Zafin Kai 7
_Arewabooks@Mamuhgee 7_
Wani babban tashin hankali mafi tsoratarwa da Benazir ta shiga bayan wasu shekaru shine fara lura da sumayyah data fara samun ciwon qwaqwalwa kaman Annensu sbd
lokuta da dama haka zata zauna tayi shiru ta qurawa guri daya ido tana magana a hankali kokuma ta ringa kuka a hankali tana kiran sunan Ababa dana samirah sbd Safnah haka kawai Allah ya cire musu ita cikin ransu sbd abinda tayi din kafin guduwarta wanda kuma guduwar naya ya sake tsanananta musu komai daga gurin Ababa din.Azabar dasuke ciki da qunci yayi nasarar taba qwaqwalwanta kaman mahaifiyarsu,
Wace qaddara mai girma ce wannan ta hau kanta?
Tayaya zataji da wannan masifar?
Ya zatayi da sumayyah din?
Tayaya zata ringa boye wannan lamarin?sbd komai tsananin tsanani bazata iya bari Ababa ko hande su san da wannan sabuwar qaddarar ba sbd Ababa komai zai iya aikatawa akanta sbd ganin itama tamkar wata asarar ce zaiyi na dukiyar daya kashe akanta.
Zubewa tayi tsakiyar dakinsu ta fashe wani irin kuka mara sauti dayake yankan kirjinta sbd tausayin kanta danasu sumayyah da Annen,
Inama itama zata haukace gabaki daya ta yanda zata dena jin radadi da kuncin dayake ranta ta manta komai.
Sumayyah dake zaune shiru tana magana ita daya a hankali ganin benazir din a hakan yasata tasowa ta dawo gurinta tana rungumota muryarta a hankali ba kuzari tace
"Benazir kuka kikeyi nima na fara samun matsala ko?
Karki damu nima mutuwa zanyi idan na mutu komai zaizo miki da sauki zaki iya samun damar dauke Anne ku tafiyarku ko bara kuyi zakuji dadi a gaba insha Allah...
Girgiza kai Benazir tafara hawayenta na tsananta gudu bata iya cewa komai sbd matukar Sumayyah ko Anne a yanzu ta sake rasa daya itama nata lokacin na zaucewa tayi.
Hawaye ne suka gangarowa Sumayyah ta sake rungume Benazir din jikinta cikin rauni da mutuwar jiki tareda sarewa tace"
Benazir nima banason na haukace ko na mutu amma da alama kaddarata ta haukacewan kafin mutuwar a kusa take,
Kuka mai sauti Benazir ta kasa riqewa ta fashe dashi tana cusa kanta cikin tafin hannuwanta dukkanin zuciyarta na karyewa dan Allah ya sani a jininta da tsokan zuciyanta take jin Sumayyah,
Itace qanwa sumayyah din ce yayarta amma a gareta kaman sumayyah din ce qanwa sbd jin takeyi alhakin kulawa dasu a ynzu duka a kanta yake.
Ita kanta sumayyah kukan mai sauti ta sake tana yin qasa da kanta sbd sanin lalura zasu zamarwa Benazir itada Anne dan haka har cikin ranta take rokon Allah idan zata zamewa Benazir 'dinta da Annensu kaddara mai wahala da nauyi Allah ya dauki ranta ta huta.
Kaman Benazir tasan adduar da Sumayyah din keyi ta dago jajayen idanuwanta ta kalli Sumayyah kafin ta kalli Annensu dake gefe tana kallonsu cikin tsananin kukan da itama take rokon Allah ya dauki ranta idan har 'yayanta zasu samu 'yancin guduwa daga ukubar mahaifinsu su samu kyakkyaqar rayuwa a waje.
Ahankali Benazir din ta bude baki muryarta a shaqe sbd kuka tace"
Insha Allah zamu rayu a tare mu sauyi a tare
Idanma mutuwar itace hutu garemu duka Allah ya kawo mata ita gabaki daya mu tafi garesa mu huta.
Sunkuyar da kai sumayyah tayi tanajin kaman itace kaddarar Benazir a yanzu sbd halin datake neman sakata na dawainiya da ita.
Benazir ganin naz tashin hankalinta akan lalurar sumayyah din na neman qarasa taba qwaqwalwanta dan haka ta sakawa kanta juriya ta danne ta nuna mata ba komai bane babu abinda yake samunta lafiyanta kalau hakama qwaqwalwanta lafiyanta kalau.
Hakan yasa kaman yarinya qarama sumayyah din ta yarda ta sake suka koma rayuwar wahalarsu a tare harda Annensu sbd sun gano a yanzu hadin kansu da girman kaunar dasu kewa juna shine qarfinsu.
