan baki yanda akewa Yara a Nigeria sabo da ko da bakinsu ya baci,Tissue ta sa ta sake goge masa bakinsa Yana ta dariya marar sauti,Cele tana kallonsa tace kaga idan kana gani kayi magana wannan Ido tangararan ace bawa baya gani da su gwara ka sa glass dinka ai sai ka hanani sukuni na zaci kana gani haba Ido fess haka Anya ba salon Iskanci bane wannan amma bari zan kureka sai dakko Allura nazo Zan tsira a idon Indai kana gani ai Zan gane shu'umin bawa.


    Hannunsa ta kamo ta Dora a cikinta tace cikina kaji sai tauri yake na shiga uku ni kam,Cele ganin Wai baya gani ta taba boobs dinta tace gaskiya Ina Jin Dadi a gidan nan sai wata uwar kiba nake ji kirjina haka tabashasha dariya tayi tace an cuceka bakwa Jin hausa wlh kalmomi iri iri na iya shege bakwa ji.


     Maheerah ta leko taga Sanda Cele take bawa Ahsan abinci kishi kamar tayi ihu,Fitowa tayi Kawai ta shiga dakin cele ta kwaso Mata kayanta kaf tace gashi nan ta dauka ta bar musu gida ciki basa so,Cele ta gane nufinta duk da bata Jin me take cewa,Murmushi Cele tayi tace wallahi Zama daram ba inda zani in tafi inje Ina ai Naga gidan zama inci me kyau Insha me kyau a Sadaka ba tare da na Zama takari ba Zama daram,Maheerah ta nunawa duwawu ta zauna tace Zama dole,Ahsan ne ya musu magana yace su daina fada,Cele ba jinsa take ba sai Maheerah da ta dage tana masifa na gaji kana kallo ai wannan bakuwar tana taba ka yanda taga dama ko  Haram baza kace ba dama kana so ta taba maka jiki to sai ta bar gidan Nan,yace sau nawa kike ji Ina ce Mata Haram Haram ba inda zata je wannan ai zulunci ne an sa Mata ciki kuma a koreta to gida nawa ne ba inda zata je ko ta haihu sai ta zabi tafiya ko Zama amma tana gidan Nan,Maheerah tace baza ta zauna min a gida ba tana masifa Ahsan ya farara laluben Maheerah Wai zai mareta tana Raina Masa hankali,Cele ce ta jawo Masa ita ta karfi ta danno fuskarta jikinsa Wai gata ya daketa, Dan Marin ma wani tas kadan ko yaro bazai ma wannan lalataccen Marin na Ahsan ba,amma Maheerah sai kuka tana yarfe hannu ta shiga uku yau miji ya mareta shima Ahsan a Dole Namiji yayi bajinta,Cele taja Tsaki tace Kai dai ko wani Salahu wani Sahanunu da kai wannan Zama a gidanku akwai takaici Yar iskar yarinya tana ma Iskanci ka kasa komai,Kan Maheerah ta juya tace Yi Mana shuru shegen hakora Kamar katangar kwalabe, Dan iskan hakora Kamar kwano yaji lamba dakinta ta wuce tace irn wannan bakin ciki a gidan Ahsan ai ya baci wannan ba karamin dakikin balarabe bane haba.


