Zafin Kai 11
_Mamuhgee 11_
*_ASSALAMU ALAIKUM JAMA’AR KWARAI JAMA’AR ZAFAFA BIYAR_*
*_KAMAN KO DA YAUSHE DA MUKE KAWO MUKU ABABEN AMFANI GANGARIYA KUMA DAKI BARI MASU AMINCI A KUDADE KALILAN_*
*_YAU MA MUN ZO MUKU DA TALLAN BABBAN SHAGON NAN DA KE KAWO MU KAYAYYAKI NA KASAR GERMANY!! KUNSAN DAI GERMANY SUNE AGABA A FANNIN KAYAYYAKI MASU KYAU DA KARKO_*
*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*
*_MAAB LUXURY HOME_*
*_SUN KAWO MUKU DALLADALLAN KAYAYYAKIN GIDAH NA KAWATARWA DANA KITCHEN MASU HASKA DAKUNAN GIRKI… KWASHA KWASHA_*
*_SU DIN KARSHE NE A DUNIYAR KAYAYYAKIN GIDAH DANA KITCHEN NA KECE RAI NI… INA UWAYEN GIDAH, AMARE? ANTOCI, KAWUNNI, YAYYU MAZA, KANNE DA MA IYAYEN MU MAZA?_*
*_KU ZO A DAMA DA KU A WANNAN DAMAR ME DAUKE DA DIMBIN KAYAYYAKI MASU KYAU A KUDI DEDE MISALI WANDA KOWANE ZAI IYA MALLAKA IYA KARFIN SA_*
*_KU ZIYARCI SHAGON DA KE A KANO.. TITIN AHMADU BELLO WAY_*
*_KO KUYI ORDER DA GA SHAFUKAN SADARWA TA INSTAGRAM:@Maabluxuryhome_*
*_FACEBOOK:@maabluxuryhome_*
*_SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDAH,, INGANCI DA RAHUSA, KYAU A DADE ANA AMFANI DA SU SAI KAYAYYAKIN MAAB LUXURY HOME_*
*_A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY ORIGINAL HOME DECORS AND KITCHEN UTENSILS_*
*_MAAB LUXURY HOME GOT YOUR HOME AND YOUR KITCHENS COVERED… JUST A VISIT/CALL/DM AWAY_*
*_08034631010 MAAB LUXURY HOME👈🏽_*
************
Suna shiga gida Hande dake tsakar gida zaune tana jiran dawowarsu tahau fada da masifa sosai tana hadasu da kalmomi marasa dadi iri iri amma babu wanda ya dago kai acikinsu kansu na qasa harta gama fadan tace su matsa mata daga ka tukuna suka bar gurin suka isa dakinsu jakunkunan hannunsu kawai sika aje suka fito sikai Alwala suka koma suka hau sallolin dake kansu tin daga azahar sbd a asibitin Benazir bata samu ko motsawa ba ita kuma Sumayyah batama san ina kanta yake ba.
Suna gama sallah Annensu ta kalli Sumayyah dake sallah tana hawayen azaba tayi mata sannu tareda kamo qafar ta duba ta tofa mata addua cikeda jin qai da tausayawa 'yar tata datake jinsu su biyun a zuciyarta fiyeda yanda take jin kanta.
Benazir da Annensu ne suka fito suka hau wankin kayan shago da aka kawo Sumayyah kuma tana daki kwance tana fama da azabar ciwon ga yunwa a cikinsu kaman bazasu iya jan numfashi daidai ba.
Sai bayan ishai suka gama kuma har lokacin Ababa bai dawoba dan haka Hande na basu abincinsu suka koma daki suka zauna suka cinye sukasha ruwa suka kwanta.
Saar da suka samu a ranar Ababa koda ya dawo Hande tayi bacci bata samu sanar dashi sunyi lattin dawowa gida ba,
Qarfe hudu na asuba suka tashi suna gama sallah Benazir ta fito tafara goge kayan da sukai wankin da daddare
Gari na fara haske Sumayyah ta fito ta fara gugar itama sbd kada Ababa ya fito yaga ita batayi,
Akwai zazzabi da rashin qarfin jiki sosai a tareda da ita amma hakanan ta daure sika qarasa gugan tareda Benazir suna kammalawa sukai wanka tareda shirin makaranta Hande ta basu sauran taliyar da aka dafa musu da safen suka karya,
Banda sumayyah wadda ko ruwa takasa sha sbd qarfin zazzabin dake cinta haka suka lallaba suka fice har lokacin Ababa bai tashi ba.
Suna fitowa gurin hawa mashin dinsu baqar lexus na parking gabansu babu bata lokaci suka shiga sbd Sumayyah dake gap da zubewa qasa
Aikuwa suna shiga motar ta some dan haka hankali tashe suka isa asibiti dan kuwa daga Benazir din har Bilal babu wanda yake tina komai bayan samuwar sumayyar da rayuwarta daga halinda take ciki.
Kaman wancan karon take aka kwantar da ita nurse da likita suka fara abinda ya kamata akanta Bilal din da Benazir suna waje babu mai iya magana a cikinsu sbd Benazir datake neman zauncewa da tashin hankali.