A duk kowace rana kafin fitan Ababa sai maimaita musu gargadinsa mai tsoratarwa akan kada ko a tsautsayi su kula kowane namiji a makaranta ko a hanya.
Wannan gargadin nasa kusan kullum yayi sa sai sunji hankalinsu ya tashi saidai daman babu wata niyar kula kowa a ransu bare dasuka tabbatarda maimaicin gargadinsa akan maganar na nufin komai mai muni zai iya faruwa idan makamancin hakan ta faru.
****wannan dalilin ne yasa suka kama kansu acikin dubban mutane fiyeda kowa a makaranta,
Sun fara zuwa makaranta tamkar mujiyoyi acikin mutane ahakan suke zuwa su dawo,
Basu taba qara mintina ko biyu ba da an tashi suke dawowa gida sbd aduk lokacin da suka saka qafa suka fita Azabar Annensu ke farawa dawowarsu da wuri shine samun saukin azabarta dan haka da an fito lectures basa bata lokaci da sauri suke dawowa.
Da haka Ababan ya riqe lokacin dawowarsu kan lokaci batareda magana ba idan sun dawo Annensu ta huta idan basu dawoba tana cikin wuya.
Da zasu fara karatu Hande yabawa kudi ta siyo musu atamfo masu saukin kudi kusan guda biyar biyar sai jallabiya masu saukin kudi suka kusan guda uku uku shikanan sai mayafai biyu da hijab biyu kowannensu sai takarma daddaya.
Ahaka suka fara karatun cikin taka tsantsan da tsoro da fargaba,
Babu wani mutum daya dasuke hulda dashi a makarantar kaman yanda basa yarda ko bada fuskan ayi hulda dasu.
Sumayyah fara shigarta cikin mutane sai yake kokarin bayyanarda matsalarta ta cikin qwaqwalwanta a fili sbd a duk lokacinda ta shiga mutane sai take jin kanta na juyawa,
Sam tunda suka fara karatun bata wani gane komai sam sbd mummunan sabon da Ababa yayi musu bata iya shiga mutane tafi son zaman gidan.
Benazir kuwa sosai ta maida hankali ta qwallafa rai a karatun sbd samun Abin tsira daga mahaifinsu da yardar Allah saidai kuma yanayin Sumayyah yafara hanata kwanciyar hankali a yanda ya kamata a karatun.
A duk lokacin suka fito suka zo makaranta hankalinta yakan rabu biyu ne akan sumayyah da karatun,
Tin tana boyewa cikin kama kai daga kowa har kusan anfara ankarewa da Sumayyah din na dan da tabin kai duk da ba laifi wani lokacin takan gane karatu harma da tambaya.
Ahaka suka ringa lallabawa suna karatunsu cikin kame kai daga wulaqanci da tazarcin mutane dasuke samu.
A gida kuwa idan sun daga daga makaranta babu wani sauyi daga rayuwar dasuka saba saima qari dan yanzu ganin yakeyi dukiyarsa suke ce fiye da baya dan haka a yanzu har shagon sanaar wankau ya bude wadda idan ankawo sune suke yi saidai acan shagon ayi guga a hada a leda a bayar idan masu karba sunzo dan haka yanzu wahalar taketa sake qaruwar musu sbd wankin kayan maza wani Abu ne mai tsananin wahala garesu sbd nauyi musamman manyan riguna wanda sai sunyita wankinsu kusan so uku kafin su wanku sbd sunfi qarfin hannuwansu rigunan.
Basu taba nuna gajiya ko wahalarsu a fili ba sbd babu abinda hakan zai haifar sai qarin azabar dan haka suke rayuwarsu a hakan.
A makaranta akwai wainda da yawa suke shaawar mu'amalantarsu sbd kame kansu sai yake nuni da kaman tarbiyace da suke da ita amma rashin fuskarsu da kamewarsa tareda tsoron shiga mutane dasuke a fili yasa baa tinkararsu.
Yanayin fatarsu mai duhu da kyau ga kamanninsu dasuke kusan daya ga kyan jiki na mata mai kyau da daukan hankali da Allah yayi musu yasa aka dan fara Ankara dasu wanda da basa kame kansu da tini sunfara tara samari da abokai barkatai.
*****A haka lokaci ya gangara dasu har suka gama session daya kuma babu wani sauyi ko daya bayan na Ilimi da wayewar dasuke samu cikin mutane Hakama sumayyah ta fara sabawa tini da rayuwa cikin mutane kuma a hakan bawai ta warke ko samun saukine ba kwata kwata Benazir ce a gurin kulawa da ita sosai tana kaffa kaffa kada Ababa ko hande su gane gashi Annensu a yanzu rayuwar tafi yi mata tsanani dan harsu je su dawo tana kan qafafunta tana aiki bata hutaba ko na daqiqa daya.