      Mami tana gama Idda  Auta yaje har dakin Baffa,ya shiga ya gaida shi,Baffa Yana shan lemo a zaune Yana tunanin duniya yace Autan Mami ya akayi ne Naga kana ta smiling yace Albishir Zan baka Baffa amma sai ka bani goro,yace me kake so za a baka idan fa me Dadi ne Albishir din,yace deal zamuyi Zan fada maka amma nima idan na Shiga University  zaka Yi min aure,Baffa ya bude Baki yace aure kuma wace matar? yace me rabo ce dariya Baffa yayi ya dauka Wasa yake,Auta yace satin Mami biyu da aure aka saketa fa ta dawo gidan Yaya Nawwar a can tayi Idda yau ta fita,Baffa Yana daga zaune bai san sanda ya mike tsaye ba,yace yanzu Auta tana gidan Nawwar? Ina gaya maka kuma tayi Idda ma ka yarda dani mana,wow Alhmdllh amma naji dadi yanzu ta ya Zan Mata magana ta yafe min ta dawo gidana, Simple cewar Auta abu me sauki idan zaka cika min Alkawari na to Zan wuce maka gaba,Baffa yace Auta manya to Zan cika maka yace to karka je yanzu Baffa ni nasan ya zanyi in lokaci yazo zance kaje,Auta to Ina so na ganta,to ai kaji Kuma Baffa zaka bata show kana da gaggawa,so kake ta ja ma aji ta rainaka kayi zamanka Zan ma magana,Baffa yace to Auta na sanka ba Wasa yace sure ya fice Yana fita wajen Mami yazo,ya iske tana girki yace Mami tace naam ta juyo tace Auta sai taga Auta Yana hawaye shaaaa shaaa tace Kai lafiya,harda sheshekar karya yace a...ab..abin takaici.....Mami ta tsorata tace Wai mene? ...hawayensa ya goge na karya yace ba komai ba sai ma na fada Miki ba tunda nasan baza ki damu ba ke,Mami tace bafa na son Iskanci idan zaka fada min ka fada min which kind madness be this,Auta yace wani satin za a daurawa Baffa aure,Ido Mami ta zaro ta tsaya kamar gunki tace aure Kuma tsofai tsofai da shi sabo da budurwar zuciya,Auta yace Kuma budurwa ce zata Kai sa'ar Aunty Rabi baki ganta ba Wai abokinsa ne ya bashi ya aura,Mami tace Kuma shi baida hankali sai kace yaro ba sai ya samu dattijuwa irinsa ba wannan wanne irin mutum ne, Auta yace bari Ni dai na bar Masa gidansa,Mami tace ya kamata wannan abin a bar Masa gidansa ne wannan ai wulakanci ne aikin banza aikin wofi rashin mace hauka ne Dan wulakanci ma yarinya budurwa ai shike nan ka fadawa Su Sultana su bar Masa gidansa su dawo nan,Auta yace ai Yaya Nawwar ya sani ma yasan da auren Shuru yayi da bakinsa yace tunda ba son Baffa kike ba yanzu mene ma amfanin a fada Miki Kawai yayi aurensa,Mami a ranta tace wato Nawwar baya kaunata ai shike nan a fili tace ba komai Auta jeka kawai, Auta ya juya ya tafi yaga Mami kishi karara ya fito lallai tana son Baffa.