Haka sukai zaman jira bayan an barsu a dakin su kadai suna tsimayin farfadowarta.
Guraren qarfe goma numfashinta ya dawo daidai alaman bacci mai qarfi ya dauketa daga wahalar,
Kallan Benazir Sir Bilal yayi yace mata zai tafi office yanada masu jiransa zai dawo ba jimawa.
Gyada masa kai kawai ta iya yi harya fice bata iya motsawa ba.
Zaman jira ta dasa har bayan azahar ta samu tayi alwala a toilet din Amenity room din dasuke ta futo tayi sallah tana idarwa Sumayyah din na farkawa ta taimaka mata zuwa toilet tayo fitsari da Alwala tazo a zaune tayi sallah tana idarwa Akai knocking kofar dakin tareda turowa aka shigo.
Kallon wanda ya shigo sukayi dukkaninsu a tare harda Sumayyah dake cikin mutuwar jiki.
Kallansu yayi shima cikin yar girmamawa yace Sir bilal ne ya aikosa ya kawo musu sako,
Ajiye ledojin hannunsa yayi gaban Benazir yana juyawa bayan yayi musu fatan samun sauki ya fice daga dakin tareda rufo kofar.
Kaman bazasu taba ledojin ba tsawon mintina kafin Benazir ta bude ta duba taga take aways ne masu dauke da sunan tsadaddan restaurant din KAANTEs Hotels & Suites.
Wasu irin tsadaddun Deserts ne da crispy chicken sai chicken biryani da kuma salad sai drinks marasa sanyi sosai da ruwa katan daya.
Wani tsinkakken yawu ya wuce maqogwaransu su duka biyun sbd wani irin kamshi da basu saba ji ba dayake shiga hancinsu.
Kallon juna sikai kowannen hanjinsa na fidda wani sautin kukan yunwar datake tauye dasu.
Babu wanda yayi magana a cikinsu abincin sike sake kalla Sumayyah na jin kaman zatayi amai sbd yunwa da matsuwa taci abincin,
Ita kanta Benazir yawunta sun kasa tsayawa sai tsinkewa sikeyi suna wucewa maqogaranta.
Sun jima suna shawarwari da zuciya da hanjinsu kafin daga karshe dai suka afkawa abincin da bismillah suka cinye komai tas sbd Nama wani abu ne da a iya shekarunsu bazasu iya fadan so nawa suka taba cinsa ba,layya Ababa bayayi,baya siyo nama gidansa baya yanka,idan kaga yaci nama iya wanda zaici ne shi kadai sai Hande dayake bawa dan haka a rayuwarsu dai bakinsu bai wani san dandanon namaba dan haka yau din suka ci kaman ba gobe.
Suna gamawa Nurse ta shigo ta bawa Sumayyah magani tareda wasu allurai take sumayyah din takoma bacci.
Ita kanta Benazir din sbd hutu da Cimar da basu saba ba take bacci ya dan dauketa daga kujerar datake zaune.
Basu farkaba sai bayan laasar da sauri Benazir ta tashi ta fada toilet din dakin ta wanko fuskarta tareda Alwala ta fito ta kama Sumayyah tayo Alwala itama suka fito babu bata lokaci sikar sallar laasar suna idarwa sika fara tinanin tafiya gida sbd ba laifi sosai Sumayyah din ta samu sassauci daga mummunan azabar datake ciki,
Babban abinda yasa duk ha'darin hakan Benazir ta yarda suka zo asibitin shine tinawa takeyi da hadda qonuwar wuta ne yayi sanadin Rasuwar Samirah,
Idan ta tina hakan jin takeyi zauncewa zatayi daga ita har Annensu idan wani abu mai kama da hakan ya samu Sumayyah sbd a yanzu da suka debo shekaru iya su tini sika manta da komai da kowa bayan junansu,
Wata irin kauna ce mai tsananin gaske da qarfi take sukewa junansu,
Tin shekarun baya da suke tareda sauran yan uwansu daman Kaunar Benazir a ran sumayyah daban ce hakama ita kanta Benazir din sumayyah daban take a ranta bayan Annensu,sai samirah da itama suke ji da ita sbd tana kaunar yan uwanta sosai da zuciya daya,Safnah ce zasu ce basu tabbatarda tasu kaunarba a ranta amma a nasu ran itama suna kaunarta har cikin zuciyarsu amma daga ranar datayi amfani da Annensu ga gudu suka rufeta daga zuciyoyinsu dan bazasu iya ciretaba jininsu ce kuma suna sonta gaskia.
Kokarin barin dakin sukeyi Nurse ta shigo ta hanasu tareda sanar dasu sai Sir Kaante ya dawo umarninsa ne.
Babu yanda basuyiba su tafi aka qi barinsu haka suka zauna suna jiransa har Sumayyah ta sake komawa bacci sbd akwai abinda yake sakata baccin tsakanin allurar da aka saka mata a drip nata kokuma maganin da aka bata.
Benazir zuwa lokacin hankalinta ya dawo jikinta gabaji daya bata cikin nutsuwa tsoro da bugawar zuciyarta gabaki daya sun zaburo,ko wane iskar numfashin datake shaqa tafe yake da zallar tsoro da fargaba.