Results dinsu na exams na sumayyah ko kadan baiyi kyau ba duk da bata fadi duka ba amma kusan fiyeda rabi duka ta fadi,
Ababan bai wani damu ba sbd shidai iya ilimin yakeson su samu da turancin bawai cin jarabawa ba da sakamako mai kyau sam babu matsalarsa da wannan amma dik da hakan saida yayi mata dukan data kusan sati bata miqewa daidai harda Annensu da benazir ya hada duk da ita nata sakamakon yayi kyau matuka sbd babu course daya data fadi.
********Sun kammala hutunsu sun koma session na biyu wanda ita sumayyah ba dan rashin kyan sakamakon ta ba da session dinta na karshe ne tun karatun 2years ne.
Dawowarsu hutu yasa sumayyah takura qwaqwalwanta gane karatu sbd Azabar data ringa sha daga Ababa tin daga farkon hutun har qarshensa gashi harda Annensu da Benazir yake hadawa kaman jakuna haka yake binsu kullum ya musu duka ga fucewarsa.
*****Sumayyah yau tsaban azaba har yamma takai makaranta wata abokiyar karatunta da itama bata ganewa irinta suka kai sunata bita suna takura qwaqwalwanrsu har Allah yasa suka gane abinda suke son ganewa tabiyo hanyarta tabi ta department dinsu Benazir wadda tasan bazata taba tafiya ba bata jurata ba.
Sauri takeyi hankalinta a tashe sbd tasan Yau sai Ababa ya yanki naman jikinsu ya zubar a bola sbd kusan anfara kiran magrib.
"Excuse me,Aslm alkim" taji anfada daga bayanta kusan gab da ita A hankali ta dakata tareda juyowa zuciyarta na bugawa kaman zata fado sbd tsoro jin muryar namiji Abinda tafi tsoro a komai duniya yanzu shine wani namijin ya mata magana.
Wanda tagani ne yasata neman rasa numfashinta sbd tsananin tsoro da rudewa tareda firgici mai tsananin gaske.
Rawa qafafunta suka dauka ta juya da sauri zata wuce batareda ko sallamarsa ta amsa ba dan tabbas batajin ma da ita yake.
Da kallon mamaki ya bita da Id card dinta a hannunsa yana dan yamutsa fuskar kalau take kuwa,
Ta gabansa ta zubarda id card din bata saniba ya dauka ya miqa mata amma ta wucesa kaman wadda taga abin tsoro.
Isowar professor Abdallah gabansa fuska a matukar sake da zallar girmamawa yana cewa"
BILAL KAANTE you are highly welcome Sir.
Wani qayataccen murmushi ya saki tareda saka id card din aljihun wandon tsadaddiyar yadin dake jikinsa ya miqawa prof Abdallah din hannunnsa mai haske da taushin hutu yana cewa
"Thanks prof,
Bazan dauki time dinka da yawa ba time ya shige sai gobe zan dawo muyi magana insha Allah
Nazo ne sbd nayi maka alqwarin zuwa din yau din amma wanj aikin ne ya dan riqe ni."
"Ba komai zan jira ka goben idan kuma zan sameka a Kaante ne duk ba damuwa tinda nasan abubuwan nada yawa a gabanka"
"No karka damu insha Allah zan samar da time din nazo gaben"
Juyawa yayi prof din na biye dashi suna magana har zuwa ina wata lafiyayyar tsadaddiyar motarsa ta Lexus take black yana bude securityn motar prof yayi saurin bude masa yana ce masa
"A sauka lafiya Sir"
Ngd yafada a hankali cikin nutsuwarsa da Allah yayi masa ta rashin garaje ga komai.
Yana zama cikin motar ya prof ya rufe masa ya tada motar a hankali ya fice daga makarantar yana duba time na gold Agogon rolex dake hannunsa sai kuma a lokacin yaji Id card din dake aljihunsa ya saka hannunsa daya ha ciro tareda kallon fuskarta yana karanta sunan Dake rubuce a id card din SUMAYYAH ABABA.
Numfashi ya sauke a hankali tareda ajiye card din gefensa a hankali yana maida hankalinsa kan tuqin dayake yi.
#MAMUH#
#BENAZIR ABABA
#DD KAANTE#
#BILAL KAANTE#
#LOVE#MARRIAGE#ROMANCE#
#HOTLOVE#LIFE#FAMILY#CHILDSLOVE#
ZAFAFA BIYAR🔥
-ZAFIN KAI
Mamuhgee
-TABARMAR 'KASHI
Safiyya Huguma
-FURAR DANKO
Billyn Abdul
-BAKON MUNAFIKI
Miss xoxo
Duka hudu 1k
Uku 800
Biyu 600
Daya 400
Pay at
09033181070
09032345899
Zafafa🫶🔥🔥
Leave a Comment