     Mami fasa girkin tayi ta kashe gas din gaba daya ta dawo bedroom ta zauna gefen bed ta saki kuka, Nawwar yau da wuri ya dawo gida Yana taya Mami Murna ta gama Idda ni kuwa palon Mami nazo da abinci iri iri Dana shirya  na jera Mata a Dining sannan nayi docoration a  dining din Muka kawo cake hadadde Muka ajiye   table din yaji adon flowers red, munci gayu ni da Nawwar kayanmu iri Daya shadda Muka sa Fara kal mun zuba kyau,nace Baby ka Kira Mami yau ranar murna ce fa,Nawwar kiss ya manna min a saman lips sannan ya haura sama da sauri Yana Kiran Mami na,knocking yayi Shuru Shuru a hankali ya tura kofar ya shiga tun daga bakin kofa yake Jin sheshekar kuka,da sauri ya karasa Gaban Mami dake zaune a gefen bed tana sharbar kukan soyayya,Hannu yasa zai taba ta a zabure tace karka sake ka tabani munafuki ai ban san baka kaunata ba sai yau,da Kai za a hada baki Kai da ubanka kasan da zancen kaki fada min karka sake kulani,Nawwar yace me nayi Mami hankalinsa ya tashi tace ban sani ba Kai da matarka karku sake Shiga harkata tunda Baku da mutunci,Nawwar ya sake Kai hannu zai riketa ta doke Masa hannu tace get out,Jin Nawwar shiru yasa na taho Nima Ina cewa Baby zamu je unguwa fa ko Mamin bata nan na shiga ciki nima,a wajen na daskare ganin Mami tana kuka Nawwar Yana gabanta yana bata hakuri Yana ta lallashinta yana lallabata ta fada Masa laifinsa, ganin haka na juya Zan fita tace dawo kema munafuka Ina Zaki dawo sai ku zuba ruwa a kasa ku Sha dan Sulaiman yayi aure sai me sai akace muku mutuwa zanyi se waiting? sabo da Baffanka yayi aure nace se waiting? So what sai aka ce muku Zan mutu ko mene,namijin banza namijin wofi ni Namiji ya Isa ya bata min rai,Nawwar yace au Baffa aure zaiyi? Kai dalla rufe min baki gulmamme ai kasan komai ai Auta ya fada min komai yace wani satin zaiyi aure ka San zancen ma da sa hannunka kuke boye min to sai me ance maka Ina son ubanka ne,Sai yanzu Nawwar ya fahimci kishi ne yake damun Mami yace Auta ne yace Miki na San zancen? tace ae Auta baya karya,dariya Nawwar ya boye yace wallahi Wallahi kinji na rantse ban San zancen ba amma dai naji su Sultana suna kus kus da zancen na zaci ai gulmar Mata ce shima Nawwar ya sake shigar da Mami,Nace Kiyi hakuri Mami bamu San zancen ba wlh Kuma Inshaallah kece Zaki koma gidanki ne ke kadai wace ma ta Isa ta shiga gidan nan ban ci ubanta ba ai Baffa naki ne ke kadai,Tsaki Mami tayi a ranta ma tafi yarda da Rabi tasan zata iya Hana auren ko da tsiya tsiya,tayi kwanciyarta ta juya Mana baya,nace Celebration din fa? tace Cele what?  Ku tafi ku bani waje baza ayi Celebration din ba,tashi mukayi Muka fito nace kai Mami fa wallahi sun koma Yara abinda sukeyi ko mu baza muyi shi ba,Nawwar yayi dariya yace ai auren da mace tun tana karama ake yi musu tare suke tasowa su girma tare shi yasa Suka fi kowa shakuwa auren da akwai shakuwa,Lallai Auta Dan Iska ne shine yace na san zancen yaron nan haushi na yake ji akan na aurar da Wise ga Papa shike nan ya rainani,Dariya nayi nace nidai a samowa Auta wata Kawai mun shiga Uku da shi ya iya hada bom haka,Nawwar a waya ya Kira Auta yace yazo zai aike shi Office.

   Ya manta yayi gulma yazo da sauri Yana zuwa Nawwar ya mammake shi ya dinga cin uban Auta yace ka hadani fada da Mami,Auta yace Sorry Yaya Kuma sai ka mareni ,fita dalla Kar na sake ganinka tunda Kai baka da hankali,Nace haba Kuma sai ka doke shi na Kai hannu Zan ruko Auta Nawwar ya min tsawa yace ke wannan balagaggen yaron Zaki rike to Auta Yana zuwa ki saka hijab,Auta ya juyo ya kalli Nawwar sai da ya bari yaje jikin kofa yace ni me Zan ci da matarka old version ya fice da gudu,dariya nayi nace kaji yaro wallahi sai naci....Shuru nayi,yace Sorry new version karya yake da za a bashi ke karba zaiyi da gudu yasan bazai samu bane abu lutsu lutsu haka,dariya nayi ya jawoni jikinsa.