Wani abincin aka kuma kawo musu wannan karon snacks ne,Samosas manya masu kyan gani sai doughnuts masu girma da taushin gaske sai cup cakes da wata kalar crispy chicken din,
Ladar daya kuwa drinks ne sai Apples.
Numfashi ta sauke sbd wannan karon kam Asarar kayan zaayi dan bazasu iya cinyewa ba haka bazasu iya zuwa gida dashi ba.
Sumayyah data farka kadan taci sbd maganinta akwai me saka cin abinci sbd ganowa da akai akwai yunwa tareda uta sun dauka itace batason cin abinci basusan samun abincin ne batayiba taci ta koshi.
Benazir kasa cin komai tayi sbd fargaban zuwa gida da abubuwan gashi a yanayin ciwon sumayyah da maganinta tana buqatan abinci.
Tana cikin shawarwari akazo tafiya dasu gida ba Bilal din bane aiki ya riqesa suna ganin hakan suka saka ya ajiyesu makaranta daga can suka hau mashin suka koma gida.
Cikin tsoro da fargaba mai tsanani suka shiga gidan
Hande na dakinta Annensu ce kawai tsakar gidan tana aikin wankin kayan Hande dasu zannuwan gadon Ababa.
Suna ture ture sbd rawar jiki da tsoro suka fada dakinsu
cikik rawar jiki Benazir ta fidda ledan kayan ta tura cikin kayansu na sakawa dake daure a gefe
Sai alokacin ta saki ajiyan zuciya gabanta na tsananta faduwa tinda ba cinyewa akai ba har lokacin suna cikin hadari mai girma.
Sumayyah da zuciyarta da jikinta suka kasa dena rawa itama kallon Benazir tayi murya a sarke tace
"Bena ki shigo da Anne tin Ababa be dawoba a cinye kayan nan mu saka ledojin a bra tsoro nakeji sosai wlh,
Idan tsautsayi da kadda yasa Ababa yaga ledan nan sai rasuwar samirah tafi tamu sauki da rahama.
Ita kanta Benazir bata cikin kwanciyar hankali idan ba kawar da komai akai ba tunda mummunan kaddara tasasu shigowa gidan da kayan sbd Annensu sukeso itama yau taciwa cikinta abinda zai koshi tinda abune da basu taba ba arayuwarsu ci a koshi.
Sallar magrib sukayi suna idarwa suka fito Benazir ta kamawa Anne wankin suka qarasa ba bata lokaci suna gama shanya suka shigo daki.
Benazir ce ta zauna setin kofa tana hango mai tahowa suka fidda kayan tareda budewa Anne suka ce tayi sauri taci ta koshi.
Wani tsalle zuciyar Anne tayi kaman zata fado sbd tsananin tsoro da firgita muryanta na rawa qasa qasa tace
"Ina kuka samo?
Menene wannan din?
Meyasa kuka taho dashi gidan nan?
Kusan kashemu Ababa zaiyi idan yaga wannan kayan ko Hande.
Sumayyah ce ta dauko doughnut hannunta na rawa sbd tsoro ta tura mata a baki itama murya na rawar tashin hankali tace
"Anne kiyi sauri kici zamu fada miki daga baya inda muka samu"
Laushinsa da qamshin mai dadi tareda azababbiyar yunwar cikin Annen yasata yagar rabinsa tafara ci take taji cikinta yana kukan yunwar ya samu abinci.
Hannu baka hannu qwarya takecin kayan musamman kazar me shegen dadi tana gamawa ta shanye orange drink din dasuka juye a leda suka dauro mata sbd bazasu iya shigowa da robar gidan ba.
Hamdala Annen tayi bayan da cikinta ya cika sosai
Ta hada wani irin uban zuba sbd tana cin kowace irin loma cikin babban tashin hankali da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa,
Yanda kasan barayi haka dukkanin idanuwansu suke a waje kowannensu na hada gumi suna kallonta ta koshi.
Sauran abinda ta rage Sumayyah taci ta bawa Benazir sauran itama ta cinye suka nade ledojin kowacce ta tura cikin rigarta dasu suka kwana ajiki dan abincin da aka basu ma dole suka turasa sbd kar a gane sunci wani abin.
Washe gari ba laifi jikin Sumayyah saidai akwai zazzabi data kuma tashi dashi sbd yanayin makwancinsu basuda kofa a dakinsu shiyasa kusan kullum ko lafiyansu kalau kusan da zazzabi suke tashi kowannensu sbd sanyi dan duk zafi su yanada wahala sujisa sosai sbd anguwar tasu kaman daji take ba mutane dan haka akwai sanyi sosai.
#MAMUH#
#BILLONAIREROMANCE #DD KAANTE
#CONTRACT#HOTLOVE#ABABA#BENAZIR ABABA KAANTE.
ZAFAFA BIYAR🔥
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR 'KASHI
Safiyya Huguma
-FURAR DANKO
Billyn Abdul
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
09033181070
09032345899
Zafafa🫶🔥🔥
Leave a Comment