    Star yau fada sukayi da Malam Abhulkhair Wai ya Dade a masallaci bai dawo gida ba,Star tace kaje kayi ta karatu baji ba gani murya kamar ta zakara haka akeyi ai sai a dinga Yi ana bawa iyali hakkinsu,Malam yace ke ai kin rainani kije masallaci kiga yanda ake gaisheni ana girmamani ke Kuwa ina,Star tace ka gama min kukan kullum,kana rokata local government,kazo tumbir zigidir yanda kazo duniya sannan kace Wai bana girmamaka sabo da Allah ai Ina kokari ma su mutanen kaje musu a yanda kake zuwar min ka gani idan zasu sake saurarka,ai wlh bata kamata ma na gaisheka ba,Ni ya kamata ka gaisar kullum kace ya fargaban jiya,tunda a zauce zaka zo min kana ihu gaka ba Kaya ai abin fargaba ne amma sabo da kokarinmu na Mata washe gari harda gaisuwa wlh bazan gaisar dakai ba ai baizo a musulunci dole ba Kaine ma ya Dace ka gaisheni,bazan gaisar dakai ba fa Abhulkhair yawwa kuma body lotion Dina ya kusa karewa ka min transfer,kullum ka Tara min gajiya Kuma kana jira na tashi na gaisheka cab ashe zaka bushe,Malam Abhulkhair dariya yayi kawai yace ke komai naki yayi kinyi a rayuwa amma idan Kika tashi fadanki Kawai bi kike ta kaina,wa yace ka Dade a masallacin anyi karatu an Gama ka dawo muyi namu mana muma nifa baza a cuceni da malinta ba Dole ka bani lokaci na yawwa Kuma kayanka na gaji da ganinsu dinki kala uku ka Kara tun Aurenmu sabo da haka muje a siyi Kaya sababbi sannan kana Nan kaya ka dinga saka min a gidana Ina kallonka Ina Jin Dadi idan ba haka ba zanyi tawaye wlh,Malam Abhulkhair yace ya zanyi tunda na Zama mijin tace shike Nan naji yanda kike so Haka Zan koma amma kana nan kayan a iya gida Zan saka Miki? tace au da nufinka ka fita da su wata ta gani? Ni zaka sawa fa,an gama Aunty ya furta,tace yawwa Banda cin kudin marayu ko tallafin masallaci da ake sakawa a asusu kaci iya hakkinka albashinka na limanci da Kuma business dinka banda taba hakkin wasu,abinda zamuyi iya karfinka shi zamuyi,Yace na'am malama Tauraruwa wannan wa'azin ya shigeni,dariya Star tayi tace ai dai yau nace bazan yi girki ba a waje zamu je mu ci mu Dan shana,yace Inshaallah taso muje ki cudeni,Star tace wanka Mana please ni bana son gargajiyar nan mene cudewa Maganar dattijai,Malam dai sai yanda akayi da shi gaba daya star ta Gama mallake shi,gashi idan ya Mata laifi tayi ta jaraba,shi baida zafi ba ruwansa shi yayi Dace yasan dole baza ka samu Abu yanda kake so ba tunda kowa a duniya Yana da halin kwarai Dana banza Kuma baza kace zaka samu mutun dari bisa dari ba sai anyi hakuri.


       Kaka yau ana kwalla rana yayi Niyyar Umrah yaje ya dakko niyya da hiraminsa ya sake zuwa ya sauke Umrah ranar kwanansa uku a masallaci dakin Allah sai Ibada Kawai yake sai in yaji yunwa ya fito harabar masallaci ya siya yaci ya koshi ya koma,Addua yake kawai akan Allah ya bayyana masa Cele dinsa sannan Yana Addua Allah ya bashi kudin da zai dauki nauyin Kansa ba tare da yayi bara ba, yana zaune sai ga wata matar sarkin kasar Yemen,da masu take Mata baya mutum uku tazo Ibada,kana ganinta kasan akwai kudi,Kaka Yana zaune kawai yaga ta duka a gefensa ta zube Masa wasu makudan kudade Wanda dollars ne Kawai ta zube Masa Sadaka ta wuce ko kallonsa bata Yi ba,mutane suna kallo wasu suna cewa tsoho ya washe,Kaka ya daga hannu Yana Addua yaga kudin nan yace Allahu Akbar sai ya sauke Hannu yace Alhmdllh Alhmdllh Addua ta Kare ya kwashe kudi jiki na rawa ya mike maimako ya karasa Ina farin ciki yasa bazai iya ba tashi yayi yabar masallaci yace sai gida, a hanya ko gabansa baya kallo sauri yake yaje gida,sai ya hadu da askarawa suna kame yanzu sabo da ya samu kudi baya so su Kama shi duk askarawan Nan sun San Kaka yawanci sabo da duk inda ya gansu sai yaje ya Mika musu Hannu akan su kamashi sunki Kuma,wannan karon suna ganinsa daga ganinsu sai ya kwashe da uban gudu Kamar ana gudun fanfalaki tsoho dashi ya iya uban gudu haka,gulma sukayi Suka to ya Fara Jin dadi a kasarsu dole su Kama shi duk Sanda suka ganshi back to Nigeria, tun daga ranar Kaka da Askarawa Suka sa kafar wando daya, baya ma Fitowa daga masallacin layinsu sai gida,abinci ma a wajen takari yake siya masu kawowa gidansu Yana daki sai masallaci ko keyar Kaka Basu sake gani ba sabanin da Wanda kullum sai yaje wajensu, suyi ta labarin Kaka suna dariya,wani ogan askarawan kame  a cikinsu yace Dan Allah ko sun ganshi Kar su kamashi su kyale shi ai tsoho ne dukkansu ya musu fada Kar su sake su Kama Kaka su kyaleshi ai rayuwarsa ta Kare ya tsufa kadan ya rage ya karasa sabo da ya tsufa,suka ce to Suka kyale Kaka idan ya fito ma har zuwa suke su Mika Masa hannu su tafa su dariya yake basu tsabar harkalla da hausawa wasu larabawan masu shaguna da masu kame suna Dan jin hausa,Yan kasuwar ma Kamar sun zauna a kasar hausa haka Suka iya sosai.


    Wani Askari ne da Hausa ya tare Kaka a hanyar masallaci yace kazo Ni Zan baka aiki zaka iya? da hausarsa lalatacciya yayiwa kaka magana,Kaka yace wanne iri? Yace Ina da mota Zan baka ka dinga tukawa taxi Zan maka takardu da komai ka iya mota? Kaka yace ai ni tsohon driver ne a Nigeria na Iya mota,yace idan baza ka iya yawo ba Ina da motar Yogourt Zan baka Ina da company na Madara zaka dinga kwaso Madara kana kaiwa wani kantuna da address Zan baka zan sa a koya maka aikin,Kaka yace na gode zanyi wannan ai ba na wahala bane suka tafa da ba askarar nan

  Bayan kwana biyu tsakani wani balarabe yazo daga wata state daban da gani kasan Yana da Naira ba askaren nan ya nemo Kaka,shi dai Kaka yana tsaye Yana jinsu suna ta larabci dake baya ji sai dai dai yake tsinta Kaka Bai sani ba ashe siyar da shi akayi akan kudade makudai Kamar wani Zamanin bayi anyi cinikinsa bai sani ba,Kaka ya yarda da wannan Dan sandan ya dakko kayansa yabi wannan mutumin balarabe a motarsa tunaninsa aikin za a koya Masa Suka tafi,Kaka yaga kamar hanyar Jeddah aka Yi da shi kawai dai Yana mota amma a jikinsa yaji kamar ba Alheri bane,suna uban gudu a mota Yana kwarara Addua.


    Mairo ciki ya tsufa Haihuwa ko yau ko gobe gashi takari asibitinsu ma Basu da gata a can ba kowanne asibiti suke zuwar musu ba Basu da yanci tunda basu da ingantattun shedar Zama a kasar su, Mairo kullum kudi Yana tafiya a biyan bashi Dan Wanda ta Tara shine taje siyayyar kayan jariri wani shagon larabawa,tunda taje larabawan Suka fara kus kus da sauran yaran shagon,Mairo tana zuwa Suka dinga washe Mata baki Suka ce ta shiga ta zaba ta shiga ciki ko Ina kayane iya kallonka Hanya ma a ciki kadan ce, ogan me shagon Yana bayan Mairo,yaran shagon Kuma wasu suna bayan ogan wasu mutun biyu sun tare gaban Mairo sun tsaya a gabanta wato sun sa Mairo a tsakiya kenan,Ogan ta baya Yana sosa Antenarsa gashi dattijo su Kuma yaran nasa Basu fi 20yrs ba shi kuwa zai Kai 60yrs ma amma sabo da zubar da girma da yaran suke hada baki,Mairo taji Antena tana guganta ta baya ga ciki tsoho ga yaran sunki matsawa sun tare Mata gabanta wani dan iska ma juyowa yayi shima Yana gogawa Mairo Antena ta gaba ogan ta baya,Mairo ta rasa yanda zata Yi ta tura ta tura sunki matsawa gashi sun matseta a tsakiya mararta sai ciwo ta fara,Yaron Dake gabanta ta samu ta galla Masa Mari ta nausheshi tana zaginsu da larabci Suma suna ramawa Wai me yasa Suka Zo musu kasa sun bar kasar su sunzo Iskanci kasarsu,Mairo sabo da su takari ne suna harka da mutane a garin har sun iya larabci ba laifi wani uban naushi ta Kai Suka rike hannunta Kuma basu fasa Mata gogen ba,yaron ta samu ta gartsawa cizo a goshinsa sai da ta fasa Masa goshi,ba shiri ya bata hanya ta fice da gudu gudu tana rike mararta ta fito bakin shagon ta tsuguna a wajen tana murkususu,Allah ne ya kawo su Sadiya Suka ga Mairo tana nakudar dole ta kamata Suka dauketa zuwa asibitin da za a iya dubata basu dade da kaita ba ta haifo yarta Mace  me Kama da Saurayin da yayi kidnapping dinta ya Mata cikin, takari ba abinda ya dame su wannan ba sabon Abu ne ba ka haihu ba miji a wajensu,murna suke ta zuwa suna taya mairo,  Mairo ta samu Sadiya ta bawa kudin Suka siyo Mata dukkan kayan bukata nata Dana jariri, zuwa dare aka sallamota ta dawo gidansu da yarta,Mairo sai Murna take yi tana kaunar yarta harda kissing dinta jinta take Kamar ranta,aka zaro nono Kamar ta taba shayarwa dake da lafiyarta ta haihu aka yo bismilla aka sawa jaririya nono a baki ana shafa Kan jaririya tace sunanki Madina kinji Yar lelena da larabci Zaki tashi kinji a lahira kin huta duk tambayar da za a Miki a lahira Zaki amsa abarki ba gargada bare Ina ina mu ki kyale mu ko ta yaya ma amsa tamu,Sadiya suna Jin Mairo,Sadiya tace in Banda jahilcinki Mairo larabci ko bakya ji a lahira ai Allah zai sa kiji dole da shi Zaki magana ba sai Wanda ya iya ba,Mairo tace ke rabu dani gwara ta iya tun a duniya.


     Bayan kwana uku Cele ce kullum ke kula da Ahsan,Maheerah tayi zuciya tunda tace ta kori Cele ya hanata tafiya to ta barwa Cele shi tayi abinda take so,Ahsan shima ko a jikinsa wanka ma Cele ce ke kaishi tana gwada Masa komai da ta gaji tace zata koya Masa ma yanda zai gane da Kansa ya dinga kai Kansa.

  Washe gari Maheerah sai data bari cele tana dakinta Ahsan Yana Palo yayi zuru sanye da makeken glass sai kuwa Maheerah tayi waya da Saurayinta yace gashi ma a gidan ta Bude Masa kofa,da sauri ta fice ta gaban Ahsan taje compound tsalle ta daka ta dane jikin Saurayinta tana murna tace da larabci my life ya makance zamu ci duniyan mu,dariya yayi Yana murna yace you are smart yana Jin turanci shi ya iya,yace I love you you are smart,yanzu wannan gidan gaba daya namu ne? Me hakora duk cin Zuma tace ae fa masoyani Suka sake rungumewa tace ai baya gani ta gabansa zamu wuce,Suka shigo tare da kwartonta Ahsan Yana Palo a zaune harda tsayawa a gabansa Suka rungume Suka hade bakinsu waje daya Hannu tasa tana waving a fuskarsa tace da Saurayin cikin rada ka gani baya gani,Ahsan yace waye anan mutum ne? Maheerah shuru,Rufaida ya Kira da Iman,Maheerah ta yatsina fuska harda yin rawa a gabansa ta ja hannun Saurayinta suka shige bedroom Suka datse da key sabo da Kar ma Cele ta gani.

  

     Cele ce ta fito cikin kwalliyarta Arabian gown ta tsula kyau tana kamshi tazo ta zauna a gefen Ahsan fuskarsa ta leka taga yana hawaye tunaninta makantar data same shi ce ta sa yake kuka, tace Allah sarki Sannu zaka warke Inshaallah hannunsa ta rike tana cewa Inshaallah Inshaallah wai ya Gane zai warke Inshaallah,Kuma ya fahimceta tsaf,ya kamata kayi wanka gashi har dare yana zuwa tamikar da shi Suka nufi bedroom dinsu ta murda handle a kulle gam,ta bubbuga tana Kiran Maheerah shuru ko motsi bata ji, taja Tsaki tasan tana ciki ta juya da shi dakinta ta kaishi toilet ta dora mosa komai yanda idan ya taba zai Gane sannan ta fito yayi wankansa da Alwala ya Kira sunanta Iman,Cele tace ya maidani wata Iman taje ta bude masa kofa ya fito ta ganshi daga shi sai towel Saura kadan ma towel din ya sabule Cele taji wata sha'awa tace Kai wani zuut zuut haka nake ji,uhm uhm da sake ta koma jikinsa ta makale Kansa Yana sama yace Haram,dariya yake bata idan yace Haram Haram din nan, ganin baya gani ta lallaba a hankali ta zame towel din Wai irin ba ruwanta faduwa yayi da Kansa ba ita bace,  Cele tace idan nace bana so bana so sai na dinga mantawa naji Ina so sai na dinga komawa jikinsa ta koma jikin Ahsan tace Dan jajir jajir harda shafa gemunsa tace you too fine fa cakulkuli ta Masa tana cewa dan Jawur Jawur komai Jajir ku Dan bakin duwawun ma babu duk duhun duwawu ku Banda ku ko ai shike nan,mu Kuwa Yan Nigeria mutum ma da haskensa sai kaga duwawu duk darba ta daskare da baki, ai shike nan amma ai Kuwa akwai juriya ba,Ahsan da larabci yace ta fiye surutu  gar gar gar har Wai haka yake Jin yaren Hausa,Cele ta gyara Masa towel dinsa,Mai ta bashi Yana dabara da Haka ya shafa sama sama,tace baka da Kaya a dakin nan ta tayashi ya maida rigarsa ta dazu, duk ta kalle Masa Antena  wajen saka Kaya gasu su basu fiye wayo ba.


    Tashi yayi ta mike itama zata kaishi Palo ya rungumeta yaga abinda take so kenan ya gaji da halinta, cikinta ya shafa tace nidai cikina ya shiga Uku Wai ni mene a cikin nan be kowa Yana son taba Boobs shi sai dai ciki wannan wanne bala'in sabon salo ne na larabawa,hannunsa ta cire da cikinta tace ba nan ne inda ake so ba Nan ne a'a haba ayi mutum dolo,Ahsan yaji abu a hannu ya janye hannunsa yace Haram ya kwace jikinsa ya fice kamar yasan Hanya,Cele tace kaga kamar Yana gani Kai wallahi ban yarda da mutumin nan ba Kamar me ido,Cele Fitowa tayi tace makafi da basira ance ta kaishi ya zauna a kujera ta kwanta a kasan carpet tana tattale kafafu sabo da ba gani yake ba,Cele tace wannan masifa ni dai Zan daina cin kayan Dadi a gidan nan ance suna jawo sha'awa, gani Kawai tayi an bude bedroom din Maheerah katon balarabe ya fito tana bayansa Suka fice ta gabansu sabo da ta San Cele baza ta iya magana da larabci ba shi Kuma mijjn baya gani ya makance suka fice,Cele zaune ta mike ta lallaba jikin Ahsan tace Kai Kai cikin rada matarka ta kawo kwarto kana zaune kaga ka saketa tam,Dole na koyi larabci wlh fita Zan dinga Yi ko Zan hadu da wasu masu Jin hausa su koya min bazai yuwu ba wannan Zama haka Ina Sam da sake ana ta cin Amanar bawan Allah wlh sai an saketa Ina ma wani na sakin matar wani amma duk da haka sai na sakar Masa Maheerah bari na Fara fita bazan bar gidan nan ba sai Naga karshen Maheerah iyye,Ahsan ta girgiza tace kwarto a gidanka Kwarto Kai,wlh ka rama dani gani nima.


     Ahsan Yana jinta tana ta zuba surutai,Driver dinsa ne ya kirashi Cele ta Kara Masa wayar a kunne ya amsa sallamar yace yazo ya kaishi unguwa,ba a dade ba sai ga driver har Palo yazo ya rike Ahsan har mota Suka fita lokacin Cele ta bisu taga yanda ake bude kofar da rufewa tace Alhmdllh,Maheerah ce ta shigo cike da nishadi ta gyara bedroom din da kanta tayi wanka ta tsarkake jikinta sannan tazo ta fice abinta ta cakare cikin Abaya da Nikaf tasha takalmi da jaka Silver tayi kyau,Cele ce ta tare Mata Hanya tace Dan uwarki wa na kama,Maheerah ta kalleta tana wani yatsina da larabci tace Indai mijine ta bar mata taje suyi harka,Cele tace naci ubanki yanzu kuma Ahsan na kwace shi daga yau bake ba shi karki sake kallonsa munafukina wal munafukatoon, Maheerah ta gane zance wato itace munafuka,ta nuna kanta Cele tace ae Munafukatoon,Majnooniya, lah lah lah Muminat,Wai ba mumina bace ita,Maheerah sai ganewa take Wai ana ci Mata mutunci karshe Kamar zata Yi kuka idonta yayi jajir,Cele tace Kuma na tare Hanya ba inda Zaki je Munafukatoon,Maheerah ta nuna wayarta Wai zata Kira askarawa su kamata da hannu Cele tace su zo su zo din,suna tsaye suna ta rigima Cele ta tare Hanya fafur tace baza ta fita ba ta hana,tace nice me magana da yawun Ahsan ba inda zaki je shegen Ido Kamar na kwado.


    Mami kwana uku ta sawa kanta damuwa akan Baffa zaiyi aure,bata ko Maganar kirki Kawai sai yake,Nawwar yana ta aikin lallashinta,tace wallahi idan baka hana ubanka aure ba baza ka taba ganin farin cikina ba,Nawwar yace idan ya dawo zaki yarda ki koma gidansa? Mami tace ae na hakura Zan koma amma Kar ya Kara aure,Nawwar yace to Auta shine da wannan Maganar Kawai,Mami tace Auta din? Yace ai bakinsu daya da Baffa sai abinda yace da Baffa shi yake yi,Mami tace to ku dai kuka sani tana Jin kunya Babba da ita tana uban kishi haka a gaban Yara.





NAJI WATA TANA MAIDA MIN DA NOVEL DINA AUDIO BADA IZINI NA BA,KI SANI HAKKINA NE HAKKIN WACCE TA SIYA NE,KU SANI KUN CI HAKKINA DUK WANDA YA MAIDA MIN AUDIO BA IZINI NA.







AsmaBaffa

08061929616

No comments

Powered by Blogger.